MATATA GIMBIYATA 49-50

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         4⃣9⃣➖5⃣0⃣

    Da Murmushi ta fito tana y'ar wak'arta daga ita sai dogon wando na jeans da vest ash mai kyau bata ma lura da cewa akwai mutum a gaban ta ba sai da ta iso dab da shi ta hangame baki ganin irin halin da yake ciki hankali a tashe ga uban gumi kuma kuka kawai yake tayi.
   Iya rayuwar Deenah bata tab'a ganin cikakken namiji iri Mr Imam yana kuka kamar ran shi zai fita ba.
   Jiki a sanyaye ta durk'ushe gaban shi
tace
"Miysa kake kuka? Miya faru da kai"
  asalin damuwa Deenah ta kai k'ololuwa taga kukan nashi ba na k'arewa bane dan haka ta tura shi zuwa falon ta sannan ta rufe k'ofa suka k'arasa ciki itama taja kujera ta zauna tana aikin bashi hak'uri amma kamar ingiza shi take yi ganin haka yasa ta mik'e gami da rungume shi tana hawaye kan shi a cikinta
tace
"Ni ban sani ba ko me yake damun ka, amma nasan cewa ba k'aramin tashin hankali kake ciki ba, dan Allah ka daure kayi min bayani ko akwai hanyar da zan iya taimaka maka pls."
   Sadeeq bai ce komai ba amma ko ba komai wannan rungumar ta Deenah ta sassauta mishi wani ciwon , zame jikin shi yayi yana goge hawayen shi
yace
"La'asar yayi bari nayi sallah"
yana kai nan ya juya ya bar falon zuwa flat nashi.

    Tun da ya nufi d'akin shi ya fad'a bathroom dan yin alwala amma ya kasa yi sai hawaye
Deenah kuwa kasa zama tayi gaba d'aya tausayin yadda ya koma karo d'aya takeyi babu abunda bata sak'a a ranta ba amma ta kasa gane dalilin wannan tashin hankali da yake ciki dan haka ta bi shi har d'aki amma ta iske d'akin a rufe, tayi ta bugawa amma sam yak'i bud'e wa haka ta hak'ura ta je tayi sallah, nan ma ta dawo bai bud'e ba.
   Har k'arfe tara na dare Sadeeq bai fito ba yana can cikin tsananin takaici.
Kitchen ta nufa ta zubo masa abinci nan ma bai bud'e ba dan haka ta koma downstairs ta zauna cikin kujera tayi jugum tana tunanin wacce irin matsala Ke damun Sadeeq.

    Duba wa yayi bai ga wayar sa ba can ya tuna cewa wayan yana falo, Sadeeya ya kira murya dishi dishi yace
"ta kaishi downstairs"
  babu b'ata lokaci ta kai shi sannan ya umarce ta da ta koma zai nemeta if the need arises.

   Har ya d'auki wayar yaji sheshek'ar kuka dan haka ya d'aga kai ya kalli inda yaji kukan ,nan ya hango ta har ta ma bashi tausayi.
  Ita kuwa ta hango Sadeeya dan haka ta kira ta, Sadeeq yana daga bayan su yaji tace 
"Shin bakya tausaya wa rayuwar ogan ki? "
  Sadeeya ta kallo shi yayi mata alama kar ta nuna yana nan dan haka Sadeeya
tace
"Tabbas! Amma me yasa kika ce haka?"
Murmushi Deenah tayi tace
"Gani nayi iya rayuwar shi wad'anda ya yarda dasu sune suke watsa mishi k'asa a ido ,first it was his first wife Zeenat, daga labarin ta da kika bani na fahimci cewa mayaudariya ce kuma butulu, yanzu kuma bashi da wasu mak'iya irin Hajiya da Ramlah, ba dan Allah suke zaune da shi ba, banda Hajiya ma mai ya rageta dashi? Bai son b'acin ranta , ba'a tanka mata sannan yana daidai da ya bata rayuwar shi in ta buk'ata ni fa ko wannan na samu nagode Allah. Ni ina ga su Hajiya sune dalilin shigar shi halin da ya shiga yau domin na sha jin hirar su shiyasa sam basu da k'ima a ido na amma sai dai ina tsoron fad'a masa saboda nasan baya k'aunar b'acin ran Hajiya amma in da rai watarana zai ji da kan shi, amma na d'auki alk'awarin koma me zai faru ya faru amma bazan tab'a bari a cutar min da miji bako da zan rasa rai na"

    Wasu zafafan hawaye ke sintiri a fuskar Sadeeq Lallai wannan shine ake cewa
*an yi walk'iya kowa yaga kowa*

Ko ba komai Sadeeq ya san wanda zai yi trusting yasan wanda zai yi kaffa kaffa da shi .............

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245