MATATA GIMBIYATA 55-56

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         5⃣5⃣➖5⃣6⃣

*On phone*

  Hajiya
"Haba Abubakar! Yanzu kana nufin har ka fice ka tafi ba tare da ka min sallama ba? Baka saba haka ba Lallai akwai wani abu"

Sadeeq
"am sorry na yi latti ne kuma zan yi missing flight shi yasa, ban tsayaba, yanzu ma I'll hang up saboda...."
  Bai k'arasa ba ta dakatar da shi ta hanyar cewa
"Ina buk'atar wasu kud'ad'e kuma gashi baka nan ya zan yi?"

  Wani shu'umin murmushi yayi yana tuna abunda yaji suna fad'a kafin
yace
"Hajiya kud'i akwai su, ki tambayi Deenah zata baki komai na hannun ta"
  Wani irin juyawa kayan cikin Hajiya suka yi ,kanta ya Sara a hankali tace
"Wace Deenah?"
"Hajiya Deenah d'aya nake da shi fa, ita zaki tambaya komai a hannunta yake se anjima, take care"
  Kashe wayar yayi yana k'are mata kallo kafin ya jinjina kai yace
"hmmph! Wai wace Deenah"

  "Ramlah duk yadda akayi ta tsafe shi ,har Yaushe ta shigo rayuwar Abubakar da zai yarda ya d'auki duk responsibility na gida ya d'aura mata, a dani kad'ai ke da wannan hurumin kuma ko Zee bata isa ta tanka ba, amma wannan kod'add'iyar makirar k'arshen zamani ce wallahi.
Ni dai bazan k'ask'antar da kai na ga ita ba.
  Ramlah tayi Murmushi gami da zauna wa
tace
"Kud'i zamu karb'esu , amma zan yi maganin shegiyar kwana kusa, Idan tana cin k'asa ta kiyayi na shuri"

   Deenah da Sadeeya suna shan iska a filin gida Ramlah ta iso inda suke, kunkumi ta rik'e tana k'are musu kallo daga sama har k'asa sannan ta hararo Sadeeya cikin hasala tace
"ke! Uban mi kike a nan? Har kin gama girki kenan?"
kai Sadeeya ta girgiza kafin tace
"gas ya k'are kuma rana tayi sai gari yayi sanyi zan tafi shopping Orders from Madame".

   Ramlah ta saki baki wangalele cike da mamakin Sadeeya
"Iyeeee! Tirk'ashi, wannan shine ana wata ga wata! Y'ar aiki da ke har kina da bakin tanka wa y'ar gida? Koda yake ba laifinki bane duk laifin tane "
Ita dai Deenah bata ce komai ba ,mik'ewa tayi ta bar ta a tsaye ko a jikin ta, Ramlah kuwa bak'in ciki ya ishe ta , tabi bayan Deenah har d'akin ta

  "Me gidan ya ce ki bani kud'i in kai wa Hajiya"
  Deenah ta d'auki wayar ta tayi dialling numbern Sadeeq da yake amfani da shi a can,
"Me kuma zakiyi?"
Ramlah ta tambaya
"zan tambayi mai gidan kin san bazan d'auki k'adararsa in banzatar a banza ba ba tare da yai min izini ba."
Ramlah dai daskarewa tayi tana kallon ta....

   Zaune yake kan kujera yana amfani da computer amma hankalin shi ya karkata zuwa tunani, mamaki yake yadda Hajiya take shirin cutar dashi kawai don dukiya, he can't imagine how selfish she is, bai ma san hawaye yake ba. Wayar shi ce tayi k'ara dan haka ya maida duban shi ga screen d'in, ganin wanda ke k'ira yasa ya goge hawayen shi sannan ya d'aga wayan tare da sa Murmushi.

"Missing me already?"
Ya fad'a yana langab'ar da kai sannan yaci gaba da cewa
"ai da baki kira ba ma da yanzu zan kiraki "

   Wani haushi Deenah taji a ranta tace
"ji yadda yake fasa kai ya d'auka na wani damune dan baya nan"

"Kawai na kira in fad'a maka Ramlah tace Hajiya na buk'atar kud'i, ni ban san kan abun ba"

  Murmushi yayi yace
"ki bata duk amount da ya kwanta miki a rai, take care! Yanzu zan shiga wani important meeting I'll call you later"
"Ok"
  shine amsar Deenah tana kashe waya ta juya idanuwa k'asa k'asa
tace
"Wannan shine daidai! Zaku Rena kanku yau."

  Key ta d'auka ta shige gaba Ramlah na biye da ita har k'ofar Sadeeq, juyowa tayi ta d'aga hannu a Deenah
tace
"nan ba hurumin ki bane pls wait outside"
nan ma Ramlah har saida purse d'in hannunta ya fad'i k'asa dan mamakin Isar da Deenah ke nunawa.

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245