MATATA GIMBIYATA 57-58

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

PAGE DINNAN NAKUNE BESTY ZARAH BUKAR MY LOVELY DOTA MISS XOXO ND SWEETHEART HAFSAT RANO #1love♥
#Ana tare
#if you know you know kawai👍🏻

         5⃣7⃣➖5⃣8⃣

   Haka ta jira Deenah ta fito da bunches na dubu d'aya guda biyu a hannunta gami da mik'a mata.
  Juya kud'ad'en Ramlah tayi kafin ta d'ago ta dubi Deenah tace
"two hundred thousand? Me Wannan zai mana?"
  "Haka naga daman bayarwa, kin mayi sa'a da d'ari Daya zan baki fa"
Cewar Deenah dake k'ok'arin rufe k'ofar, tana rufe wa kuwa tayi tafiyar ta.
  Ramlah kam gaba d'aya ranta a dak'ile yake bata gane me yake faruwa ba.

    Babban tashin hankalinma sai da Hajiya taga kud'in, ita cewa ma tayi Ramlah ta maida kud'in daga baya kuma ta fasa ta amshe su gami da sa wa a jaka ta fice tana huci suka bar gidan.
  Tun daga nan Hajiya da Ramlah suka daina tanka wa Deenah ita ma hakan yai mata daidai don bata k'aunar ganinsu ma,
Cikin kwanaki shida da Sadeeq yayi kullum dare zai kira Deenah tsabar Jan ajin sai taga daman d'auka haka sati ya shige kamar kyafta ido.

     ☁☁☁☁☁☁

     Tun fitowar shi daga babban filin jirgin Nnamdi Azikwe yake kiran wayar ta amma babu amsa, Mahmoud ya hango tsaye yana Murmushi jikin motarsa, kai tsaye ya nufi inda yake suka gaisa ba tare daya sake magana ba ya shige motar Mahmoud ya Mak'e kafad'a shima ya shige zai ja motar. Saida suka hau hanya Mahmoud yace
"ya dai? Naga kamar kana cikin damuwa?"
Sadeeq ya Furzar da iska daga baki yace
"Its my wife, naita kiranta bata d'aga waya,"
Dariya sosai Mahmoud yayi yace
"Toh yanzu kam ba gashi ka dawoba? Ta d'aga kar ta d'aga ai yanzu kam zaka jame da ita, miye kuma na damun kanka?"
Harara Sadeeq ya watsa masa shi kuwa bai san ma yana yi ba.

   
     Da sallama ya shigo falon babu kowa sai Sadeeya wanda ta cika da farin cikin ganin shi da k'afafun shi, jakar ta karb'a ta nufi d'akin shi. Kai tsaye ya nufi kitchen ya bud'e fridge ya zuba ruwa yana sha gami da k'are wa kitchen d'in kallo kafin ya fice ya nufi upstairs.

  Da gudu take sauk'owa shima cikin sauri yake hawa basu ankara ba suka ci karo which send them rolling down the staircase, iya k'arfin shi ya rungume ta gami da rik'e kanta da hannun shi d'aya don kar tabugu. Basu daina rolling ba har sai da suka kawo k'arshen stairs se haki suke their eyes locked , saida ya tabbatar ta gama samun nutsuwa tukunna yayi kissing nata gami da sakar Murmushi ya kashe ido d'aya kafin ya mik'e. Hannu ya mik'a mata don taimaka mata ta tashi amma ko kallon inda yake bata yiba tamik'e da kanta tana d'ingishi ba tare da ta bari sun had'a ido ba ta juya zuwa cikin falon ta zauna sai duba hannunta take yi inda ya kuje shi kuwa first aid kit ya d'auko ya sa disinfectant a jikin cotton ya kai hannu zai kama hannun ta janye, kawai ya k'ura mata ido ganin zai had'iye ta da kallo yasa ta mik'a hannun yana goge mata yana hura iska har ya gama
"Thanks"
ta fad'a murya ciki ciki, dariya yai kawai ya mik'e ya haura zuwa d'akin shi.
Ita kuwa kitchen ta nufa don dama yunwa take ji ,ko da ta deb'o abincin flat nata ta nufa dan bata son ta zauna yan bala'in nan su fito su dameta, a hallway suka had'e ya fito yana nemanta, kuma ga Hajiya a gefen shi suna tsaye
"Yawwa munafuka!" Cewar Hajiya ta rik'e kunkumi ,Deenah saida gaban ta ya fad'i domin tayi mugun tsorata ranar da Hajiya, tunda tagan su tare tayi tunanin akwai wata mak'ark'ashiya
Sadeeq ya d'ago yace
"Deenah ke kad'ai na bawa access to my bedroom, me ya faru? All the money is gone? Kuma haka wasu documents ma, ina kika kaimin su?"
  Deenah tun da aka haifeta bata tab'a jin tashin hankali irin na Wannan ranar ba duk ta daburce ta kasa magana ta ture Sadeeq daga hanya ta kutsa kai cikin d'akin only to find nothing inside the shelf se takardun company d'in shi guda d'aya hankali a tashe ta juyo baki na rawa tace
"Wlh ban san inda kud'in ka suka shiga ba, believe me bani na d'auka ba"

  Murmushi Sadeeq yayi yace
"pls Deenah !Hajiya ta fad'a min babu d'aya daga cikin su wanda kika bawa access to my bedroom Toh Yaya haka ta faru? Let's just go straight to the point!  Ki fad'a min inda kud'ina suke. "

   "Wlh Allah ban d'auka ba yanzu in har zan yi Wannan satan kana tunani zan zauna a nan ne? Tun da Nazo gidan nan ko k'afa ban sa waje ba don haka in baka yarda da ni ba ka yi bincike tunda duk inda na kai da satar bazan wuce cikin gidan nan ba"
"Annamimiya ai hakan ma zaifi, Abubakar kayi binciken, muje d'akin naki"

  Deenah na kuka ta shige gaba su Hajiya aka bita a baya har d'akin ta Sadeeq kuwa yasa hannu a aljihu idanuwan sa sun kad'a jajir ya bi bayan su ya dafa kafad'ar Deenah ba tare da Hajiya ta gani ba yace
"Relax! Worry not please"
ganin Hajiya ta juyo yasa ya shige yana kallon ta, salati ta fara doka wa tana kuka

"Oh Allah! Ashe b'arauniya ce aka auro maka! Rayuwa zata yiwu a haka kuwa? Wai ace yaro irin Abubakar baya had'uwa da matan kirki sai na tsiya?."

Tana maganar ta d'auko jakar kud'in tare da envelope d'in takardun
"an dai ji kunya wallahi"
  A take wani abu ya tokare wa Deenah wuya ko miyau ta kasa had'iya ,da gudu ta nufi inda Sadeeq ke tsaye tana kuka tana fad'in
"Wallahi ban san yadda akayi suka zo d'aki na ba, ni ban tab'a sata ba pls try and understand"

Hannuwanta jikin rigar shi duk ta chakume shi har ta gaji da kanta ta zube a k'asa tana matsanancin kuka. Juyawa yayi ya bar d'akin ya nufi d'akin shi Hajiya kuwa abin nema ya samu sai gori da banbami.
  A kwance take k'asa sai kuka take kamar ranta zai fice gashi babu wanda zata kaiwa kukanta, bata da kowa dangi ba k'aunar ta suke ba bata taso cikin soyayya ba kuma ba gata take da shi ba ta rasa tunanin da zatayi domin Lallai tana cikin tashin hankali da d'imuwa..........

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245