RASHIN GATA 66-70

🌼🌼 *RASHIN GATA* 🌼🌼

         *TANBARI*
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

```NAH```
*FOUR STAR*🌟🌟🌟🌟

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HUSAYN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```

*PAGE DIN BABBAN SADAUKARWA NE GA NAGARTA OFFICIAL* Muna matukar jinjina Mu tare dayi muku fatan alkhairre. *FOUR STARS✨✨✨✨ NA ALFAHARE DAKU*

66-70

    Koda ya k'arasa gida cikin sauri yayi parking motarsa ya fito, aman da alamu Daddy baya nan dan bai ga motar sa ba hakan ba k'aramin b'ata mai rai yayi ba shi da yakeso yayi shirin komai a yau aman kuma yadawo gida Daddynsa bayana tsaki yaja yayi part dinsa, bedroom d'inshi ya shiga yayi wanka sana ya fito yabi lafiyar gado duk dajin kiraye kirayen sallah da akeyi aman hakan bai hanasa bin lafiyar gado ba,
ae kam atake barci yayi gaba dashi.
   Koda ya farka biyar saura minti bakwai, cikin azama yamike yafada toilet alwala yad'aura ya had'a azahar da la'asar babu ko addua'a ya mike (wa iya zubillah wannan wace irin rayuwace shikenan dan mutum suna da kud'i sai abinda ya gadama zaiyi tabbas wasu yaran masu kud'in basu san miye addinini ba bare su san ya akeyinshi Allah yasa mudace kabamu yara masu tsoronka masu san addini)
   Sai da ya huta sosai a cikin d'akinsa kana ya mik'e yasa kaya, wando da riga yasa kayan sun masa kyau sosai sanan ya fita zuwa part d'in Mummynsa.
   Cikin farin ciki har wata yar dariya yake saboda ya fara tunani ta yarda zai sa akori Dr Nana daga asibiti, yana gab da shiga parlourn yaji an rungume sa, yasan babu Wanda zai masa haka sai Mummynsa hakan yasa shi juyawa ya rugumeta shima, My Son ina kashiga ne yau? murmushi yayi yace "Momy barci nayi" shiyasa ka kashe phone's dinka? Eh Mummy ina son yin barci ne sosai, ok babu damuwa Son muje ciki kaci abinci, dariya yayi yace "to Mummyna" hannusa taja zuwa dainnning

***** ****** ******* *****

    Koda Nana ta k'arasa gida bata bari Mama ta gane halin da take ciki ba saboda sanni irrin tashin hakalin da zata shiga, "Nana ni yau naga kindawo da wuri inji dai lafiya?" Ta tambayeta Eh Mama Lafiya lau babu aiki da yawane, ayya sannu kinji! yauwa Mama, kallonta Mama keyi tana murmushi.
  Tace "Nana kinga yarda kika Kara zama Kuwa?" Dariya tayi tace "a'a Mama yanazama?" Kinyi kyau fatar jikinki ta sauya tayi fresh, Allah sarki Umma sauyin gurine.

   Satin ta d'aya bata zuwa aiki, yayin da kullum Sameer yana kan hanyar zuwa asibiti domin wata babbar niya *cikar burinsa* aman kuma kullum yaje maganar d'aya ce batazo aiki ba, hakan kuma bai hanasa zuwa kullum ba, yau takama Monday, dan haka Nana ta tashi tun 7:00 tafad'a bedroom domin yau tayi niyar zuwa aikinta tana fitowa wayarta tafara k'ara dakamar bazata d'auka ba gani Dr Ammar ne yasa ta saurin d'auka, sallama yayi cikin salon voice nasa amsa mashi tayi, yau Monday zaki shigo aiki koh? "Eh Dr insha Allah" tabashi amsa to Allah yakawoki Lafiya Dr Nana, "Ameen" tace tare da saurin katse wayar, pink d'in leshi ta saka ta d'auko pink hijab ta saka tayi kyau sosai, baka gane komai a jikinta sai fuskarta itama daga baya tad'auki nik'af d'inta ta rufeta Lokacin da tagama har 8:29 tayi, koda tafita Falo Mama tagani tana shirya mata breakfast rungume Mama tayi tace "Allah sarki Mama nah har kintashi" d'iyatama ta tashi Bari ni? Dariya tayi tace "hakane kumafa" sai da ta cika cikinta da abin ci kana tad'auki key motar ta tafita...
