MATATA GIMBIYATA 29-30

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         2⃣9⃣➖3⃣0⃣

  Sadeeya bata tsaya b'ata lokaci ba ta nufi flat d'in Deenah wanda k'ofar yake facing na Mr Imam. Tana bud'e k'ofar Saida na sake baki kamar y'ar k'auye ba k'aramin living room bane ya sha wani silver coloured tiles ga pink posh Italian carpet a tsakiya da kujeru wanda suka saje da kalan tile d'in wato Ash se throw pillows oh gosh tsaya wa bayanin k'ayatuwan wajen ma b'ata lokaci ne dan haka Sadeeya bata tsaya wata wata ba tayi saurin fara goge goge ta tartare komai sannan ta tabbatar babu wani matsala sannan ta fita sai farin ciki take ,kai tsaye ta dawo downstairs bata zame ko ina ba se d'akin ta, inda ta iske Deenah kwance tayi Shiru kamar me bacci tace
"Madam, muje in nuna miki d'akin ki Oga ne ya umarce ni da haka."
  Kamar bata ji me Sadeeya tace ba ,ta share ta Saida Sadeeya ta sake maimaitawa sannan ta bud'e idanuwa cikin nuna b'acin rai tace
"Mts! Wlh duk kin ishe ni da surutu, ni wasu lokutan se inga kamar bakin ku ma had'e yake Ke da ogan naki, dallah Ki sanar da shi ni nan ma yayi min in kuma na takura kine se ki fad'a in san inda dare yayi min."
Mik'e wa Sadeeya tayi ta dafe k'irji  tace
"ni a su wa zan ce kin ishe ni? kina so Oga ya fatattake ni kenan?"
  Dariya sosai ta bawa Deenah, Saida tayi me isarta sannan tace
  "Wannan Ogan naki bai damu da damuwar wasu ba dan kiji ,da ma a wancan buhun kika yi wa laifi jinin shi har tafarfasa zai yi"
  Deenah ta k'are maganar tana dariya Sadeeya ta ce
"babu ruwana Madam, kar su ji mu. Ke ma ba'a kyale Ki ba balle ni ai sedai kiga k'ullin kaya na anyi waje road."

  Deenah kam me take banda dariya harda gwada tafiyar Hajiya hakan yasa suka sake saka dariya juyawan da Deenah zata yi jikin ta ya d'au b'ari haka ma Sadeeya, Deenah ta had'iye miyau wanda da kyar ya wuce mak'ogwaro ta dubi Sadeeya tace
"Yau fa Mun kamu"
  Sadeeya kai a k'asa tace
  "gaskiya kam madam!"
    Make ta Deenah tayi da bayan hannu tace
"ni wallahi wannan madam da kike k'ira na bai dace da ni ba sam da wancan Hajiyar ya dace kawai ki kirani Deenah."
  K'asa k'asa suke magana cike da tsoro.

   Tun da ya iso bakin k'ofar kallon su kawai yake, shi bai san dalilin dariyar su ba su kuma sun yi zaton duk ya ji su. Shi kuwa sam ya zo ne don yayi ta kiran Sadeeya bata d'auka ba kuma. Yana son Aiken ta.
  Yanda suka tsaya suna k'us k'us yasa dariya ta kusa kufce masa amma ya gimtse ya ce

"Baki da kunne ne? Sau nawa zan k'ira amma Saida kika sa na fito?"
   Yana maganar idanuwan sa na kan Deenah da ta had'e rai.
"Kayi hak'uri ban san ka k'ira ba".
  Sadeeya ta bashi amsa kai a k'asa cike da ladabi.
Bunch na kud'i dubu d'ari ya bata yace ta je tayi masa shopping ya had'a mata da list.
  Jiki na b'ari ta karb'a hannu bibbiyu ta d'auki hijabin ta tafice.

   Ya dad'e a wajen yana kallon ta amma tak'i d'ago kai, abun da ya mata kawai take tunawa ji take kamar ta hankad'e shi daga shi har wheelchair d'in
Cikin zuciyar ta tace
"Careful Deenah kar kije garin b'acin rai Ki kashe shi"
  wata guntuwar tsaki tayi
"mts "
   gwara in bar nan wajen ma in fita dan zan fi sakewa amma. Wata zuciyar ta sake cewa
"Ki gode wa Allah bai ji Ki ba d'azun da yanzu kin sha mak'ura a hannun gurgu."

  Gefen shi ta rab'a zata wuce ya kamo hannun ta yana k'are ma ciwon da taji kallo ita kuwa wafce wa tayi ta fice ma daga falon ta nufi inda motocin gidan Ke ajiye ta  zauna, nan tunanin abubuwan da suka faru da ita a rayuwar ta suka fara dawo mata ta gama kukan ta iya son ranta.
    Haka Sadeeya tai ta lallab'a Deenah har ta yarda ta koma flat d'in, ko da ta sa k'afa at first cikin living room d'in wand cikin shi akwai three bedrooms se taji tana mugun son wajen. Sun dad'e suna hira da Sadeeya kafin ta fice, yau dai Deenah bata ji d'uriyar mutanen ta ba wato su Hajiya hakan ya mata daidai, mik'e wa tayi ta k'are ma waje kallo sannan ta shige d'aki bayan ta rufe k'ofa. Deenah bata runtsa ba saida tayi ta kai kukan ta ga mahalicci akan sallaya ma tayi baccin ta....

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245