JARABAWA TACE 181~185

JARABAWA TACE



yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                          (NWA)


                     1⃣8⃣1⃣➖1⃣8⃣5⃣

   Kuka Fu'ad keyi sosai yana sabbatu, kallonshi Dr yayi yace "wayace maka yanzu ta mutu kake kuka haka?" Da sauri ya d'ago ya kalli Dr yace "kana nufin bata mutu ba? Amma kuma kace muyi hak'uri?" Dariya Dr yayi yace "muje Office" ba musu suka d'unguma sukayi office d'inshi....
   Da sallama suka shiga, gurin zama yabasu saida yagama rubuce rubucenshi kana ya d'ago ya kallesu d'aya bayan d'aya, kan Fu'ad ya aje fuskarshi tambayar Fu'ad yayi yace "ya kake da ita?" Matata ce yabashi amsa kowa kallonshi yakeyi suna murmushi, wannan kuma iyayenta ne. Girgiza kai yayi yace "yayi."
   Kallon Uncle yayi yace "Alh dama tana da ciwon zuciya ne?" Eh ya bashi amsa, toh miyasa ake d'aga mata hankali? Kodayake mijinta ya kamata ya amsa wannan tambayar ido Fu'ad ya zaro, yace "Dr bansani ba Allah" marairaicewa yayi kamar zaiyi kuka...

   Murmushi Dr yayi yace "to amma miyake kawo mata damuwa haka a shekarunta bai kamata ace jininta yau ba har yakai 250 gaskiya ba k'aramin sa'a kukayi ba dan idan da tsohuwa ce da idan bata rasa ranta ba zatayi paralyze" gaba d'aya sukace "Dr ba abunda ya sameta ko?" Dariya yayi yace "babu dogon suma ne tayi amma yanzu munshawo kan matsalar jininta ya komai daidai dan haka saiku kiyaye adaina b'ata mata rai abinda takeso ayi k'ok'ari amatashi"..
    "In shaa Allah Dr bazata k'ara neman abu bata samu ba" Yaya ce ta fad'i haka, hannu ya mik'ama Fu'ad yace "Congratz matarka na da rai baza ayi gawa biyu ba kamar yanda ka fad'a lallai matar nan taka kanaji da ita dayawa" dariya kowa yayi..
   Aflan yace "Dr zamu iya ganinta yanzu?" Mizai hana kuje kuganta amma karku dameta da surutu..
   Godiya sukama Dr suka fita suka nufi d'akin Lady...

   Da sallama suka shiga d'akin kwance suka tarar data tana bacci ga numfashi tana fitarwa a hankali, k'are mata kallo nayi duk ta rame tayi wani irin fari, tausayi taba kowa na halin datake ciki...
   K'arasawa wajen gadonta Fu'ad yayi  yaja kujera ya zauna k'uri ya mata da ido kamar mai nazarin wani abu, kanshi ya d'ora bisa hannuta da aka samata drip yace "Lady kiyafeman wlh ban tab'a san kowa ba saike ke nakeso zan iya komai akanki pls kiyafeman ina sanki san da bazan iya misaltashi ba ki taimakeni kisoni koda kad'an daga cikin sanda nake maki ne"..
   Babu wanda Fu'ad bai ba tausayi ba wurin, dafashi Uncle yayi yace "kayi hak'uri komi yazo k'arshe" girgiza kai yayi yace "dasauran rina a kaba Daddy kamanta kalamanta d'azu? Cewa fa tayi ta tsaneni" mai da kanshi yayi bisa hannunta yana hawaye...

   Hawayenshi ne ke d'iga kan hannunta, a hankali tafara bud'e idonta, d'akin ta fara bi da kallo idanuwanta ta sauke kan Fu'ad dake tafaman hawaye...
   D'ayan hannunta tasa ta shafi kanshi, dasauri ya d'ago jin anshafa mashi kai suna had'a ido tayi sauri ta juya kanta dasauri ya tashi yace "Lady kiyafeman" k'in juyowa tayi kuma bata bashi amsa ba, sudai su Uncle sun zama yan kallo dan babu wanda ke magana...

   "Lady kiman magana konaji sanyi" mizance maka? Bayan ka kasa cinye Jarabawar dana maka Fu'ad ashe duk k'arya kake fad'a akan san da kake man miyasa zaka zab'i bak'anta man rai akan farin cikina? Miyasa ka zab'i soyayya da yar uwata tabbas nasan na maka abubuwa marassa dad'i amma ban cancanci irin wannan daga wurinka ba, wlh Fu'ad tun randa nafara ganinka naji inasanka sai dai ina gudun karna k'ara shiga halin dana shiga duk abinda na maka ina tursasama kaina ne bawai da niya ba idan na maka komawa d'aki nakeyi na kulle kaina nayi kuka"..
   Wani irin farin ciki ya rufeshi jin Lady tace tanasanshi...
   Wlh Lady kena keso ba wata ba duk abinda na gaya maki ba k'arya kuma maganan Inteesar da kikeyi setup ne, dasauri ta juyo ta kalleshi d'aga mata kai yayi yace "i mean it" kallon Aflan tayi dan tasan duk shi zai shirya komai, dariya Aflan yayi yace "daina dogon tunani aiki nane nina had'a komai..."