    Shima Can gurinsa shirin yake farar shadda ya saka da bak'ar hula domin aikin shaddar tasa bak'i ne yayi kyau matuk'a domin komai na Sameer mai kyau ne yau ko ta kansu Mummy bai biba bare ace abinci, motarshi ya d'auka yafita zuwa asibiti.......

   Koda ta 'karasa asibitin ko office d'in Dr Ammar batayi ba direct office d'inta ta wuce jakar jikinta kawai ta cire ta aajiye sannan taja kujera ta zauna yau garin da sanyi-sanyi dan haka ko nik'af d'inta bata cire ba illah d'aukar glass d'inta datayi ta mak'ala ta fara duba tarin takardun da jummai ta tara Mata..
    Murmushi kawai tayi tafara dubawa daya bayan daya, bayan zuwanta da 40 minutes Sameer ya iso asibitin tare da addua'ar Allah yasa yau tana nan fake d'in katin magani da ya taho dashi ya d'auko ya kalla tare da tun tsirewa da dariyar mugunta kafin nan  fita daga motar.
   Direct office d'in Dr Ammar yayi dan bai da masaniyar tazo ko ba tazo ba, knocking yayi "yes" Dr Ammar yace daga ciki, kai tsaye ya bud'e ya shiga, a'a Sameer yau ma kaine? "Eh nine" kawai yace yaja kajera ya zauna ina fatan yau tazo? Shuru yayi kamar bai san wa yake nufi ba kayi shuru? Kallonshi yayi yace " wa kake nufi?" Kafini sani Kowa ce ae murmushi Dr Ammar yayi sannan yace "nima banda masaniya akai aman munyi waya tace zatazo" cikin azama ya mik'e ina zuwa kawai yace dashi yayi hanyar fita yana ji Dr Ammar yana masa magana aman ko juyawa bai ba bare ya basa amsa.

   Hanyar office d'in Dr Nana yayi yana Kama handle d'in k'ofar yaji abude, hakan yasa ya tura k'ofar cikin k'arfinsa jikake bam!!! Dai-dai lokacin data d'ago domin ganin mai mata mumunar aikin nan.
    Sameer ta gani hakan yasa ta mik'e itama yau ko damai yazo sai ta sauke masa shi, domin ta daina kyalesa yana sata kuka da bak'in ciki dan ba tasan mai ta tsare masa ba. Tura k'ofar yayi ta rufe ya yinda ita kuma ta bisa da kallo kujera yaja ya zauna kafin yayi mata nuni da hannu alamar itama tazauna, "bazan zauna ba" tunda ba kai ka ajeni ba infact ae ba office d'in ka bane da zaka sa na zauna, murmushi yayi ya kafeta da ido shi dai ya rasa mai take b'oyewa a fuskarta ta, cikin tsawa yadaka nata "kizauna nace" cikin sauri tabi kujerata ta zauna, dariyar k'eta yayi yace "ashema matsoraciya ce ke? duk ina tsiwar take?" Bansani ba dan  ita ba'a tab'a yimata tsawa irin wannan ba shiyasa ta tsorata dashi, kafin komai bara na farayi miki introducing d'in kaina. Am sameer Muhammad Saddam, d only son of Alhaji Muhammad Saddam. ina fatan kin gane? Kibi ahankali wannan office d'in da kike tak'am na kine nan da wani lokaci zai zama banaki bane...

   Kallonshi tayi a wulak'ance tace "tun da kai nakema aiki sai ka koreni" dariya yayi yace "ki zuba ido kigani yanmata in dai nine sai kinyi dana sanin shiga gonata"..
   Wai kai mi kake tak'ma dashi? Dukiya? Mulki? Hmmm toh duk anyi wanda suka fika kuma basu ci nasara ba dan haka in shaa Allah bazaka tab'a na sara akaina ba, haka kikace? "Eh haka nace" tabashi amsa..
   Toh shikenan zaki sha mamaki, kallonshi tayi tace "Malam get out of my office"..
   Dariya yayi yace "soon zai zama office d'in wani" yana fad'ar haka ya mik'e ya fita...

FOUR STAR'S✨✨✨✨

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245