MATATA GIMBIYATA 31-32

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         3⃣1⃣➖3⃣2⃣

     Hasken rana ne ya hasko d'akin hakan yasa ta farka tana salati, gudu ta antaya bayi tayi alwala sannan ta dawo ta yi sallah, gaba d'aya ta rasa yanda akayi ta makara. Bayan ta idar ne ta yi wanka ta bud'e wardrobe.
"Oh my gosh"
   ta fad'a tana kallon sink'in kayan da Ke a ciki. Ta sake baki kawai tana kallo, komai na ciki sabo ne kama daga kan Abaya, dupatta, atamfa laces da materials, kuma gasu a d'inke, har ta kai hannu kan wata jar atamfa mai kyaun gaske se ta tuna abun da Ramlah tayi mata, nan da nan ta rufe wardrobe d'in ta zira hijabin ta a kan towel d'in dake jikin ta, ficewa tayi daga d'akin tayi downstairs amma bata yi sa'a ba ,iyalan jarabar na falo tun kafin ta sauk'o suka kafe ta da ido, Ramlah ta tab'e baki tace
"ji munafuka, ta shararo hijabi kai kace matar malam"
   Deenah da tuni ta sha ruwan jikin ta tana iso wa ta rusuna sannan ta gaida Hajiya.
Tsaki Hajiya ta ja gami da kawar da kai tace
"Ke yanzu wato tsabar samun waje an tsamo Ki daga talauci kin shigo daula shine se yanzu zaki fito Ki d'aura wa mutane break fast ko? Mara mutunci."
   "Har ni zaku nuna wa dukiya ku da rab'ar dukiyar kuke yi ni kuwa a cikin ta aka haifo ni, ba dan K'addara ba har zaku ganni a nan ne balle ku samu abin zagi"
duk cikin ranta take maganar kamar ta shak'e Hajiya.
  "Tunanin Uban mi kike yi kod'add'iya?"
Hajiya ke fad'an haka, kai Deenah ta gyada ta mik'e tsaye cikin nuna isa tace       
"ni bazan iya d'aura abinci yanzu ba gaskiya dan ciwon ciki Ke damu Nah ai Sadeeya tana nan me zai hana tayi?"
   Gaba d'aya suka sake baki dalala suna kallon ta, Ramlah ta mik'e gami da d'aga hannu zata kai mari Deenah ta rik'e hannun tace
"wlh Allah kin yi kad'an bazai yiwu in bari ana cin kashi a kai na ba."
Mik'ewa Hajiya tayi baki sake ta zuba wa Deenah mari hakan yasa Deenah ta kama kuncin ta ba shiri cikin b'acin rai ta d'aga hannu zata rama.

"DEENAH"
"DON'T YOU DARE"
abinda ya iya fad'i kenan jikin shi har rawa yake yi idanuwan sa kuwa sun yi jajir da su.
  Tabbas ba k'aramin tsorata Deenah tayi ba dan ji tayi kamar ta saki fitsari Sadeeya da tun da aka fara rigimar take tsaye ita ma kasa ko motsi tayi.
Idanuwan Deenah cikin nashi tana kallon yadda yake tafarfasa bai wata wata ba ya turo keken shi zuwa gaban ta ya tsaya ai kuwa kafin ya bud'e baki yace k'ala, Deenah ta ranci ta kare shi kuwa hakan ba k'aramin k'ular shi yayi ba.

      "Ai ga irin ta nan Duk laifinane da na zo gidan ka na zauna, ni nayi zaton har yanzu ni uwa ce a gare ka Ashe akwai wanda har zata iya taka ni ta wuce kana kallo, kawai ma zai fiye min in kwashi kaya na in bar mata gidanta"
duk maganganun da take cikin kukan munafurci take yin su ita kuwa Ramlah se share mata hawaye take tana bata baki. Ran Mr Imam ba k'aramin b'aci yayi ba har muryar shi na rawa ya fara bata hak'uri

   "No Hajiya pls kar kice haka, wlhy you are the most important person in my life, Ke kike da guri a cikin gida na domin duk wannan daular bazan sameta ba in baki Raine ni har nasan kaina ba, Ki kwantar da hankalin Ki babu inda zaki je sedai ita ta fice ta bar min gida."

   Har ya juya zai nufi upstairs Ramlah munafuka harda kama keken zata tura shi Hajiya tay tunani tace.
"Ai bazan so Deenah ta bar gidan nan cikin ruwan sanyi ba dole se ta gane kuranta"
cikin ranta tayi maganar gami da sakin shu'umin Murmushi ta antayo da gudu ta rik'e wheelchair d'in tana Rok'on shi
"A'a son! Kada zuciya ta saka ka yanke d'anyen hukunci pls, Deenah is such a nice gal kawai de watak'il bata fahimce ni bane ,kada ka mata komai ni kam na yafe"
   Ganin kalaman ta sun yi tasiri gare shi yasa ta mik'e dan munafurci wai take tambayar me zai ci.
"Bana jin yunwa"
ya bata amsa a tak'aice sannan ya ce Ramlah ta kai shi d'aki........

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245