JARABAWA TACE 196~200

JARABAWA TACE


yar_ficika


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                          (NWA)


When i think of you d word, "strong" immediately comes  to mind.  Use dat strength to get well soon Tweety..💔😭


               1⃣9⃣6⃣➖2⃣0⃣0⃣

   Lady ta warke tsab kamar ba ita tayi ciwo ba, dama ciwon na ganin za ama mata kwacen Fu'ad ne lolzzz..
    Kwance take ta d'aga kanta sama komi take tunani oho, wayarta naji tayi ringing idanta ta aza kan screen d'in wayar ganin sunan Fu'ad yasa ta saki wani irin murmushi, wanda ni kanshi bansan ma'anarshi ba. A hankali ta d'aga wayan "Hello" abinda tace kenan murmushi yayi daga d'ayan b'an garen yace "bae ya kike?" Lafiya lau ta bashi amsa, "ya missing d'ina?" An gayama ina missing d'inka ne, dariya yayi mai sauti yace "ko ba'a fad'a ba nasan kinyi" murmushi tayi tace "to banyi ba"...
   Shikenan tun da bakiyi ba sai nazo ba yau kenan, marairaicewa tayi tace "please kazo you know i miss you so much rabon da in ganka fa tun jiya" dariya yayi yace "kema kin san dole nazo kedai kiman kwalliya kinji" baka da matsala, haka suka cigaba da firarsu cikin so da k'auna daga k'arshe sukayi bankwana kowa ya aje waya...

   Tsintar kanta tayi da san yima Fu'ad abinci, tashi tayi ta nufi kitchen kaza ta d'auko daga frigde wanke kazar tayi tas kana ta sakata a roba, attarugu da albasa da garlic ta jajjaga tana gamawa ta kwashe ta saka curry da thyme da spices da su maggi ya mutse su tayi gaba d'aya kana ta shafama kazar nan tas, tana gamawa ta saka ta a micro oven...
   Flour ta d'ebo 3cups ta had'a samosa..
    Tunanin abinda zata girka mashi tayi can ta tuna couscous ne fav food d'inshi, store ta nufa ta d'auko couscous, pride couscous wadda taji kayan had'i gashi yayi wara wara source tayi wadda hanta ce zalla kana ta had'a coslow, kafin kace mi k'amshi ya gauraye gidan...
   Fruits tai blanding ta had'a   fruits salad wanda yaji kayan k'amshi tana gamawa ta saka a fridge, daidai tana fito da kazar ta datake ta faman k'amshi...

   Daga baya taji an rufe mata fuska, sanin waye zai rufe mata fuska yasa bata damu ba, sakinta yayi ya d'ora kanshi bisa bayanta yace "Anty Lady kinji k'amshin girkinki kuwa? Wlh tun daga waje nakejin k'amshi lallai yau zamu kwashi delicious.."
   Dariya tayi tace "kai dawa zaku kwasa delicious d'in?" Nida yan gida mana ban gane me kike nufi ba..
   Juyowa tayi ta kalleshi tace "to waya gaya maka ku namawa?" Wa kika mawa? "Mijina mana" ta bashi amsa, kai bari na gayama ba mai cin abinnan inma da wanda zai ci to Uncle ne dan ku kam ba abinda zan baku...
   Dariya yayi yace "sai na koma gidan su Fu'ad d'in muzo tare dashi tun da dama ni abokinshi ne kinga idan mukazo tare dole kibamu muci" dariya tayi tace "saboda gaka mai kwadayin tsiya?" komi zakice kice amma Allah girkin nan bai wuceni, dan bak'in hali gamu yan gida baza'a bamu ba sai wani Fu'ad, yana tafiya yana mita har yabar kitchen d'in, dariya tayi ta girgiza kai ta cigaba da aikinta...

    Tana gamawa ya kwashe komai a kula, ta zubama yan gida nasu Deeyerh ta kwalama kira da sauri tazo tace "Anty gani" yauwa Deeyerh kinga kula's d'innan? "EH" nagani Anty, yauwa to abincin Fu'ad ne ki kula dasu wannan kuma na kune na gida ki kai kan daining, ba musu ta kwashi na gida ta nufi daining dasu. Fita Lady tayi ta nufi d'akinta..
   Tana shiga d'aki toilet ta fad'a danyi wanka tana gama wanka ta d'auro alwallar magrib, fitowa tayi ta kabbara sallah bata tashi daga inda take ba sai da tayi isha tayi adu'o i kana ta mik'e dan ta shirya...
   Mai ta shafa na company makari simple makeup tayi dan batasan hayaniya ta shafe jikinta da turaruka kalakala wanda ya bada wani k'amshi na daban wanda duk wanda ya shak'i k'amshin sai yaji sanyi a ranshi...
    Gaban wardrobe ta tsaya tana tunanin kayan da zata saka, wata sabuwar pink super ta jawo touch of backgroud d'in super blue  riga da skrt ne sakasu tayi ta kifa d'aurin d'an kwalin kayan sun zauna chif jikinta sai kace dama jikinta aka k'erasu, kallon kanta tayi a mirror wani killer smile ta saki wanda ke tafiya da imanin duk wanda akamashi ita kanta tasan tayi kyau bama k'arami ba jikinta ta feshe da turare designers sun kai kala uku, ya salam abinda ni yar_ficika na iya fad'a kenan, wannan san k'amshi haka sai kace *FOUR STARS*

