MATATA GIMBIYATA 63-64

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         6⃣3⃣➖6⃣4⃣

  Hannunta yaja suka haura wani spiral staircase har wani had'add'en flat wanda da kallo d'aya ya sace zuciyar Deenah.
"Cry no more GIMBIYA ta!  I promise never to hurt your feeling even for a second"
D'agowa tayi tana kallon cikin idanun shi tace
"Nan ina ne?"

  "Gidanki ne"
yabata amsa yana murmushin sannan ya sake ta yace
"barin deb'o kaya a mota, ki shiga kiyi freshening up nasan kin gaji take some rest ni zanje in taho miki da Sadeeya"
Ita dai bata fahimtaba, meye laifin wancan gidan? Amma fa wannan ya d'auke mata hankali sai dai yana fita tsoro ya kama ta da gudu ta bi bayan shi har ya kunna mota ta bud'e tayi zamanta a gaba, Murmushi yayi kawai ya fara tuk'a motar, bai d'aukeshi lokaciba ya isa gida, tare suka shigo su Hajiya anyi bak'e bak'e kan seater gani su tare yasa gabanta fad'uwa musamman yanda hannunsu ke sark'e cikin na juna.
  Farin ciki ne ya lullub'e Sadeeya ganin Madame d'inta tadawo da sauri ta kawo mata ruwa tana musu iso , Deenah tayi hugging nata tace
"Ya kike?"
Lafiya nake Madame musamman ma da naga kin dawo

"Sadeeya jeki deb'o duk abubuwan da zaki buk'ata zamu koma sabon gida ne pls be fast"
Cewar Sadeeq yana k'ok'arin wuce wa upstairs.
"A'a Abubakar! Har zamu koma sabon gidan shine ko sanar damu baka yi mu fara shirye shirye ba?"
Hajiyace ke magana tana washe hak'ora
Da shu'umin Murmushi ya juyo shimfid'e a fuskar sa ya dubi Hajiya kafin yace
"Nida suwa zan koma sabon gidan? Da ku? Wait a second! Akwai wanda muka Tara kud'in yin ginin gidan dashi a cikin ku? Ko kuma gadon gidan kuke da? Ai daga ni se MATATA da Sadeeya"
   yana kai nan ya juya kai gefe

    Hajiya bata san lokacin data mik'e ba Jiki ba kwari tace
"Abubakar? Kaine kuwa?"
K'arasowa tayi ta tab'a shi taga dai shi d'in ne .

  "Get your hands off me! Dubi yadda kike abu kamar baki san komai ba, na d'aukeki tamkar uwa, na darajaki ko da wasa jini na tafarfasa yake in antab'a ki amma karo d'aya saboda kyashi da son abun duniya ni Abubakar Sadeeq Imam kike son gani a k'asa, nine kike so na mutu dan ki mallaki abunda na mallaka! Hajiya da ace kin tambaye ni har raina in kin buk'ata zan baki menene na yin zagon k'asa? Da kunne na naji komai kin b'ata Ramlah kin mayar da ita mai irin tunaninki kaico walah nayi danasani dana girma a hannun mace irin ki wanda zata bak'anta ran d'a domin abun duniya. Kin gama dani baki samu biyan buk'ata ba sai kika juya kan Deenah baiwar Allah bataci ba bata sha ba kika d'aura mata laifin sata , K'azafi after all ke kika yi Satan. Toh yanzu reshe ya juye da mujiya ya kuma zakiyi?"
"Haba d'ana dan Allah ka yafeni wallahi sharrin shed'an ne dan Allah ka yafe ni ba da niyya nayi ba"
Hajiya kenan da tuni ta zube k'asa a k'afar shi , Cikin sanyin murya da kawar da kai yace
"I am not your son and will never be! Sai kun aikata laifi sai kuce sharrin shed'an, kafin na chanja mind d'ina nayi worst than this Hajiya ga driver can yana jira zai mayar da ku can damaturu amma ni to be frank bana k'aunar sake ganin ki domin ko a labari ban tab'a jin uwa tayi abinda kika aikata min ba, you hurt me Hajiya"

