MATATA GIMBIYATA 39-40

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         3⃣9⃣➖4⃣0⃣

    Zaune yake as usual kan wheelchair yana k'ok'arin had'a tea yayinda saman table d'in Ke cike da food, flasks iri iri Sadeeya zata fara aikin serving nasu.
  Salamar Deenah ta sa duk suka mai da duban su ga inda suka ji Salamar amma me? Kowa sakar baki yayi dalala musamman Sadeeq da ya kasa k'arisa amsa Salamar ya d'auko kallo tun daga k'afafun ta har k'ugun ta sannan ya cigaba zuwa k'irjin ta kafin idanuwan su suka yi arba da juna.
  "Assalamu Alaikum"
  Ta sake maimaita wa nan ma da kyar ya iya amsa wa Hajiya da Ramlah ganin hankalin shi ya dugunzuma duk haushi ya kama su sai ji suke kamar su shak'e Deenah.
  Ita kuwa cikin salon shak'iyanci ta durk'ushe har k'asa ta kwashi gaisuwa tana musu wani shu'umin kallo.
  Hankalin Sadeeq bai gama tashi ba sai lokacin da ta iso gaban shi ta karb'i tea spoon d'in ta had'a masa tea sannan tayi serving nashi, Sadeeq abubuwan suka mishi yawa ,ga k'amshi ga kyau ga kuma dukiyar Fulani half opened kwata kwata ya ma manta inda yake yana k'ok'arin janyo Deenah jikin shi kamar a mafarki yaji Hajiya tana tari da sauri Deenah ta zuba ruwa a glass mug ta mik'a mata gami da kashe mata ido d'aya tace
"Wayyo sannu Hajiya! Ki ci abincin a hankali kin san fa pepper soup akwai shi da borkono ga ruwa ki kora ko zaki ji dama dama"
  Hararar ta Hajiya tayi sannan ta karb'a ruwan ta kurb'a can k'asa k'asa Deenah tace
"ki yi a hankali ni kai na borkono ce sai da ruwa".
  Hajiya bata san lokacin da ta jefar da glass d'in ya fashe Tush ! Cike da damuwa Sadeeq ya zagayo inda take Amma kafin ya ce komai Deenah ta cafko hannun Hajiya ta yi fuskar damuwa tace
"Subhanallah ! Hajiya I hope baki yi rauni ba? Ke Sadeeya zo ki kwashe wad'annan fasassun glass d'in barin kai Hajiya d'aki kamar tana buk'atar Hutu ne"
   Cike da bak'in ciki Hajiya ta dakatar da Deenah ta hanyar sakar mata murmushin dole tace
"Aa bana buk'ata ki zauna kawai ki ci abinci I'll manage" 
d'aga mata gira Deenah tayi gami da tab'e baki tana murd'a jelar gashin ta tace
"OK since you insist, bari na karya don dama yunwa nake ji matuk'a"
Ta fad'i hakan ne tana shafa cikin ta wanda yake shafaffe. Hajiya ta haye upstairs tana huci ,juyawan da Deenah zata yi Ramlah ta buga table gami da wurgar da spoon d'in hannun ta ta fice fuuuuu kai kace tashi sama zata yi.

  Sadeeq kuwa shi da Sadeeya tuni sun dad'e da zama y'an kallo dan har ya manta bakin shi yana neman saka cokali a hanci ita kuwa Deenah ko a jikin  ta abinci ta zuba ta fara harbawa ciki tana yi tana danna wayar ta tana Murmushi Sadeeq duk iya k'ok'arin da zai yi su had'a ido ya kasa don ta k'i ta dubi inda yake ma .
Bayan sun kammala cin abinci ta taya Sadeeya kwashe kwanuka suka kai kitchen.
  Duk inda ta bi shi ma bin ta yake da kallo har ta kammala ta dawo falo ta ja balance k'afa d'aya kan d'aya  tana game.

  Ganin bata da niyyar kula shi da gangan ya matso da wheelchair d'in kusa da ita yace,
"Wuya na yayi min tsami ko zaki taimaka  ki min massage?" 
   Matsawa tayi kusa da Kunnen shi cikin shu'umanci tace
"as you wish"
    Nan ta fara masa tausa cikin kwarewa shi kuwa har wani lumshe idanu yake ya ma manta inda yake.

  Ita kuwa Deenah ta sake zagewa musamman da ta hango Ramlah a saman bene tana kallon su cike da jin haushi da bak'in ciki hakan yasa Ramlah ta juya da gudu ta bar wajen ta koma d'aki ita kuwa Deenah buk'atar ta ta biya dan haka ta langab'ar da kai cikin sanyin murya tace
"ni na gaji wlh bacci nake ji."
  Murya k'asa k'asa yace
"nima baccin nake ji pls take me to my room"
  kai kawai ta jinjina tace "OK"
nan ta d'aukar masa wayar shi sannan ta tura shi suka yi d'aki.

   A hankali ta bud'e k'ofar d'akin ta tura shi sannan ta taimaka mishi ya hau gado ya kwanta ta ajiye masa wayar shi kan bedside drawer ta juya zata fita.

  Hannun ta ya chafko yace
"stay with me pls"
Murmushi kawai tayi tace
"bacci nake ji nima"
haka ta bashi amsa a tak'aice, fisgota yayi ta fad'o jikin shi rigijib sannan ya cije leb'en shi yace
"Sleep with me my PRINCESS"
k'ok'arin tashi tayi Amma ta kasa dan yadda ya matse ta a jikin shi dan haka ta hak'ura tayi k'ok'arin gyara kwanciyar ta sannan ta rage jewelries nata ta ajiye su gefenta.
  Sadeeq kuwa matse ta ya sake yi a jikin shi.
Cikin zuciyar ta tace
"Wannan ina ga sai ya murk'usa ni zai huta."

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245