MATATA GIMBIYATA 37-38

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         3⃣7⃣➖3⃣8⃣

     Ya dad'e yana zaune yayin da take baccin ta a jikin shi, yasan magariba ta kusa dan haka ya mik'e da ita a hannun shi kamar y'ar tsana ,ya kwantar kan gado ya yi saurin koma wa kan wheelchair nashi ya zauna dan yasan zata iya farka wa any moment from now saboda baccin da tayi na wahala ne daman.
    Juyawa yayi ya bar d'akin ya nufi nashi flat d'in don yayi wanka.
Deenah kuwa bai dad'e da fita ba ta farka cikin magagin bacci ta mik'e don a lokacin an k'ira sallah ne ai kuwa k'afa ta rik'e ga wani ubansun ciwo ba shiri ta saki k'ara ta rik'e k'afar.
   Yana shirin fitowa dan zuwa masallaci ya jiyo ihun wanda hakan yasa ya nufi d'akin Deenah, tana zaune yadda take bata sake yin motsi ba har ya k'arisa gaban ta suka fuskanci juna. D'ago k'afar yayi ya fara ja, tun tana kuka tana masa magiya har ta hak'ura dan ba dainawa zai ba, sai da ya ji k'afar tayi masa daidai sannan ya mik'e ya nufi waje bai d'au lokaci mai tsawo ba ya dawo d'auke da tube na neurogesic ointment ya shafa mata a kaf'an..

    Ajiye mai d'in yayi ya k'ura mata ido hakan yasa ta d'ago idanuwa da guntun hawayen ta tana kallon shi. Shi kuwa wani dank'areren Murmushi yai sannan ya fice. K'asa k'asa
tace
"Mugu dai bazai tab'a canza halin sa ba"
Ta bashi dariya sosai ko da ya fice ma dariyar yake yi ita kuwa mik'e wa tayi a daddafe ta shige bathroom tayi alwala dan gudanar da sallar magariba.

   Hajiya, Ramlah, Sadeeq duk suna zaune a dining section don cin abincin dare da gangan Hajiya ta bugi cikin Sadeeq
"Abubakar! Ni kam ina y'ar tawa ne ? Ko baza ta ci abincin bane?"

  Sadeeq bai ce komai ba hakan yasa ta kashewa Ramlah ido suka yi dariya k'asa k'asa duk Wannan a idon Sadeeya ne, kai kawai ta girgiza ta cigaba da serving d'in su abinci.
   Har k'arfe goma Deenah na kwance kan gado tana game bata ma damu da wayar ta ba chaji ba. Sadeeya ta yi ta knocking amma bata kula ba don a zaton ta Mr Imam ne kuma dama can wutan d'akin ma a kashe yake dan haka da ta gaji ta fad'a bayi tayi alwala sannan ta dawo ta kwanta gami da Jan bargo.

  Sadeeq kuwa tun da ya ga bata fita sun ci abinci ba hankalin shi ya kasa kwanciya tunanin shi ciwon kaf'an ne. Amma ganin sun yi ta knocking bata bud'e ba haka yasa Sadeeya ta bar buga k'ofar kawai shi ma ya nufi d'akin shi amma duk cikin damuwa.
Hajiya kuwa suna komawa d'aki Shewa suka sa wai a ganin su Sadeeq bai shiri da Deenah shi yasa ko maganar ta bai son a yi.
"Ai na fad'a miki Umma cikin sauk'i zamu kawar da ita daga hurumin shi sannan mu cimma burin mu, musamman ma da Yaya baya son b'acin ran ki"
  Cewar Ramlah dake k'ok'arin kwanciya. Hajiya ta girgiza kai tace
"Umm Umm! Kar ki ganta haka kamar kazar mayu nasan ba zata zauna Shiru haka babu martani ba dole nasan akwai wani shirin da take shirya wa ke dai mu bi a hankali dan daga ganin idanuwan Abubakar ba k'aramin k'aunar ta yake ba. Ni nasan idan muka yi wasa kamar kashi zata mayar da mu a idanuwan shi dan haka dole mu tashi tsaye!"

  *Washegari*

    Tun da Deenah tayi sallar Asubah bata kwanta ba tana karatu har saida gari ya waye rana ta fito sannan ta mik'e ta shiga wanka.
  D'aure da towel ta fito hannun ta d'auke da wani towel d'in tana tsane gashin kan ta Stool ta ja ta zauna ta d'auko hand dryer tana busar  da gashin ,ko da ta kammala bata tsaya b'ata lokaci ba ta tsara kanta da wata kwalliya kai kace sarauniyar kyau ce a gaban ka. Kitse gashin tayi yayi jela ta dawo dashi kafad'a duk da ba tsayin a zo a gani bane amma Masha Allah ta fi Rookie kwakwiyes!

   Wani ash Swiss lace me pink flowers ta saka riga da zani plane sannan ta kashe dauri
"gosh fellas zo kuga Deenah yadda tayi matuk'ar kyau kamar wata first lady."
   Tana kammala komai ta feshe jikin ta da Arabian perfumes masu k'amshin gaske sannan ta zari wayar ta ta fice ,kai tsaye falo ta nufa downstairs yanda take taku sam baza ka ce k'afar ta na ciwo ba dan kuwa ta tafiyar da kanta ne cikin salon tsare wa da kuma kware wa.........

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245