"Nikam bazan koma wahalaba da kai zan zauna kayi min aikin gafara Sadeeq me zan ce da y'ar uwata?"
Sadeeq bai ko kulata ba ya haura sama nan ta dinga Rok'on Deenah tana kuka duk Deenah sai taji tausayinta Amma tsoron yanayin Sadeeq take yi ita ma dan ido rufe yake magana har yana cije wa dan haka tace
"Kiyi hak'uri Hajiya gaskiya yanzu bazan iya sa baki a maganar nan ba domin Sadeeq ya fusata amma kiyi abinda yace ni zanyi iya k'ok'ari na inga nayi masa magana later on"....

      Tsaye yake a cikin d'aki ya zubawa hotuna uku ido.
"Dukkaninku abu d'aya ne, halin yaudarar ku d'aya ne I don't need you! I don't ever want to see you again! Abun haushin shine duk kun had'a jini da ni"
irin maganganun dake fita daga bakin Sadeeq kenan da ya tsaya yana kallon hotunan Hajiya, Ramlah da Zee inda daga bisani ya doka hotunan d'aya bayan d'aya duk suka farfashe d'iba yayi ya wurga su kan gado gami da banka musu wuta yana tsaye babu abunda yake sai zufa  har suka cinye wutan Yakama blanket da bed sheet Sadeeq yana durk'ushe inda yake yana zufa idanuwan shi tsaye kan gadon suke kallo
"Get out of my life ! Forever! You all are cheats duk halin ku d'aya ne!"
Ya fad'a da k'arfi.

   K'auri Deenah ta jiyo hakan yasa ta haura a guje domin duba abunda yake faruwa.
  Daskarewa tayi ganin yadda wuta ke cin gadon ba k'akk'autawa , da gudu ta d'auki pillow tana bubbuge wutan sam baya mutuwa, bathroom ta shiga ta deb'o ruwa gami da kwara shi kan gadon ta jefar da bucket d'in da gudu ta durk'usa gaban shi tana kallon yadda yake gumi
"Me yasa kika kashe wutan? Da kin barsu sun k'onesu fita daga rayuwata bana buk'atar Wannan rayuwar ko tunanin su bana sonyi. Kawai dalilin dukiya uwa ke neman ran d'an ta, mace ke gudun mijinta dalilin kasa wa da yayi wai a ina kika taba jin haka?"
  Ita dai Deenah iya hak'uri da rarrashi babu wanda batayi ba da kyar tasa ya mik'e ta d'auki briefcase na documents nashi suka fita daga d'akin Sadeeya kuwa har ta janyo akwatinta , ita murna take asirin Hajiya ya tonu.
  K'ofa direct suka nufa Hajiya kuwa duk ta fita hayyacin ta tana bin shi tana magiya.
Bud'e k'ofa da yayine yasa suka yi turus daga shi har Sadeeya Deenah kuwa kallon su kawai take yi.

Cikin sark'akk'iyar murya wanda duk ta dishe yace
"MOM?"
Zaro idanuwa Deenah tayi sai lokacin taga kamannin sak Sadeeq.
"Ya ilahi! Meye haka? Look at you! Baka da lafiya ne ? Ka dubi yadda kayi wujiga wujiga baby"

    Kukane yaci k'arfin Sadeeq yayi hugging Mom yace "
They all are cheats ba soyayyar tsakani da Allah suke min ba, A mother can never choose wealth over her son"
  Kai Mom ta girgiza ba tare data fahimceshi ba ta jashi suka shiga ciki, wata yarinya da zata kai Kimanin shekaru sha takwasce ta kama hannun Deenah suka koma cikin falon domin Mom ta buk'aci kowa ya zauna kuma ta tambaye shi abunda yake faruwa, Sadeeq ko harafi bai rage ba duk ya labarta mata komai.
Hankalin Mom ya mugun tashi ba kad'an ba , ta cika da mamakin irin butulcin da Hajiya ta tafka ,Lallai d'an Adam butulu ne!!............

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245