RASHIN GATA 76-80

🌼🌼 *RASHIN GATA*🌼🌼

®```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

*NAH*
``` FOUR STARS```🌟🌟🌟🌟

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR_FICIKA)*

```ZAINAB Y HUSSEAIN```
```(AUTAR HAJIYA```

*SADIYA ABDULLAHI*
  *(STYLISH BCH)*

```ZAHRA BUKAR```
```(CUTE ZARAH)```

76-80

   Sameer yana gida kan gadon sa babu abinda yake face murmushi da zuba ido yaga wani action za'a d'auka kan Dr? Tunda maganin daya rubuta bana ciwon bane hasali a d'akin Dady yaga kwalin shine yai copying nasa tunda ya nada target akan wannan sharrin.
   Mama wai in tambaye ki mana?, inajin ki Nana yi tambayar ki amma kafin nan d'aga ni kada ki karya ni kin wani kwanta bayan kinsan k'afar ciwo take ba wani ciwo Mama Allah na fijin dad'in kwanciya a haka d'an yimun kalaba ko uku ce nagaji da barin kan a haka...
   Yo dama sai da nace kizo nai miki ko kije kika k'i, au kada na manta yimun tambayar inaji Allah ya sadai suruki nasamu.
  Nana darajar ki d'akin mijin ki, nifa kullum babban burina naji kince yau ga wanda yazo gun ki ko naji anyi sallama amma shiru..

   Kallon Mama tayi tace "Mama kada kisaka komai aran ki, aure lokaci ne idan yayi saikiga nayi auren." Hmm kullum dana maki maganar aure haka kike ceman..
   B'ata fuska Nana tai tace "Mama kingaji dani ne kome? Nifa wallahi mazan ne sai a hankali su ba kwarya ko tangaran bane daza kace za kasan nagari shiyasa ma ni ban tab'a jin wai zanyi aure ba duk da ana tsaidani sosai."
  Nidai gaskiya kifara tsayawa ba haka zan saki gaba ina kallo ba, to Mama abar maganar..
   Marairaicewa tai kana ta dubi uwar ta furta cikin bad mood tace "Mama wai dama mutum bai maka komai ba baka damu dashi  ba ba bugu bare zagi ko fad'a saika tsane sa kayi ta burin quntata masa?".
   Nana kenan ana haka sosai amma meyasa kikamun wannan tambayar? Ba komai wata ce wajen aikin mu wani ya tsaneta shine nake mamaki dama ana haka ashe anayi to Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu, "Ameen dai" Mama tace bacci fa yazo bara nai wanka sai na kwanta Asubah tagari Mama, yauwa Nana ta...
*****
   A can nurse d'in bata tsaya duba sunan maganin ba d'aukar paper kawai tayi tafice zuwa pharmacy ta siyo da kanta ta b'allo maganin ta ciro goran ruwa na eva ta bata tasha...
   Sannu koh zakaji sauk'i yanzu tunda Dr Nana itace ta rubuta maki maganin sorry kinji, za kiji sauki'i yanzu..

   Kwanciyar patient d'in keda wuya idon ta yafara qafewa bakin ta yafara fidda miyau daga nan sai jiki ya rikice nan da nan Dr Mikel da Dr Goodwin sukayo kanta dan bata taimakon gaggawa...
   Cikin mintuna kad'an suka gano tasha maganin da bai kamata tasha ba tunda bana ciwon ta bane..
   Suna cikin maganar ne bayan sun gama duba ta da allurai saiga chief da Consulta na Asibitin ya shigo yakuma ji komai karb'ar maganin yayi yaga wani iri ne?, OMG waya rubuta wannan maganin before nafara tambayar waya rubuta ko me?, let me see her file...
   Nan da nan aka d'auko masa karb'a yayi ya fara karanta abubuwan dake ciki.
   Tsaye ya mik'e fuskar sa cike da tashin hankali yace "waye wanda ya rubuta? yanaso ad'auki action akan asibitin mu?" Hawan jini ke damun ta an kuma bata maganin Diabetes kunsan kuwa gara abata magani daban akan a d'auki na diabetes abata...

   I swear da bada sauran kwanan ta ba yau sai ta mutu, taimakon mu d'aya rabi aka bata wacce ko wanne useless ne ya bata? sauri Dr Goodwin yace "Oga i think DR ce"  Nana? Who ia Dr nana wace ita? New Dr d'in nan...
   Ohhh wannan yarinyar amma kuma kaf maganin dake cikin pharmacy d'in nan na America ne(USA) daga can ake ka mana komai shi kuma wannan na UAE ne Dubai, Qatar,Saudi,Oman etc.
