MATATA GIMBIYATA 47-48

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         4⃣7⃣➖4⃣8⃣

     Tun da ta shiga kitchen take sak'e sak'en yadda zata yi maganin Hajiya, cije leb'e tayi sannan ta fara haramar yin girki tsabar tsiya ruwa Deenah ta d'aura bayan ta soya mai da albasa sannan ta jajjaga attaruhu mai Uban yawa ta d'irka a ciki sannan ta gabza kayan k'amshi da seasonings hakan yasa duk yadda k'amshi ya kai Wannan girki ya kai. Cikin y'an mintina ta kammala komai. D'an kad'an ta saka a bakin ta don jin yadda yajin yayi ita kan ta saida ta kurb'i ruwa. Sannan tayi wata dank'areriyar Murmushi gami da zuba wa a plate ta fito d'auke da roban ruwa mai uban sanyi ta ajiye gaban Hajiya  sannan ta koma setin ta tazauna tana jiran wasan ya fara.
    Cike da isa ta bud'e plate ,zo kaji yadda k'amshi ya rufe ko ina su Hajiya har yawu ya tsinke, bata tsaya b'ata lokaci ba ta takarkara ta doka loma ,ga zafi ga yaji,ga ga ga!!! Ba abun ta Furzar ba Deenah tayi mata dariya Idan tak'ici Deenah zata samu hanyar sabon rashin mutunci Idan kuma tayi magana Sadeeq zai iya suspecting wani abu kuma ta fi so yanda suka fara gwabza wa da Deenah su cigaba a haka. Gashi ba abun ta mik'e ba ta bar wajen Deenah zata iya yin abinda ba ta ruga, kenan ma tayi accepting defeat dan haka ta sake kai loma karo na biyu tana k'irk'iro Murmushi. Deenah kuwa cikin ranta tace
"Ci dai munafuka yau zan ga bakin dake zagar min iyaye"
    A yayin da Hajiya ta antaya loma ta Uku har ta fara hawaye ga zufa tuni hanci ya fara yoyo amma saboda k'arfin hali ta dake tace
"Abubakar kai bazaka ci abincin bane?"
nufin ta shi ma a zuba masa yaji irin ta'asar da matar sa tayi amma sai ya girgiza kai
yace
"Umma kin manta bana cin macaroni ne?"
Kai ta girgiza baki dalala tace
"shhh Uhh!  Sorry ......na shhhsh... Manta wlhy."
   Deenah kuwa duk iya k'ok'arin ta tayi dan matse dariyar ta ta kasa saboda haka ta haura upstairs bata zame ko ina ba sai d'aki ,ai kuwa tana tura k'ofa  yadda kasan comedy hall haka d'akin ya koma tsabar dariya Deenah har da rik'e ciki ta yi tsalle kan gado tace
"ai kad'an ma kika gani"

  Hajiya kuwa tun tafiyar Deenah ita ma cikin tafiyar agwagi ta nufi kitchen ta fara kokawa da fridge inda ta hango Kwalbar Zuma ai kuwa ba b'ata lokaci ta bud'e Kwalbar ta antaya a baki  da kyar ta samu bakin ta ya daidaita sannan ta dawo falo ,sai lokacin ne Sadeeq ya d'ago kai ya dubeta yace.
"Daman ina son fad'a miki Cewar gobe zan tafi Egypt don duba lafiya ta akwai wani babban likita yace zan iya sake tafiya da k'afafu na."
   Wani wahalallen gumin ne ya sake karyo wa Hajiya cikin ranta
tace
"Da alama dai nikam yau ban tashi da sa'a ba ,ita matar tana harbi na da alburusai amma shi tashin farko makamin k'are dangi ya wurgo min! Ai warkewar Sadeeq daidai take da fad'uwa na warwas gaskiya dole nasan abin yi."

  "Hajiya"
Yaya naji kin yi Shiru? Hope all is well babu wata matsala ko?

A firgice ta d'ago daga dogon daydream da ta tsunduma tace
"Ahaah A'a Babu komai Allah ya nuna mana dana nayi matuk'ar farin ciki "
  Ya amsa da
"Ameen"
sannan ya cigaba da kallon da yake .

  Simi simi ta mik'e kai tsaye ta nufi d'aki tana maganganun zuci tana neman Hanyar da zata bi dan hana Sadeeq yin Wannan tafiyar.

  Waya ta d'auka ta k'ira Ramlah dake fama da shopping tace
"kiyi maza ki dawo dan akwai Babban matsala"
"Toh"
shine amsar Ramlah sannan ta ajiye wayar.
Tsabar tsurku da son jin kwakwaf Ramlah bata kammala shopping ba ta dawo gida don jin dalilin kiran da Hajiya tayi mata, A falo ta iske Sadeeq Shiru shi kad'ai dan haka ta k'arasa ciki da sallama, da Murmushi ya amsa ta gaida shi sannan tace
"ya naga kai kad'ai Yaya? Ena Auntyn nawa ? Ai zaman ka Shiru haka ba dad'i."
   Murmushi yay mata yace
"yanzu ta shiga ciki ,don't worry dear sis, kawai abunda ya dace kiyi yanzu shine ki kai ni d'aki"
  Cike da ladabi amma irin na kunama ta tura shi har d'aki sannan ta nufi d'akin Hajiya.
"Hajiya amma nayi mamakin yadda kika kira ni cikin gaggawa Allah yasa de lafiya"?
"Ba lafiya ba! Nace ba lafiya ba Ramlatuh!!"
  Nan Hajiya ta kwashe duk badak'alar da Deenah ta aikata mata d'azu ta labarta mata .
"Amma duk ba wannan ba, yayanki wai ya samu likita da zai masa maganin ciwon shi a Egypt, kin san me hakan yake nufi? Total lost! Mun fad'i warwas, ni buri na mu mallaki dukiyar Abubakar amma in ya warke hakan bazai yiwu ba saboda zai koma kan aikin sa kinga once again Mun yi losing chance"

"Dank'ari!"
Cewar Ramlah tana k'ok'arin d'aura mayafin ta a k'irji tace
"Umma dole mu d'auki mataki"

Kai Hajiya ta girgiza
tace
"ai Mun makara, yo ana zancen gobe zai tafi ina muka ga time d'in shiri"
   Duk hirar da suke yi a kunnenshi tun yana hawaye har gumi ya keto masa jikin shi yayi sanyi bai san lokacin da ya juya akalar wheelchair d'in ta yi reverse ya nufi hanyar d'akin shi............ .

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245