  Yaya ce tayi magana tace "sai ku warware mana mi kuke nufi dan kun jefamu a duhu" dariya Uncle yayi yace "nima dai abinda zance kenan"...
   Aflan yace "yanzu kuwa zakuji komai" zama sukayi gaba d'aya shiru ya biyo baya na d'an wani lokaci sannan Aflan yace "kamar yanda kuka sani nina tsara komai ganin irin wahalar da Fu'ad kesha kan Lady..

     Ranan da na rakaku gidansu, da dare ya kirani yace yana nemana danaje na sameshi nace mashi gani lafiya yake nemana? Bai ban amsa ba sai kuka daya saman hankalina yatashi ganin yana kuka, dakyar nasamu yayi shiru nace mike damunshi yace man zaije wajen Lady idan tak'i amincewa dashi wlh zai kashe kanshi akanta, kuma na tabbata da zai iya, hankalina ya gama tashi kallonshi nayi nace "ina da shawara idan zai amince" dasauri ya kalleni yace "idan zata kawo mashi mafita wlh zai bita..."
   Kallonshi nayi nace "soyayya zaka fara" mik'ewa yayi zumbur yace "Aflan kana da hankali kuwa? Kasan mi kake fad'a?" Kamoshi nayi na zaunar dashi nace ai bakaji k'arshen magana ta ba ka mik'e, ba soyayya gaskiya zakayi ba so nake kayi soyayya da wata amma plan ne za'a had'a...
   Girgiza kanshi ya dingayi yace "bazan iya ba bazan so na b'atama Lady rai ba" kallonshi nayi nace wai baka da aiki sai karka b'atama Lady rai? Ita take b'atamaka soyayya da zakayi da wata ita zai sa ka gane idan Lady tana sanka ko bata sanka haka na dinga lallashinshi har ya amince zaiyi...
   Kallona yayi yace "to kasan ni bansan mata ba fa?" Dariya nayi nace yabar man komai a hannuna akwai wata cousin dina kuma galfrnd d'itace nasan zata iya komai, ya shirya muje wajenta gobe..

   Washe gari mukaje wajen Inteesar nafad'a mata duk abinda zatayi da farko taso k'in amincewa amma da taga raina yab'aci shine ta amince..
    Randa Fu'ad ya yaje wajen Lady duk muna tare mu duka ukun idan ta amince mashi to shikenan idan tak'i to Inteesar zata fara aikinta, koda Fu'ad yajema Lady k'in amincewa tayi dashi daga nan Inteesar tafara aikinta...
   kallon Lady yayi yace "duk wayar daren da Inteesar keyi dani takeyi bada Fu'ad ba, duk abinda kikaga yafaru shirine ba dagaske ba ranan da kika ga pix d'insu a IG ranan na sakashi kuma namaki tagging dan nasan da kinga nottification zaki shiga, Anty Lady babu Alaka'ar soyayya tsakanin Fu'ad da Inteesar asalima Intee girl frnd d'ina ce kuma ita zan aura in shaa Allah.. irin tsananin san da Fu'ad ke maki yasa na shirya wannan abun dan ina tausaya mashi kuma ina sha'awar ki aureshi cz zakiji dad'i.
   Kallon iyayenshi yayi yace "kunji abinda yafaru"...
   Ajiyar zuciya Uncle yayi yace "baku kyauta ba da kuka ma Lady na haka"..
   Dariya Yaya tayi tace "sun kyauta mana"..

   Hawaye ta share ta mik'ama Intee hannu alamar tazo, tashi Intee tayi ta isa wajenta tana hawaye, hawayen ta share mata tace "kiyafeman kan marin dana maki cikin rashin sanine" hawayenta ta share mata tace "karki damu Anty Lady"...

  Rik'e hannunta Fu'ad yayi yace "pls Lady kice kina sona" murmushi ta mashi ta juya kanta, juyowa yayi da ita yace "pls kice" dariya tayi tace i love you from d buttum of my hrt" wani irin ihu yayi yana dariya...
   Salati Yaya tayi tace "ashe bakuda kunya?" Dariya yayi ita ko ta sunne kanta bisa cinyar Inteesar..
   "Hajiya d'agama matata cinya kinji" Aflan ne yafad'i haka yana d'aure fuska, hararshi Fu'ad yayi yace "bazata d'aga ba" tsaki Yaya tayi tace "kanajinsu fa?" Dariya Uncle yayi sosai yace "to mizance masu zamani ne kema ai zamaninmu munyi haka" dariya Aflan da Fu'ad sukayi sukace "Daddy fad'a mata dai..
   Allah ya shiryaku nikam banyi haka gaban iyayena ba..

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245