MATATA GIMBIYATA 53-54

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

        5⃣3⃣➖5⃣4⃣

    Koda Sadeeq ya dawo d'aki ya wuce bai fito ba sai da ya tabbatar ya shirya tsaf in black suit komai normal sannan ya ja trolley d'in shi zuwa k'ofa kafin ya ajiye, kai tsaye d'akin Deenah ya nufa inda ya iske ta kan sallaya, ko da suka yi ido hud'u mik'e wa tayi ba tare da ta kalli inda yake ba ta nad'e sallayar sannan ta ajiye tana k'ok'arin zare hijab.
  Hannun ta ya fisgo har saida k'irjin su ya bugu dana juna, ba tare da ta d'ago ba ta fara k'ok'arin wafce hannun nata tana ja da baya yana matsowa har ta had'e da bango.
   Ganin babu mafita yasa ta tsaya idanuwan ta kan hannun shi da yayi mata zobe a bango da shi.
Zan tafi Egypt"
ya fad'a cike da shu'umanci, sannan ya cigaba da cewa
"Its more like a business trip sati d'aya zan yi but mind you kada ki kuskura ki sanar musu cewa ba ganin likita zan je ba"
   yana kai nan yayi Murmushi gami da manna mata quick peck a kumatu.
Had'e girar sama da na k'asa tayi bata tanka mishi ba sai da ya juya zai fice ta rik'e hannun shi, cak ya tsaya yana kallon hannun ta jikin nashi da gangan ya juyo girar shi d'age
yace
"Woah!! Missing me already?"
  Sake hannun tayi gami da kawar da kanta rai a b'ace
tace
"daman lafiyar ka kalau?"
   Shiru yayi kamar mai tunanin wani abu kafin yace
"We'll talk about this later "
   bai jira amsar ta ba yaja hannun ta zuwa d'akin shi ,wani locker ne manne a bango ya nuna mata
"if you need money kafin na dawo ki d'auka a ciki sannan stay away from Hajiya da Ramlah duk abunda zasu miki kar ki tanka, nasan ma hakan ba mai yiwuwa bane but please kar ki biye musu"

    K'asa k'asa Deenah tace
"why does it sound like my Mummy is trying to be protective?"
Karaf sai kunnen Sadeeq hakan yasa ya tsaya kallon ta kawai daga nan bai ce komai ba ya zauna kan wheelchair yadda ya saba wai Deenah ta tura shi.

   A hankali ta d'ago ido ta dube shi zaune yana wani danna waya k'asa k'asa tace
"a da dai bansan wa nake tura wa ba Amma wlhy bazan tara wa kai na gajiya in tura k'ato ba"
  da gangan ta k'ira Sadeeya dan ta kaishi downstairs ita kuwa ta ja akwatin shi se banbami take
"wanda zai yi sati ya jibgo kaya kamar mai tafiyan wata biyu"

   Kai tsaye yasa Sadeeya ta kai shi mota ba tare da sun yi sallama da su Hajiya ba Deenah daman ba k'aunar had'uwa da su take ba hakan dad'i yayi mata.
  Ko da ya shiga motar Deenah ta saka akwatin sa a truck ta juya zata tafi cikin sauri ya sha gaban ta da mota har saida ta tsorata da yadda ya ja birki, from head to toe ya Ke duban ta kafin yace
"Ki kula min da kanki "
juyawa tayi ta barshi tana fad'in
"an fad'a maka ni d'in taka ce da zan kula maka kai na? Lallai ma."

    Murmushi yayi yana shafa k'asumbar sa cikin wata shu'umar murya yace
"Believe it or not you are mine! My princess"
daga nan ya ja motar sa ya k'ara gaba.......

      Tun dawowar ta daga rakiyar Sadeeq tayi kwanciyar ta a falo tana game ko break bata yi ba.
  Da k'asaita Ramlah ta fito tana hararar Deenah har ta k'araso inda take.

"Ke! Ke!".
Duk da Deenah tasan da ita take bata ko d'ago kai ba,
"Ba dake nake magana ba? Ina Yaya na?"
Sai lokacin Deenah ta d'ago ta gyara Wuyan rigar ta sannan tace
"Kin bani ajiyar yayan ki ne? Pls da sassafe nan kar ki dame ni da haushi. haba sai kace kare?"

"Jar Uban can !!
Ni kika k'ira da kare? Lallai Wuyan ki yayi kwari zaki ga abinda zai biyo baya"
tana kai nan ta wuce fuuuuu ita kuwa Deenah mik'e wa tayi ta nufi dining ta zuba abinda ranta yake so ta ci sannan ta nufi wajen Sadeeya suka kafa hira.

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245