MATATA GIMBIYATA 41-42

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         4⃣1⃣➖4⃣2⃣

  "Jar Uban can! Amma tunda aka haifen ban tab'a ganin makira irin wancan lankwashashiyar Deenah n ba! Ko munafurci ma tsoron ta yake. Amma tunda tace ita y'ar wasa ne ni kuma captain ce! Bazan tab'a barin ta ba wlh se na cimma buri na "
  Ramlah dake tsaye jikin k'ofa ta saki doguwar tsaki tace
"Ummah abun takaicin ma kin ga yadda take masa tausa yadda kika san wasu turawa Umma wallahi bak'in cikin da naji baki ji shi ba dan wallahi ni na so in shak'e Deenah d'azun, wai daman akwai wata kuchaka irin Deenah da zata iya tanka miki? "
   Hajiya tayi dariyar manya tace
"Yaro yaro ne! Ai kuskuren mu d'aya ne kawai, da tun farko ya kamata mu fara shafe Deenah daga rayuwar Abubakar amma tunda bamuyi hakan ba salon da ta d'auko shi zamu d'auka sannan mu shafe ta domin in muka nuna b'acin rai toh Lallai hak'ar mu bazata cimma ruwa ba yarinyar akwai kwakwalwa daga gani ta san me rayuwa take ciki kuma zata iya gane dalilin zaman mu a nan gidan zai fi mana kyau mu bi shegiya yadda take bi da mu"
  Shewa Ramlah ta saka sannan tace
"sai Mama! Ni yanzu ma har kin sa na d'an ji dad'i barin yi in shirya na fice dan yau akwai birthday party d'in wani friend d'ina da za'a yi yau dole na jajigee"
  Kai Hajiya ta jinjina tana Murmushi tace
"yi maza ki shirya nima akwai siyayyar da zaki min , in kin je shopping"
  "Toh"
shi ne amsar Ramlah ta shige bayi tana dariya hajiya kuwa ta kishingid'e amma a hankali take tuna irin abubuwan da Deenah tai mata.
Cike da bak'in ciki Ta yi wurgi da cup d'in hannun ta gami da Jan tsaki.

   Har yanzu Mr Imam bai sassauta rik'on da yayi mata ba ita kuwa bata bari sun had'a ido ba. K'arar wayar shi ne yasa ya sake ta ya zaune dan amsa wayar.

   Ya dad'e yana wayar wanda da alama daga wajen aiki ne Deenah kuwa tuni tayi bacci har d'ankwali ya fita. Yana kammala wayar ya juyo ya k'ura mata idanuwan shi kamar zai had'iye ta. Ganin baya jin bacci yasa ya d'auki wayar shi yana exploring internet, sam bai jima ba yaji Deenah ta fara wasu irin maganganu daga gani mafarki take yi mai tsoratar wa karo d'aya gumi ya karyo mata Jiki ya fara rawa tana fad'in
"dan Allah uncle khamees kayi hak'uri Kar ka kashe ni,"
abun da take ta maimaita wa kenan. Sosai Sadeeq ya tsorata ya fara jijjiga Deenah don ta farka amma duk ta k'ank'ame shi  tayi squeezing rigar jikin sa.

   Ganin tana fiffisgewa yasa ya yi hugging nata so thigh yana k'ok'arin kwantar mata da hankali, sai lokacin ta fara dawowa hayyacin ta gumi duk ya jik'ata kamar tai wanka.

   A hankali ta d'ago suka had'a ido da Sadeeq wanda har yanzu mamakin irin firgici da ta shiga yake yi sannan ta zame jikin ta daga nashi zata tashi Sadeeq ya dakatar da ita ta hanyar rik'e  hannun ta. Da k'arfin gaske ta fisge hannun ta sannan ta mik'e ta bar d'akin zuwa nata d'akin inda ta zauna tana tuna irin uk'ubar da su Uncle d'in ta suka sa ta, irin wahala da cin mutuncin da suka mata da yadda suka zaune kan gadon ta kamar dukiyar su ce.
"Allah Sarki Mutuwa me raba d'a da mahaifi, da iyaye na suna raye da bazan shiga k'uncin rayuwa ba"
  Cewar Deenah tana zubar da kwalla.
     Hannun shi yasa yana share mata hawayen yace
"Allah ya jik'ansu".
A tsorace ta d'ago tana kallon shi bata ma san lokacin da ya shigo ba.
  "Ameen"
  ta amsa masa a takaice sannan ta k'irk'iro Murmushi tace
"Ni ban rayu cikin jin dad'i ba, ban samu na sake da mutane ba, an doke ni an cutar dani , sun rabani da duk farin cikin rayuwa sun bani wahala ,sai gashi duk da na yi nesa da su har a mafarki ma bibiya ta suke yi"

   Mr Imam wanda ya dad'e da sanin asalin Deenah da yadda tayi rayuwar takaici ya tausaya mata sosai dan haka ya fara bata hak'uri har ta daina kuka ta mik'e ta nufi bathroom ta wanke fuskar ta tafito sannan ta zauna bakin gado, Sadeeq ya duba agogon shi yaga sha d'aya dan haka yayi mata sallama ya fice dan yana da inda zai je yana so su had'u da Dr Bilal........

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245