MATATA GIMBIYATA 65-66

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         6⃣5⃣➖6⃣6⃣

   "Domin farin cikinki na hana kaina farin ciki na d'auki d'an da na mallaka duk duniya na bakishi, kin zo da kuka mijinki ya gaji da zama ba haihuwa, labarai dai iri daban daban masu narkadda zuciya, Abban Sadeeq yasa na bakishi kika nesantani dashi, all those years I stay silent under pain of loosing him, ni da bana tare dashi ban yi kyashi akan abunda ya Tara ba saike wanda babu hidimar ki da bai d'auke ba? Kin cuceni, Ashe haka d'an uwa yake ba alk'awari? Murmushi Sadeeq yayi yace
"Wasu y'an uwan"..
Ya nisa sannan yaci gaba da cewa

"Zan bar gidan nan Mom, domin ganina a cikin shi ma yana sa memories su dinga dawo min ,I want a new life!"

   Daidai shigowar Ramlah kenan tana kuka, da gudu Hajiyar ta rik'e ta tana tambayarta abunda ya faru cikin kuka Ramlah ke bayani
"Wallahi ya cuceni, wai ba Aure na zaiyi ba kuma saida na tabbatar masa ina da juna biyu Umma kamar kare haka ya dinga jana har k'ofa wai kar ya k'ara gani na Wayyo na shiga uku!!"

  Hajiya kam bakin magana ta rasa shi tabbas abinda ta shuka ne take girbewa da tafin hannunta, Lallai Hausawa sunyi gaskiya da suka ce ramin mugunta ka gina shi d'an kad'an dan wataran kai zaka afka tabbas yau taga illar cuta.
  Sadeeq ko inda take baya gani ya mik'e yaja Mom suka fice yarinyar nan ta ja hannun Deenah ,tausayi ya gama mamaye Deenah kuma ta tabbata har yanzu Sadeeq yana son Hajiya kawai baya son su had'a ido tausayi yasa ya yafe mata ne though she deserve what she just got!

  Zubewa Hajiya tayi k'asa kan gwiwowinta tana kuka tana nadamar abunda ta aikata amma fa ku sani bature yace

*ITS TOO LATE TO CRY WHEN THE HEAD IS CUT OFF*"

**********************

  Yau kwanaki biyu kenan da faruwar al'amarin Mom tana tare dasu Deenah saboda halin da ya shiga bata tafi ba so take se ya mance komai.
Aysha ta kasance K'anwar Sadeeq ne mai matuk'ar kama dashi though miskilancinta ya ninka nashi , tun da tazo take mannewa Deenah gata da surutu.
   Deenah sosai take jin dad'in zamansu tare gashi Mom kamar kwai take tarairayarta Deenah cikin kwana biyu tayi realizing how lucky she was to be amidst such wonderful family.
   Mom na zaune a falo tana waya Sadeeq ya dawo daga aiki ,wurgi yayi da jakarshi sannan ya kwanta kan cinyar ta.

"A'a haba baby d'agani yanzu wannan ai ba aiki na bane kana son kwanciya ga can matar ka nikam ai sedai ka ruguza ni da wannan shekarun nawa"
Aysha da Deenah dake kitchen suka kwashe da dariya hakan yasa ya mik'e ya nufi kitchen ya tsaya bakin k'ofa ya nad'e hannunshi ya jingina da k'ofa
" sannu da zuwa Bro!"
Aysha ta fad'a tana slicing tomatoes.
  Ido ya mata alamar ta fita ita kuwa tab'e baki tayi tace
"Mutum yana aikin shi za'a Kore shi ai sai kayi"
yaji me tace hakan yasa ya ja kunnenta yayinda ta saki k'ara tana kiran Mom sam hankalinsa baya kan Aysha kallon Deenah yake yana Murmushi
"cire mata kunnen kuma"
maganar da Deenah ta fad'a kenan hakan yasa ya saki kunnen Aisha ,cikin takun isa ya k'arasa kitchen d'in yana Murmushi ita kuwa tana ta had'a pizza dough.

