RASHIN GATA 116-120

🌼🌼 *RASHIN GATA* 🌼🌼

         *TAMBARIN*
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

```NAH```
*FOUR STAR*🌟🌟🌟🌟

*Xarah Bukar*
*(Cute xarah)*

```SADIYA ABDULLAHI
(STYLISH BCH)```

*FEEDOH DEEDOH*
     *(YAR FICIKA)*

```ZAINAB Y HUSAYN```
``(AUTAR HAJIYA)```

116-120

K'asa ya zauna wanwas dafe da kansa yana zubda hawaye, wani irin k'una da rad'adi zuciyar sa ke masa tamkar an tsikaramai mitsilla, ganin ba mafita yasa ya mike adaddafe ya karasa b'angaransa..

Hannuta Umma ta rik'a suka nufi dakinta had'e da  nema wa mazaunin su gurin kan gado, fuskartan juna sukayi, Umma tace "Nana meke tsakanin ki da Sameer ?
Ware ido tayi jin tambayar bambarakwai, sai kuma tayi sauri duk'ar da kai saboda wani nauyi da kunyar Umma dasuka dirar mata farat daya, "Umma babu komai tsakanin mu, nikaina na rasa dalilin sa na d'auramin karan tsana" ta fadi tana wasa da yan yatsunta.
"Ke kina sonshi ne? Acewar Umma, gabanta ne ya fadi tayi sauri maido dubanta gareta, cikin rawar murya ta mike tsaye tana fadin "nikam babu so araina, shiyasa ban taba sa son wani azuciyata ba". murmushi Umma ta saki batare datace uffan ba, tsum Nana tayi ta fice daga dakin jiki a sabule, palo ta zauna bayan ta sauke doguwar ajiyar zuciya, harga Allah bata kaunar Sameer kawaici yasa bata fayyace wa Umma zuciyar taba ta fake da amsar data bata.

****
Bayan Sati biyu, Sameer bai kara yadda sun hadu da Nana ba, duk da k'ok'arin tausasa zuciyar sa yake akan ya daina son fuskarta amma ya faskara, sau da dama ko rufe idanuwan sa yayi surarta kadai ke masa ambaliya cikin k'wayar kansa amma daya tuna da Nana ce dogon tsaki yakan ja yayi azaman kaucewa tunanin, kullum safiyar Allah yakan yi shirinsa tsaf ya tafi office ya zauna koda baya da aikin yi bayan ya tashi da yamma gidan Mama yake nufa yaci abinci susha hirar daga bisa ya koma gida, ta bangaren Nana kuwa bai taba d'ad'arata ba, tuni ta koma bakin aikinta da wuta wuta, da safe take leka momy sannan ta wuce asibiti, abu daya ke damunta kwana biu nan da Mama ke mata batun aure akan lailai tafara kula masu zuwa ne manta, ayadda take balagagga mace mai shekaru sama da ashirin gidan miji ne ya kamaceta, ba yadda bata roki mama tabar xancen ba taki bari tamkar kara tunzara ta ake.

Jikin Momy ya samu cigaba sosai, zaune take palo suna hira da Umma, ya shigo da sallaman sa, amsawa sukayi atare ya karasa kusa da Momy ya zauna, dariya k'asa k'asa Umma take tana duban momy tace "ai yarinyan nan Nana Allah kadai zai biyata da hallacin da tayi mata..." Ba ta ida magana ba ya mike zumbur tamkar an tsigare shi, daure fuska yayi tsam yabi hanyar fita da hanxari, azuciyar sa banda Allah ya isa ba abunda yake cewa Nana, babu tatanma ta lashe k'urwan iyayansa shiyasa basu da xancen sai nata, parking lot ya nufa ya shiga motar sa hade da janta afusace.

"Sameer kenan, Allah ya shiryamin kai" Umma ta cigaba da fadi tana darawa, dariyar momy tayi tace "aini inda zai yadda ya aureta da naji dadi"
Cab'e xance Umma tayi da cewa "toh mexai hana ki hada su auren, kece Uwa nasan zai amince da maganarki, ni kaina na dade da ayyana hakan a raina"
"anya kuwa Sameer zai yadda, kinsan shi da kyaman talaka kuma dai ba sonta yake ba"
Galala Umma ta bita da idanu. "aikuwa Nana ba abar kyama bace, hakan kadai zaisa su shirya kuma Sameer ya san darajan mutane, bawai atsaya bin ra'ayin saba,  batun so kuma ki ajiye shi gefe, sau nawa ana aure ba so kuma azauna lapia".
Girgiza kai Momy tayi tana jinjina xancen Umma aranta, tabbas aurawa  sameer Nana ne kadai hanyar dazata biya nana da alherin datai mata, "haka ne hajiya Sadiya, amma ya zamu tuntub'i Sameer da Nana da zancen".
"Sameer ba matsala bane, Nanan ce matsala"
Kallon rashin fahimta Momy tayi mata, Umma ta cigaba "zamu aura mai Nana batare da munji ta bakinsa ba, kinsan dai ko sama da k'asa zasu had'e bazai aminci da auran ta ba, aura masa ita zamuyi idan yaso ya hadiyi zuciya ya mutu"
Magana sosai momy da Umma sukayi, daga baya suke yaken shawarar xantawa da Abba, koda ya dawo da dadaddare zuka iske shi da batun, yaji dadi sosai hade da sanya alheri.

Washegari koda Nana tazo gidan Momy kadai ta tadda a gidan, Umma da Abba basa nan sun nufi gidan mama dan tattaunawa.

*Four Stars*🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245