MATATA GIMBIYATA 33-34

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         3⃣3⃣➖3⃣4⃣

Assalamu Alaikum my beautiful people, inaso inyi amfani da wannan damar na k'ara mik'a maku godia ta akan karamcin da kukaman text, kira na amsa ba adadi har da wanda ma sukazo tun daga wani gari dan ku tayani rashin Maama danayi nagode sosai Allah ya saka da alkairi yabar zumunci, wanda basu samu damar kira ba ko text kuma na gode maku saboda adua duk inda akayita tana zuwa banda bakin da zan gode maku sai dai kusani wallahi yar_ficika na k'aunarku kuma tana alfahari daku a duk inda kuke nagode! nagode!! nagode!!! #1love♥

      Tun da Deenah ta shige d'aki bata ko lek'a k'ofa ba tana kan gado ta had'e kai da gwiwa ko kayan ma bata sa ba.
  Shi kuwa Ramlah na kai shi, tun daga bakin k'ofa ya dakatar da ita nan ta juya ta koma k'asa wajen Hajiya.
Yana shiga d'aki ya mik'e ya fad'a bayi ya fesa wankan shi sannan ya fito, bak'ar shirt ya d'auko daga wardrobe ya saka da blue Armani jeans ya feshe jikin shi da turare sannan ya d'auki wayar shi ya fice yana gyara agogon hannun sa. Sam in ka ganshi bazaka yi zaton shine yake yawo a wheelchair ba. Fice wa yayi already motar sa tana ajiye inda ba kowa ne ma zai san ya fita ba, mai gadi bai b'ata lokaci ba ya bud'e masa k'ofa ya fice kamar zai tashi sama da motar, bai zame ko ina ba sai wani babban company  S&M constructions ya ratsa ta gate ya nufi parking lot yayi parking sannan ya fito yana k'arema wajen kallo.

   Tun da Sadeeq ya tsaya da mota abokin shi wanda tun ranar da aka kawo Deenah wato Mahmoud ya Ke kallon shi. Sedai tun da Mr Imam ya ce ya fita ya bashi waje ranshi ya b'aci dan haka yanzu ma juyawa yayi kamar bai ganshi ba. Mr Imam na wuce wa ma'aikatan wajen sai kwasar gaisuwa suke yi ko kula su bai yi ba cikin sauri ya shige elevator ta haura da shi hawa na uku bai zame ba sai da ya iso wata k'ofa wanda jikinta an rubuta CEO jikin wani golden plate, k'ofar tana amfani da thumbprints dan haka yana sa hannu Na'ura ta tantance yatsun sa sannan ta bud'e.
 
   Come see how Feedoh dey open mouth haaaa y'ar k'auye taga office kamar a white house. Kai kawai ya kutsa ciki ya dafe kujerar zaman sa yana kallon takardun dake kan table d'in Amma komai juya masa yake zuwa fuskar Deenah. Abun da ta aikata wa Hajiya d'azun shi ya sake dawo wa nan da nan ya birkice idanuwan sa suka kad'a ya sa hannu ya buge wasu files suka zube daidai lokacin Mahmoud
yace
"Sai Yaushe zaka daina k'unsa wa kanka bak'in ciki? In ita ma bata yi maka ba sai ka daina b'ata mata lokaci ka sauwwak'e mata kawai"
    Mr Imam da bai san da shigowar Mahmud ba ya d'ago idanuwan shi da suka yi jajir ya dubi Mahmud yace
"I love her Mahmoud! I damn Love Deenah!! Why can't you understand? She has made a mistake! A huge mistake to think of d'aga hannu tayi yunk'urin Marin Hajiya"
    Murmushi Mahmoud yayi ya k'ariso ya dafe table d'in suka yi facing juna sannan yace.
"Sadeeq kafin ta d'aga hannu zata mari Hajiya shin kana wajen? Ka san mai ta aikata mata? Deenah na san ta da ladabi bata da y'ancin kanta ma balle ta samu sake, kuma tana da girmama na gaba dan haka dole akwai wani al'amari boyayye kada ka yanke hukuncin da zai cutar da zuciyar ka kawai ka sa ta bawa Hajiya Hak'uri komai ya wuce dan masu iya magana sun ce *Idan tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba, Toh jaki fa bazai ji kunyar sambad'a shi k'asa ba*"

   A fusace Mr Imam ya d'ago yace
"me kake nufi eh? Kana nufin Hajiya ce tsoho Deenah jaki zata kada Hajiya? Ko kuwa Deenah ce tsohon Hajiya jaki zata doka Deenah da k'asa?"

      Wata muguwar dariya ce ta kufce wa Mahmud shi kuwa Sadeeq yayi tsaye yana kallon ikon Allah, ganin Mahmud bashi da shirin daina dariya Mr Imam ya bi shi da gudu hakan yasa ya fice gami da rufe k'ofar
Sosai Sadeeq yayi dariya ya koma zai zauna Mahmoud ya lek'o yace
"ban san cewa gurgu ya iya gudu haka ba"

  Wani Award Sadeeq ya d'auka ya wurga wa Mahmud luckily ya chafke sannan ya dawo cikin office d'in ya dubi Mr Imam dake danna waya yace
"just think about it, ka sa ta bawa Hajiya hak'uri hakan zai fi maka"
  Ko d'agowa Sadeeq bai yi ba, sai Murmushi da yayi kawai..........
   

*4:00pm*
    Daidai wannan lokacin ya shigo gida. Kuma ta inda ya saba ya shige gida, bayan yayi wanka ya zira 3quater jeans da farar shirt k'amshi sai tashi yake ya d'auki wayar shi ya k'ira Sadeeya, bata d'auki lokaci ba ta shigo,
to her surprise ya sakar mata Murmushi
yace
"kai ni downstairs"
Kai ta gyada masa cikin sauri ta soma tura Shi a ranta tace
"tab!! Yau me ya samu Oga? Yau an tab'a masa Hajiya Amma yana Murmushi? Strange"

    Yana sauk'o wa suka yi ido hud'u da Hajiya ta kishingid'e kan kujera tana kallo ,
"A'a Abubakar tun d'azu nake tambayar ka
Ramlah tace
"baka d'aki ina ka shiga ne haka?"
Murmushi yayi yace
"na d'an fita ne Hajiya"
Nan da nan ta dafe k'irji tace
"kai Abubakar ka cika rigima ta Yaya zaka dinga fita cikin wannan halin da kake ciki?"
  Murmushi ya sakar mata kawai bai ce komai ba.
  Ya dubi Sadeeya yace
"je Ki k'ira Deenah"
kai ta girgiza ta nufi flat d'in Deenah amma bata ganta ba sam bata cikin d'aki kuma bata ko band'aki don haka ta sanar da Mr Imam cikin gaggawa Hajiyar kuwa Allah Allah take ma ace Deenah b'ata tayi shi kuwa ba k'aramin tashi hankalin shi yayi ba yana gudun kar ita ma ta bar shi...........

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245