Ya akayi yazo cikin pharmacy d'in mu?.
Ammmm duru-duru kowa yafara har Dr Ammar wanda aka kira daga baya.
Shouting yai musu aka, tell me mana ya akayi aka samu cikin pharmacy namu?, Oga babu maganin ya qare shine ta rubuta aka fita aka siyo...
   Wayace babu jiya aka sauke container kuma kaf ta magungunan mu ne, nakuma bada order akawo nan ajera ya haka to?
Kai ya dafe sosai yaji ciwon abun, tsaki yai daga baya yace "DR Nana ta kori kanta bazata zo ta kashen asibiti ba" yana gama fad'a ya fice.
Jaje suka fara daga Hausawan har Indai da 'yan Miami cox kowa yasan Dr Nana da kirki haka kowa ya watse ya koma kan aikin sa...

  Dr Ammar ya tausayawa Nana sosai ba halin yace kada tazo gobe aji mutuwar sarki cikin bakin sa dole yaja bakin sa yai shiru.
******

   8:00 Dr tagama shirin ta, abinci ma saida Mama tai da gaske sannan tai 4 spoon yau jinta take wata iri kamar wadda akai wa duka ga gajiya ga rashin dad'in zuciya haka ta waske dai ta tafi...
   In 20 Minutes tashiga cikin harabar asibitin.
Reception taje anan suka gaisa da kowa, amma wani abu ganitai ana kallon ta idan suka had'a ido da mutum sai taga ya juya bata kawo komai ba taje wajen saka hannu.
Dubawa tai amma babu sunan ta ciki, sawa zatayi taji ance "Dr aikin ki ya qare ai biyoni office kiyi signing nakuma tura da statement d'in duka wajen Honorable."
Dr bangane ba it seems kamar anyi wani abu which ni bansan komai ba akai totally...
    Oh I can't say anything kina sane or whatever ba ruwa na bazakiyi kisa ace wannan asibitin ne....
   K'irji ta dafe tace "kisa? Haba Dr nayi kama da mai kisa?" Bansani ba ki biyoni nace, jiki ba kwari ta bishi Office d'inshi...

   File d'in ya mik'a mata "waya duba wannan jiya?" Nice ta bashi amsa, mik'a mata takardan maganin yayi yace "kinsan mi mika rubuta mata?" Hannunta na kyarma ta karb'a...
   Ido ta zaro sakamakon abinda ta gani "No Dr bani bace wlh bani na rubuta ba taya zan rubuta mata wannan? Bayan nasan hawan jini ke damunta" in bake bace wacece? Wlh ban sani ba all i knw bani bace ba Dr bliv me wlh bani bace..
   Murmushi yayi yace "is to late Dr Nana ga takardanki nan ta sallama zamu cigaba da bincike idan mungano bake bace fine in kuma kece kin tafi kenan"..

   Hannunta na kyarma ta karb'a in banda Innalillahi wa inna ilaihir raji'un babu abinda take cewa..
   Fita tayi tana hawaye Dr Ammar taci karo dashi yana ganinta yayi saurin juyawa "Dr" takirashi k'in amsawa yayi yakuma k'i juyowa, kaima ka yarda dani ce na rubuta?..
   Sai a sannan ya juyo yace "wlh Dr ban yarda ba dan nasan bazaki iyayin haka ba amma kiyi hak'uri"..
   Murmushin takaici tayi tace "bakomai Allah na tare da mai gaskia" tana kaiwa nan ta juya ta tafi...

    Tafiya take ga duhu tana gani gabanta, jitayi an bushe da dariya daga bayanta, juyawa tayi da sauri ganin Sameer na dariya yasa zarginta yake neman tabbata..
   Basai kin wahalar da kanki wajen tunani ba ni nayi komi yan mata..
   Takowa yayi ya k'araso gabanta yace "dama na gaya maki ba'a ja dani ban tab'a neman abu banci riba ba kuma in bazaki manta ba na gaya maki sai kinbar asibitin nan gashi kin barta yanmata sai kuma a koma karkara dan nasan daga can akazo" dariya ya sake fashewa da ita..
   Kallonshi tayi tace "Sameer kenan kasani Allah ba azzalumin kowa baneba kuma in shaa Allah nan ba da dad'ewa ba zakayi dana sanin abinda kaman kaji ko"..
   Tana kaiwa nan ta juya ta wuce ta nufi motarta...
   Dariya yakeyi har yana buga k'afa motarshi ya fad'a yana dariya...

FOUR STARS 🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245