   Wayarta tafara ruri sanin waye ke kiranta yasa tayi dariya, k'arasawa tayi ta d'auki wayar "gani nazo" abinda yace kenan "ok gani nan zuwa" ta bashi amsa...
    Tana kashe waya ta kira Deeyerh da sauri tazo kallonta tayi tace "ki kai Fu'ad parloun Uncle ki kwashi kayan abincinshi ki kaimai nd drink d'inshi na cikin fridge" to ta amsa dashu ta juya ta fita...
    Sake fesa turare tayi ta d'auki gyalenta blue ta saka takalminta aldo shima blue, kallon kanta tayi a mirror ita kanta tasan tayi kyau ko ba'a a fad'a ba..
   Hanyar fita ta nufa daidai d'akin Yaya suka ci karo da ita Yaya na kallonta ta fara dariya, kumbure fuska tayi ta juya tace "wlh zakija mashi na fasa zuwa" da sauri Yaya ta rik'ota tace "yi hak'uri bani iyawa da rigimar Fu'ad" dariya tayi ta juya ta nufi parlourn Uncle...

   Da sallama ta isa parlourn tsaye yake yasha getzner fara k'afarshi slippers ne na puma ga kanshi ya d'ora hula k'amshin turaren rasasi kawai ke tashi  masha Allah abun saini dana gani lolzzz..
    Amsa mata sallamar yayi tare da ware hannunshi alamar taje, nok'ewa tayi tana dariya, takowa yayi yazo gurinta d'ago kanta yayi yace "ni kikema haka?" Dariya tayi tace "kasan fa ba kyau ni ba muharramarka bace ba" dariya yayi yace "ai kin kusa zama ko?" Toh kabari sai na zama mana, kallonta yayi yace "Matata kinga kyan da kikayi? Wlh kamar a d'aura mana auren yau nakeji" dariya tayi tace "saurin mi kake ai inda rai kamar gobe ne" haka dama zakice, kallonshi tayi tace "kaga kyan dakayi gaskia ina kishi" tana fad'a tana bubbuga k'afarta k'asa..
    Rungumota yayi ta gefenshi yace "kinsan ke kad'aice daga ke ba wata dan haka ki daina tada hankalinki kinji ko?" D'aga kanta tayi tace "naji"...

    Hannunshi ta kama suka k'arasa cikin parlourn zama sukayi suna fira, "wai ina Aflan ne?" Dariya tayi tace "d'azu ya gama man rigima to inaga yaje gidansu Inteesar"...
   Abinci ta zuba mashi ta kamo hannunshi tace "sauko" ba musu ya sauko, mik'a mashi tayi, kauda kai yayi "miye haka? Abincin dana makane baza kaci ba komi?" Ido ya zaro yace "ni na isa ba haka nake nufi bafa" ya kake nufi? kibani abaki yana d'aure fuska...
    Ita abunma dariya ya bata tace "kayi hak'uri kaci da kanka" Allah idan ba zaki ban ba na k'oshi...

   Sanin halinshi yasa dole ta dinga bashi yanaci yana mata santi itako in banda dariya ba abinda takeyi haka tagama bashi dan sai da yace mata wlh amai zanyi kana ta kyaleshi kallonta yayi yace "lallai nayi sa'ar mata dayawa nikam am lucky gata mai kyau iya abinci bugu da k'ari ilimin zamani dana arabic" dariya tayi tace "duk ni kadai?" Eh mana ai kinsani..
    Bae kiman take away d'in samosa kinji? Angama, Deeyerh ta kira ta kwashe kayan tace "tasamu fowl paper ta juye samosa ta kawo mata" haka ko Deeyerh tayi...
  
   Fira sukeyi sosai kowa yana bayyana ma d'an uwanshi yanda yake sanshi, hannunta Fu'ad ya kamo yace "Nafeesah walh sanki yaman illa daban sameki ba  da bansan halin da zan shiga ba" Murmushi tayi tace "nice dana rasaka a rayuwata dana tafka babban kuskure fatana kayafeman duk abinda na maka"  hannunshi ya d'ora bisa leb'enta yace "duk abinda kikayi kina da hujjar yin haka..."
    Haka dai suka dinga firarar soyayya sai sha d'aya yabar gidan ba dan sunso rabuwa da juna ba dan dai bayan da zasuyi ne...

©FEEDOHDEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245