MATATA GIMBIYATA 43-44

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         4⃣3⃣➖4⃣4⃣

     "Bilal ina ganin lokaci yayi da k'irk'irarren labarin cewa Abubakar Imam gurgu ne ya zama tarihi, ina ganin yanzu kam na samu abun da nake nema."
  Dr Bilal ya yi Murmushi yace
"da alama hak'ar ka ta cimma ruwa kenan?"
Kai Sadeeq ya jinjina yana mai k'urban lemo.

   Mahmoud da Ke gefe a tsaye yace
"ni daman na dad'e ina cikin duhu ban san dalilin da yasa Sadeeq yayi k'aryar cewa ya samu hatsari ya zama haka ba. So tunda yanzu wasan rainin hankalin naku ya k'are ai sai a fad'a min dalili"

     Mr imam bai ko tanka ba Dr Bilal ne ya fara bawa Mahmoud labari.

*Flashback*

     "Zaune yake kan kujera yana duba newspaper k'afa d'aya kan d'aya, duk da yana duba jaridar amma kunnuwan sa suna sauraron kalaman Bilal"

     "Abokina ni fa tsoron mata nake yi, zuciya iri biyu suke da shi d'aya a kwakwalwa take d'aya a k'irji sukan so mutum kamar ba gobe amma fa se wani abu ya faru da kai zaka gane cewa ba dan Allah suke k'aunar ka ba."
Sadeeq yayi Murmushi yace
"wasu matan ba? Ni dai kam Zee d'ina ba haka take ba, she loves me dearly and so do I".
Kai Bilal ya girgiza
yace
"I can see soyayya ta rufe maka ido, kamata yayi ka bud'e idanuwan ka ka fuskanci duniya. Nasan cewa kana k'aunar Zeenat amma fa da yau za'a ce wani abu ya same ka na gazawa, bana fatan hakan wallahi Zeenat bazata zauna ba"
Tab'e baki Mr Imam yayi yace
"Zeenat bazata tab'a yi min haka ba, don tsakani da Allah take so na"

   Bilal ya gyara zama yace
"Toh in ka yarda mu buga wani wasa , ni zan zamo alk'alin wasan"
  Sadeeq ya d'ago
yace 
"wanne irin wasa kuma?"

Gyara zama Bilal yayi yace
"plan zamu had'a, zamu ce kayi accident kuma spine naka ya samu matsala "
Mik'e wa Sadeeq yayi cike da b'acin rai
yace
"No bazan iya ba, Wannan ai ba wasa bane"

  Bilal ya yi Murmushi yace
"Ashe baka yarda da zee d'in ka ba ko?"
Jinkiri Sadeeq yayi  na wasu lokuta sannan yace
"fine! Zan yi amma ka sani in Zeenat tayi proving d'in ka wrong bazan sake yarda da zancen ka ba wawa kawai kai duk tunanin ka na rashin hankali ne".

*bayan kwanaki biyu*

       Zaune take kan kujera ta sha doguwar riga bak'a wanda ta sha kwalliya da stones looking beautiful tana waya sai dariya take , kyau kam Zeenat ta kere Deenah.
   D'ayar wayan ta ne yayi k'ara hakan yasa ta ajiye wancan wayar ta d'aga d'ayan.
"Innalillahi! Wanne asibitin wai? OK Toh gani nan zuwa"
ta kashe wayar  ta zari key d'in mota ta nufi asibiti.......

"Bilal dan Allah ka fad'a min me ya same shi? Yanzu wanne hali yake ciki? "
  Bilal ya girgiza kai
yace
"ki biyo ni zuwa office akwai abunda zamu tattauna."
  Cikin tashin hankali Zeenat ta bi bayan Bilal har office nashi ya bata waje ta zauna sannan yace
"Se dai kiyi hak'uri fa".
Tashin farko Zeenat ta dafe k'irji tace
"ya mutu ne Sadeeq d'in?".
Wani shu'umin Murmushi Bilal yayi yace
"kina so ya mutu  ne ?" Sosa kai ta fara tana fad'in
"A'a kawai na shiga rud'ani ne".

  Kai Dr Bilal ya girgiza yace
"kwantar da hankalin ki yana da rai sai dai ya samu matsala a spine nashi am afraid mijin ki bazai dawo kamar da ba, yanzu zama ma sai da support tsayuwa kuma daman babu zancen shi."

"What?!!"
Ta mik'e gami da dafa k'irji tace
"dank'ari! "
  tana kai nan ta fice daga office d'in bata ce komai ba. Bilal kuwa Murmushi yayi gami da girgiza kai yace
"Mata kenan!".............

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245