  Zagayawa yayi ta bayanta ,da hannuwan shi ya rik'e kunkumin ta gami da d'aura kanshi a kafad'arta daidai kunnen ta yace
"Anything special?"
Bata kula shiba dan haka ya matse ta a jikin shi har saida ta saki y'ar k'ara tace
"Haba baby zaka murk'usa niiiiiii"
Sake ta yayi yana dariya ya d'ale kan table da take aikin kafin yace
"Oh! Kema babyn zaki ce ? Kin ganni da feeding bottle ne?"
Ya kammala maganar yana gutsuran carrot da ya d'auka cikin grocery bag ita kuwa ta shafa masa flour dake hannun ta a fuska tace 
"tashi ka tafi"
ko kulata bai yi ba ya sauka daga table d'in ya fara slicing tomatoes d'in da Aysha ta bari
  "Ammm daman inaso in rok'eka wata alfarma"
Deenah ta fad'a kanta a k'asa wuk'ar hannunshi ya aje yace
"Anything for you my dear except for batun Hajiya and Ramlah in shi zaki sake min magana a kai na yafe ban so hold it to yourself i have made it clear to you already yanzu babu wata danganta tsakani na da ita"
"Toh amma Hajiya tayi nad.... "
bata iya ta k'arasa ba saboda yadda yayi watsi da kayan dake kan table d'in ya juya ya fice bai ma san ya ji wa Deenah ciwo ba.
  Yakai bakin k'ofa yaji ta kurma ihu ba shiri ya dawo a firgice ya rik'e hannun ta gaba d'aya ya rikice haka Mom da Aysha suka shigo, wafce hannun ta Deenah tayi suka fice da Aysha ta taya ta treating mata ciwon wanda da kyar jinin ya tsaya.
"Learn to control your anger"
iya abunda Mom tace kenan ta fice rai a b'ace shi kuwa gaba d'aya ya rasa abunda yake masa dad'i ya fice zuwa d'akin Deenah.

   Kallon kanta take a  madubi ta tsaya kamar photo haka har ya shigo bata sani ba. Hugging nata yayi ta baya yana kallon fuskar ta tana hawaye a hankali yace
"Am very sorry ,pls forgive me My princess."

  Kwace jikinta tayi ta wuce bathroom ,Furzar da numfashi yayi yabi bayan ta yana fad'in
"come on gimbiya I said am sorry, Ok fine in dai maganar Hajiya ne na yafe mata pls ki min magana."
   Zaro idanuwa tayi da mamaki tace
"da gaske?"
Kai ya gyada mata
yace
"with all my heart"

Tsalle tayi gami da hugging nashi ,k'asa k'asa yace
" Toh ni kuma zan iya Rok'on ki alfarma?"
kai ta gyada tana Murmushi hancinta yaja yace
  "Ki daina takarar inda nake when am angry pls anything can happen"
Murmushi ta sakeyi ba tare da tace komai ba. Juyawa tayi zata shiga bathroom ya chafke hannunta kai tsaye ta juyo tana kallon shi.
"Am I invited?"
Ya tambaya gira a d'age. Zare idanuwa tayi  ta kama kunkumi cikin d'aga murya tace
"NO WAY!!!"

  K'ank'ameta yayi da k'arfin tsiya cikin d'aga murya kamar yadda tayi  yace
"YES WAY!!!!"
Suka sa dariya dukan su kafin ya ja hannun ta suka shiga........

☁☁☁☁☁☁

   "Tabbas Mun tafka babban kuskure wannan laifin da muka aikata in bamu nemi gafarar Deenah ba ko Allah bazai yafe mana ba we hurt that girl to the extend that ta gaji da rayuwarta ban rik'e amanar d'an uwa na Ismael ba na cutar da Marainiya shiyasa har yau ban ga da kyau ba dole ka kaini wajen Deenah in nemi gafarar ta banaso in mutu da hakkin kowa musamman na Deenah Saeed ka kaini in  nemi gafarar ta............"

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245