MATATA GIMBIYATA 61-62

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         6⃣1⃣➖6⃣2⃣

   Babu abunda ta d'auka sai binshi takeyi, koshi kanshi yasan ba abunda zata d'auka domin dama ba da niyya ta shigo ba ma ahaka har yayi gaba ya barta tana tafe kai a k'asa, bata ankara ba taci karo da mutum harta jefar masa da waya ta durk'usa k'asa ta d'auko wayar ta mik'a gami da d'ago wa dan bashi hak'uri.
   Gaba d'aya in zaka bincika Deenah a Wannan lokacin ta riga tasha jinin jikinta, idanuwanta da bakin ta wangalele ta kasa ko da motsi mutuwar tsaye kam tayi yafi so Arba'in a lokacin nan dan danan jikin ta ya d'au b'ari ko had'iye miyau ta kasa yi balle magana.
Ai kuwa ba shiri ta ranci na kare tun k'arfinta tasa a gudun daidai lokacin Sadeeq ya juyo sai ji yayi ta fad'o jikinshi gami da rungumeshi iya k'arfinta kuwa ta chakume rigar shi kai kace yagata zaiyi, bugun k'irjin ta da saukar numfashin ta sune suka sanar dashi firgicin da take ciki.

  Da kyar ya iya d'ago fuskarta yana k'ok'arin su had'a ido amma ta k'ank'ame ido ta cije leb'en ta tana girgiza kai ga hawaye d'aya na bin d'aya, juyawa tayi ta sake had'a ido da Mutumin wanda yanzu kam inda suke ya doso ai kuwa ta k'ara gigice wa tana fisgo hannun Sadeeq shi kuwa ya tsaya kallon Mutumin data gani d'in hannunsa kuwa na shan fisga. Ganin tana neman shid'ewa yasa Sadeeq ya juya suka tafi, bata jira ya biya kud'in ba ta nufi mota , saida ya gama ya biyo ta ya shiga kai tsaye ya ja motar bai zame ko ina ba sai babban gidan shi dake Maitama district.

    Tun daga gate Deenah ta saki baki tana kallon gidan duk da bata san dalilin zuwan nasu gidan ba Amma ba shakka gida ne ajin farko. Sadeeq kuwa mind d'in shi cike suke da tambayoyi kan abunda ta aikata d'azu a shoprite ,wayeshi Mutumin? Kuma neyasa take tsoronshi haka?
  Gate da kanshi ya bud'e Sadeeq ya sa kai gami da daidaita parking a gaban wasu manyan Egyptian designed pillars wanda tsakiyar su ya kasance marvelous entrance ne k'awatacce da wani astonishing k'ofa brown with touch of Golden roses design,
"damn! That mansion is a killer!"

  Bud'e k'ofa yayi yaja hannun Deenah sukayi ciki wanda tuni ta manta inda take ,everything is Arabian. Maganar sane ta dawo da ita daga duniyar da ta shiga na kalle kalle
"Who is he?".
Ya tambaya yana kallon ta eagerly waiting for her answer.
"Who?"
ta tambayeshi ba tare da ta gane wanda yake magana a kai ba.
"Mutumin da kika gani d'azu? Tsoro! Tsoronshi kikeyi kamar kinga mala'ikan d'aukar rai."
  "Yayana ne"
ta bashi amsa a tak'aice "yayanki?".
Ya tambaya cike da mamaki.
"Eh sunan shi Saeed d'an kawu na Khamees"
"Amma shine kike tsoron shi haka? Deenah no matter what y'an uwanki ne baki da wanda ya wuce su"

   Dakatar dashi Deenah tayi ta hanyar rufe bakin shi da hannunta tace
"Wallahi ina da wanda ya wuce su, wanda duk halin da zan shiga bazai bari in cutu ba kuma bazai cutar dani yadda suka cuce ni ba"
"Waye Wannan?"
Ya tambaya cikin rashin fahimta.
"kai ne! Kai ne Sadeeq! Su suke da hakkin rik'eni amma basu rik'e amanar Marainiya ba, basu tausaya min ba sun dakeni ,sun tauye min hakki ko banida lafiya babu me damuwa ya bani magani,Sadeeq sun wahalar da ni to such an extend that I became fed up this life ,I have no shoulder to cry on."
  Goge hawaye tayi taci gaba da cewa

"Ranar da aka d'aura auren mace bak'in cikin rabuwa da iyaye ni jinayi kamar a Aljannah aka tsunduma ni, y'an uwa suna raka Amarya d'akin mijin ta ni kamar mayya aka Hankad'a ni , Sadeeq na kwana a kitchen tsabar rashin tausayawa irin nasu, abincin da zanci sai an kammalaci zan bi plates ina kale kamar mabaraciya.
   Amma tun ranar da na saka k'afa na cikin gidanka rayuwata ta canja, daga ranar nasan dad'in kwana a d'aki, nasan dad'in abinci har ma sai naga damanci, na sani cewa we have our ups and downs amma wannan zan iya kamanta shi ne da rashin sabo coz its nothing compared to wancan rayuwar They made my life a living hell! At lease a wajenka in na samu ciwo zan samu magani, you give pain and also the medicine this law is not applied with them ,you are the only one I have Sadeeq zan rok'eka karka sake dangantani dasu dan Allah"

  Sadeeq da yanzu kam hawaye yake cike da tausayinta rungumeta yayi yana bata hak'uri domin ta kashe masa Jiki da kalaman ta tabbas Deenah taga zalunci a rayuwa.........

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245