MATATA GIMBIYATA 35-36

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         3⃣5⃣➖3⃣6⃣

     Ita kuwa Deenah na chan lungun gado tana kwance, tabbas taji shigowar Sadeeya kawai bata yi niyyar amsa mata bane.
   Mr Imam da kan shi ya sa Sadeeya ta shigo da shi flat d'in Deenah. Tsaya wa yayi yana k'arema d'akin kallo kafin ya umarce Sadeeya da Cewar zata iya tafiya , babu musu ta fice direct gami da tura k'ofar ta rife kirif.

  Shu'umin Murmushi Sadeeq ya sakar yana shafa  k'asumbar sa sannan ya kawar da kai yana kallon wayar ta dake jefe a k'asa kusa da gado.
   "Ni iya rayuwa ta ban tab'a ganin mace mai irin wannan zak'ewa haka ba, kiyi laifi Kuma Ki b'ata rai har Ki takura kan Ki a k'asan gado.? Abunda zai fi kawai Ki tashi kije kiyi apologising ma Hajiya, Ki bata hak'uri kawai."

  Deenah dake kwance a ranta tace
"ba dai hak'uri ba?
Zan bata Amma wlh duk ranar da ta sake yi min rashin mutunci ita ma babu abinda zai hana na mata rashin mutunci dan bazan bari a dinga cin kashi a kaina ba"
  Mik'e wa tayi ta mayar da hijabin ta sannan ta fice daga d'akin ko kallo Sadeeq bai ishe ta ba.
  Shi kuwa gyara zaman keken shi ma yayi cikin d'akin ya zauna gami da fuskantar k'ofa yana jiran dawowar ta.

  A hankali ta k'arisa cikin falon bata yarda sun had'a ido da Hajiya ba cikin ladabi ta bata hak'uri amma zuciyar ta kamar zata fito daga k'irji tsabar takaici.
Hajiya se wani shan kunu take tana taunar chewing gum, Deenah kuwa ta mik'e ta bar falon don bata damu ba, da Hajiya ta hak'ura da kar ta hak'ura duk Uwar Uban su d'aya.
  Dawowar ta d'aki bata lura da Mr Imam ba direct bayi ta shige ta watsa ruwa ta fito tana goge Jiki shi kuwa tuni ya sha ruwan jikin sa ganin dakakkiyar sura da Deenah ta mallaka, bai k'i ta zauna haka ba. Isar ta gaban madubi tana k'ok'arin zama kan stool karaf ta hango shi ai kuwa kamar ta ga aljani ta kurma ihu gami da mik'e wa zata gudu hakan ya sa Kwalaben turaruka dake kan dressing mirror duk suka fad'o aikuwa Deenah ta taka d'aya a garin guduwa Kwalbar ta ja ta da sulu bata zame ko ina ba se rigijib ta fad'o jikin Mr Imam hakan yasa ta zame daga jikin shi ta fad'o  k'asa shima ya k'asa rik'e kan shi dan keken ya riga da ya zame dan haka ya fad'o k'asa a kan ta wannan yasa ba shiri ta saki y'ar k'ara sannan ta lumshe idanuwa.

     Shi kuwa gogan tuni ya shige wata duniyar, ya ma manta inda yake yana k'ok'arin kissing Deenah ihun ta yasa ya dawo hayyacin sa.

  "Wayyo k'afa na! Dan Allah ka d'aga ni k'afa na !!"
  Mirgina wa yayi gefe ya jingina da gado yana maida numfashi ita kuwa kuka take yi rik'e da k'afar ta bata ma san da zaman shi ba.
Hannu ya kai zai tab'a k'afar, janye wa tayi gami da rik'e hannun shi tace
"Wollah in ka tab'a sai ya fi min zafi".
Baki a sake Mr Imam yace
"saboda hannuna borkono ne kawai sai yayi miki zafi?"
Kai ta girgiza tace
"A'a dai zai min zafi ne saboda kai mugu ne baka da tausayi"
  Kai Mr Imam ya girgiza yana Murmushi ya cije leb'en shi sannan yace
"tashi Ki mayar da ni kan keke na nikam tafiya zan yi kafin Ki cika ni da bak'ak'en maganganu da wata fuskar Ki a wajen."

   K'asa k'asa Deenah tace
"ba ga irin ta ba? Ni da k'afa na Ke ciwo ta Yaya zan tashi?"
Wani mugun dariya Sadeeq ya saki sannan yace 
"Toh fa? Matar gurgu don become gurguwa, yanzu gashi wheelchair guda gare mu. Amma kar Ki damu zan sa a kawo miki wani kema."

Wani k'ullutun bak'in ciki ne ya tsaya wa Deenah a wuya nan ta zuciya zata mik'e da gangan Sadeeq ya sa mata k'afa ta fad'o kanshi sannan ya k'ank'ame ta duk yadda tayi don ta kwace ta kasa haka har ta gaji da kokawan ta yi lakaf a jikin shi tana maida numfashi hannun ta guda dafe da k'irjin shi kamar wanda yayi mata magic nan bacci ya yi fintinkau da Deenah shi kuwa jin ta a jikin shi ya sa ya sake gyara zama tsabar shu'umanci har selfie yayi musu
"Drama Queen"
ya fad'a yana kallon pics d'in......

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245