MATATA GIMBIYATA 27-28

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         2⃣7⃣➖2⃣8⃣

    "Mommy yau kina nufin shi yayan ne yayi mata duk wannan? Kai amma wlh da na fita na sha kallo,"
Cewar Ramlah tana washe baki yayinda take Jere kafad'a da kafad'a da Hajiya kai kace k'awaye ne, Hajiya kuwa sai had'e mata k'arya da gaskiya take.
    Daren ranar dai daga Mr Imam har Deenah da Sadeeya babu wanda ya runtsa, a b'angaren Deenah tana mamakin mugun hali irin na Sadeeq Imam da har zai yi mata haka. B'angaren Mr Imam kuwa ji yayi kwata kwata bai yi dai dai ba ya kasa bacci sai tuna yanda ya hankad'e Deenah kan glasses d'in nan,da kalaman sa marasa dad'i, Sadeeya kuwa tsaka tsaki take duk ta basu abinci babu wanda yaci, haka ta kwashe su, ta dawo d'aki inda ta iske Deenah tana zaune kai had'e da gwiwa, zama tayi gefen ta tace
"Daman na fad'a miki duk wani k'arshen makirci ya k'are a gindin su, haka nake hak'uri da su, matar gida ma basu kyale ba balle ni da ba kowa ba y'ar aiki ce. Amma fa kada kiga laifin Oga sam ba laifin shi bane."
  A fusace Deenah ta d'ago jajayen idanuwan ta tace
"kina nufin  kenan laifi na ne?"

  "A'a"
Sadeeya ta bata amsa a tak'aice sannan ta mik'e taci gaba da cewa
"Laifin ta ne"
    Da sauri Deenah ta d'ago kai fuska da alamar rashin fahimta tace
"ita wa?"
"ZEE"
tsohuwar matar sa, kuma wanda ya bawa tsananin k'auna da kulawa, itace sila, ita ce silar shigansa wannan halin ba haka ya kasance a baya ba, kamata yayi Ki fahimce shi kafin Ki yanke mishi duk wani hukunci amma kafin nan zan so in baki labarin abinda na sani game da Oga na
  Iya abunda na sani shine yana matuk'ar k'aunar Zeenat wato Zee kamar yadda, ko da tuntub'e bai k'aunar tayi ballantana ta cutu haka suka ci gaba da rayuwa cikin tsananin soyayya duk da Cewar ita ma Zee tana fuskantar qalubale daga wajen su Hajiya amma ita ma ba kanwar lasa bace don in suka mata rashin mutunci a gaban Oga nunawa take bata ma san suna yi ba sai ya fice office ta gana musu azaba haka har Hajiya ta ga Zee ta fi k'arfin ta shine ta bar gidan daga nan nima na samu sukuni.
   Wata rana wani abu ya faru wanda ya chanja komai. An yiwa Zee waya daga asibiti Cewar Mijinta ya samu hatsari yana asibiti, cikin rud'ani ta nufi asibiti Jiki na rawa bayan Dr Bilal ya fito ya shaida mata Sadeeq ya samu matsala a spine nashi bazai iya komai kamar da ba. Tayi kuka kam, bayan wasu Watanni aka dawo da shi gida a Cewar shi in yana gida tare da ita zai dinga samun kwanciyar hankali akan asibiti.
    Tun ranar da aka dawo da shi gida Zee ta sauya halin ta, ko abu yake buk'ata sedai in yi masa kamar su abinci ko haurawa saman stairs, duk wasu responsibility ta soke, Cewar ta yanzu bazai amfane ta da komai ba, abin takaicin ma gaban k'awayen ta take fad'in haka, a kwana a tashi ba wuya har wata d'aya amma hali sai abunda ya k'aru har ma wani Alhaji ta samu mai bushe mata kunne kuma bata shakkar Sadeeq ya ganta ko yayi magana ma kamar a iska yayi daga baya ma kayan ta takwashe kayan ta da Cewar Sadeeq Imam bai da wata mamora kuma bazata iya zaman kula da k'ato ba. 

  Bayan tafiyar ta ne Aminin shi kuma PA a company d'in shi wato MAHMOUD ya dawo kulawa da shi, tare suka taso kuma shine mai bashi duk wata shawarar rayuwa, Shi ma Mahmoud tun ranar da aka kawo Ki kina Amarya bai sake dawo wa ba saboda temper d'in Oga yayi tsananin da babu wanda ya Ke raga mawa..

flashback ends

   Sadeeya ta d'ago kai ta dubi Deenah tace
"yanzu Ki fad'a min, Idan Kece zaki ga laifin shi? Kawai dai laifin shi d'aya ne ,ya kamata ya san cewa ba duka aka taru aka zama d'aya ba."
   Shiru Deenah tayi tana mai tausayawa Mr Imam a wani b'angaren kuma tsanar shi take bisa abunda yayi mata. Kawai ta yanke shawarar daga shi har Hajiyar ma bazata yarda su had'e idanuwa ba balle ran ta ya b'aci , ko maganin shi Sadeeya ta ba wa ta kai mishi.

   Zaune ta iske shi a kan wheelchair d'in tun d'azun bai sauk'a ba ya shiga duniyar tunani yana tuna irin cin mutuncin Zee da abunda yake aikata wa Deenah idanuwan shi kuwa jajir da su. Maganin Sadeeya ta ajiye hakan yasa shi d'ago ido yace
"Wait!"
chak ta tsaya juyowa tayi tace
"sir".
"Ki bud'e wa Madame d'in Ki flat nata, make sure bata rasa komai a ciki ba and make sure she is comfortable, tun da yanzu da Ramlah ta karb'i dakinta."
Kai Sadeeya ta girgiza tace
"OK  sir"...

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245