MATATA GIMBIYATA 59-60

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         5⃣9⃣➖6⃣0⃣

   Dakyar Deenah ta daddafa tayi sallar isha kanta har sarawa yake a fusace ta mik'e ta nufi wardrobe ta sauya kayan ta zuwa doguwar Aseel jallabiya bak'a sannan ta yi Rolling kanta da mayafin shi ta zari takalman ta k'irar Vinci ta saka, ko waigo d'akin batayi ba ta fice tana rik'e da wayarta, yadda ta fito a fusace tayi waje yasa Sadeeya ta haura don sanar da Sadeeq amma sai ta iske yana waya, tayi tsammanin zai kammala da wuri amma taga akasin hakan don haka tace
"Madame fa ta bar gida"
  Sadeeq Bai san lokacin daya zame daga kan gadonshi ba yace
"What?!!! "
Sadeeya ta maimaita masa abunda ta fad'a , kamar mahaukaci haka ya zura aguje ya d'au car keys yasa maigadi ya bud'e gate amma kafin ya fita Saida ya fara firing gateman wai bai iya aikin sa ba.
  Haka yabi hanya yana baza idanuwa ta ko ina yana fatan ya ga Deenah.
Burkin mota ya ja cike da tashin hankali sanadiyyar wata mata da ta fad'o gaban motar Allah Allah yake baiji mata ciwo ba ,Jiki na b'ari ya fita zai d'aga ta amma ta mik'e tana fad'in
  "Pls let me die! Its the only option! No one trust me, na tashi cikin kad'aici ku barni na mutu a haka am tired of everything! Wanda ka soshi da zuciya d'aya ma zargin cin amana yake maka Toh meye ribar rayuwa?"

   Wani daskarewa Sadeeq yayi yana kallon ta duk surutan da take yi kawai kallon ta yake tabbas ta bashi tausayi. Hannu ya kai yana k'ok'arin tab'ata dakyar bakinshi ya furta sunan ta.
  Zaro idanuwa tayi waje data ganshi
"You? Me zaka fad'a min? Get your hands off me! Tunda mutanen da suke shirin kasheka sunfi wad'anda suke k'aunarka daraja ! Ni ban tab'a sata ba kuma bazan tab'a ba wallahi kun cuceni kuma Allah zai saka min"
a fusace ya daka mata tsawa wanda har wad'anda ke gefen titi saida suka juyo
   "Deenah!!!! Tabbas ke b'arauniya ce!"
Zaro idanuwa tayi baki bud'e tana kallonshi

  "Eh!! Eh Deenah kin sace zuciyar Abubakar Sadeeq Imam, dan haka zan sake fada ke b'arauniyace."
Kai ta sunkuyar k'asa tana kallon yatsun ta taji ya rik'e kafad'un ta
yace
"Deenah ni nasan ba ke kika yi sata ba pls kiyi hak'uri ki biyo ni I'll explain everything dan Allah Deenah"
kai ta girgiza gami da zame hannunshi daga kafad'arta gami da cigaba da tafiya yana bin ta sai sauri take ,da gangan ta zura da gudu shima Sadeeq ya bita a guje ya chafke ta gami da matse ta a jikin shi duk da kokawan da take bai saketa ba har tayi laushi ta saduda.
  A kunnen ta ya rad'a mata
"pls ya isa my princess, shhh relax just come with me I'll explain dalilin da yasa ban kula ki ba amma ina so ki sani ina matuk'ar k'aunar ki Deenah, I dearly love you"
   sai daya d'an janye jikin shi daga nata kawai yaga ashe ta sume ,k'asa ya durk'ushe tana hannun shi yayi juyin duniyar nan bata tashi ba
Mota ya nufa da ita ya tuk'a amma ba gida ya nufa ba ,gidan  Dr Bilal ya nufa yana yin horn aka bud'e gate ya kutsa kai Dr Bilal ya hango shi daga window da kuma halin da yake ciki hakan yasa ya bud'e k'ofa hankalin shi a  d'age Sadeeq ya shigo
"Dr pls help me bata motsi sam......"


  Hajiya ce zaune tayi fankan fankan a kujera dariya harda hawaye ita da Ramlah har da zamewa k'asa
"I told you my daughter wasa d'aya kadai zan buga in tarwatsa mata komai yanzu Allah kad'ai yasan irin bomb da suke tayar wa domin yanzu babu sauran yarda tsakanin su."
Ramlah tace
"gaskiya naso ace ina wajen mommy ke ta musamman ce !"

  Sadeeya kuwa kamar wanda aka yiwa mutuwa ta kasa bacci hankalinta na kan k'ofa both Oga and Madame basu dawo ba fatan ta Allah yasa lafiya.

    Sadeeq na gefen gado ya k'ura mata ido bata farka ba duk da Dr Bilal ya bata taimakon gaggawa  gaba d'aya hankalinshi a dak'ile yake  ya rasa yadda zaiyi.
"My friend ya kamata kai ma ka samu bacci you are stressed out, dubi yadda ka zube cikin y'an lokuta, ka fawwala wa Allah ,shi zaiji da komai amma shawarar da zan baka shine ,inma kayi nisa da Hajiya ko kuma matarka tayi nisa da kai, yanzu an riga da anyi walk'iya kowa ya ga kowa, kasan mai k'aunarka saboda Allah kasan kuma mai k'aunar abun daka tara, kayi tunani tunda har Deenah ta k'osa ta fice zata bar gidanka Toh Lallai kana gab da rasa ta kuma ina da yak'inin cewa in ka rasa ta zaka iya rasa ranka."
  Sadeeq ka nemawa Deenah sauk'i, in dai zakabi ta tawa ka dawo da ita sabon mansion naka dake Maitama district can babu wanda zai takurata sannan kayi maganin matsalarka da Hajiya, amma in ka barsu Hajiya will keep taking advantage of her"
  Kai kawai Sadeeq ya jinjina yace
"thank you"
daga nan suka fice daga d'akin suka koma falo jiran lokacin da zata farka.

Washegari.

   Bud'e idanuwa tayi tana k'arewa bak'on wajen da take kallo, a hankali ta zauna ta dubi drip dake hannunta tafisge gami da mik'ewa ta rik'e kanta. K'ofar d'aki ta nufa taga dai wani gida daban take , sao lokacin ta fara tuna abunda ya faru da dare jiya dafe kai tayi tace
"kash!! What have I done?"

Tana nan tsaye ta hango shiya shigo d'auke da glass na ruwa, shima tsayawa yayi yana kallonta kai a sunkuye dan tak'i d'ago kai ta dube shi.
  K'arasowa yayi kusa da ita ya mik'a mata ruwan da kyar ta karb'a ta d'an kurb'a sannan ta mik'a masa, hannunta ya kama suka fita main parlour dai-dai lokacin Bilal ya fito ya shirya tsaf zai tafi aiki
"Amaryarmu Yaya Jiki? Sorry fa ba'a yi breakfast ba kin sanni d'in gwauro ne Madame bata nan let's eat out"
  Murmushi Deenah tayi dan ya bata dariya tace
"I can cook in ba matsala"
Zaro ido Bilal yayi
yace
"rufa min asiri please! Kar ki sa Mutumin ya bani naushi ke da baki da lafiya? Kawai kuzo mu tafi kar nayi latti"

   Tun da suka kammala breakfast Bilal ya wuce Aiki Sadeeq kuwa mota suka shiga ,a zatonta gida zasu Amma akasin hakan shopping mall ya wuce da ita.
Da kyar yasa ta bishi cikin shoprite dan ko kulashi bata yi.

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245