MATATA GIMBIYATA 45-46

🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸

💘MY WIFE MY PRINCESS💘

STORY BY
JEEDDAH JA'O

WRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
         (NWA)

EDITED BY
ROOKIEY KAXS

         4⃣5⃣➖4⃣6⃣

    Haka plan d'in ya tafi smoothly Sadeeq har ya fara condemning Dr Bilal kawai rana tsaka Zeenat ta d'auke k'afarta cak daga zuwa asibiti, abu kamar wasa duk kulawar Sadeeq na hannun Mahmoud wanda shima ya san plan ne Amma bai san dalili ba, sai kuma Sadeeya y'ar aikin gidan, ko ranar da aka sallami Sadeeq daga asibiti Zeenat bata gida, da ta dawo ta iske shi cikin falo yana tambayar ta inda taje ko kallo bai isheta ba, haka Zeenat ta zama duk inda taga dama zuwa take Kuma a lokacin da taga dama, sannan kuma in ya tambaya sai tace aiki take yi. A kwana a tashi halin Zeenat gaba yake yi yanzu kam Sadeeq ya gama yarda da maganar Dr Bilal d'ari bisa d'ari ganin yadda take treating nashi kamar ba itace zee d'in da take fad'in ta fi kowacce mace sa'a ba, kamar ba ita ke fad'in bata jin dad'i in baya tare da ita ba, kamar ba ita ce wanda ke hana kanta abinci ba har sai ya dawo suci.
  Mamaki daban daban babu wanda bai yi ba. Hankalin Sadeeq bai sake tashi ba sai da ta kwashe kayan ta kaf zata tafi ,Sadeeq na rok'on ta Allah, Annabi amma bud'ar bakinta tace
"ni bazan iya zama da Mara amfani ba, ni bazan iya zaman bauta ba, ace wai wanka se an yiwa mutum haka ma bayi sai an kaishi, kaga gaskiya kayi hak'uri dan tafiya kam sai na tafi kawai ka sauwwak'e min"

   Zuciyar Sadeeq har huci take bai san lokacin da ya furta mata saki d'aya ba ta fice tana farin ciki shi kuwa tun daga nan yaji kawai gwara yayi sticking to plan d'in dan yaga wanda zata so shi ba dan wani abu nashi ba saboda Allah kad'ai...

*flashback end's*

Bilal ya dubi Mahmud yace
"yanzu kuma aboki na ya samo wanda ta so shi tsakani da Allah sannan ba dan wani abu nashi ba kuma mace me tawakkali"
  Kai Mahmud ya jinjina yace
"Toh yanzu Yaya zaka yi? Zuwa zakayi kace mata daman k'arya kake lafiya kalau kake ko me?"

  Kai Bilal ya girgiza
yace
"plan mu muka k'irk'iro sannan mu zamu goge kayan mu. Kawai abu ne mai sauk'i zai sanar da gida cewa zai tafi ganin wani kwararren likita a Egypt bayan sati biyu haka sai ya dawo full man! Aiki ya kammala".

  Hangame baki Mahmud yayi yace
"amma wallahi ba k'ananan y'an wasa bane ku."
duk suka bushe da dariya take..

       Bayan azahar ya dawo gida bai iske Deenah a flat nata. ba dan haka ya nufi falo da taimakon Sadeeya nan ya iske ta zaune tana  kallo bata ma san ya shigo ba se muryar sa da taji

"Gobe in Allah ya kai mu zan tafi Egypt ganin likita ance akwai yiwuwar zan samu sauk'i."
Murmushi ta sakar masa sannan tace
"Allah ya nuna mana goben"
"Ameen"
ya amsa sannan ya umarce ta da ta kawo mishi tea, ba musu ta mik'e zuwa kitchen dan had'o masa tea d'in, bata d'auki lokaci mai tsawo ba ta dawo d'auke da tea mug amma kafin ta ajiye masa Ramlah ta banke ta daga cup d'in har sugar duk suka juye mata a jiki.
  Duk da Sadeeq ya ga abin da Ramlah ta aikata damuwar sa jikin Deenah da tea d'in da ya zuba mata a jiki dan haka ya matsa kusa da ita  yana k'ok'arin goge mata da handkerchief nashi.
  Ramlah cikin salon Munafurci ta d'an lankwashe kai 
"Am sorry Auntyyy Deenah I didn't see you coming!".
   Deenat ta fahimci ita ma Ramlah so take ta rama abunda tayi musu da safe dan haka ta dake ta chanza salo.

    Fuskar Sadeeq ta shafa gami da sakar masa Murmushi ta rik'e hannun shi me handkerchief sannan tace
"kar ka damu, ni a waje na wannan ai ba komai bane am alright' barin had'o maka wani tea d'in just give me a moment".
Kai kawai ya girgiza alamar
"Toh"
   gaba d'aya salon Deenah tafiya take da imanin Sadeeq, ya ma manta laifin Ramlah ko existence nata a falon.

   Buga k'afa tayi ta fice cike da bak'in ciki. Wato duk yadda tayi Deenah ta dama ta ta shanye.
   Bayan ta kawo masa tea tana shirin goge inda wancan tea d'in ya zube.

"Deenah!"
Hajiya ta k'ira sunan ta.
Kai ta d'ago tace
"Na'am Hajiya"
ta amsa cike da kulawa yayinda Hajiya Ke sauk'o wa daga bene ,sai data k'ariso falon taja balance kan kujera sannan ta cije baki tace
"Kinga bana cin spaghetti ki taimaka ki dafa min  ko macaroni ne yanzu pls dan yunwa nake ji"
  Shu'umin dariya Deenah ta sakar tace
"yanzu ma kuwa Hajiya ! ba de macaroni ba? Barin dafa miki"
   Jin haka yasa Hajiya ta tsorata Amma ta dake tayi Murmushi tana duba Sadeeq kar ya ga abunda Ke faruwa shi kuwa hankalin shi na kan TV bai ma san me ake yi ba.............

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245