RASHIN GATA 81-85

🌼🌼 *RASHIN GATA*🌼🌼

```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

*NAH*
```FOUR STAR'S```✨✨✨✨

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI SHEHU
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HASSAN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```

*Dedicated this page to my Luvly Khadija Abdullah Shehu (Hajja ce) & my sweet Anty maijiddah Musa (Anty jidderh)*

81-85

   Koda tafita daga asibiti, bakin titi tayi parking d'in motar ta kanta ta d'aura saman sitiyarin tana mai cigaba da kuka mai tsuma zuciya yayinda ta yaye nik'af d'in dake fuskar kuka take kamar ranta zaifita shima bayanta yabi koda yazo saitin motar ta glass d'in motarsa ya zuge yana mai hango yanayin yarda take kukan duk da bai ga fuskar ba hakan bakaramin dad'i yayiwa Sameer ba..
   D'agowa tayi da zumar tafiya, tana juyawa suna ido biyu da Sameer dubanshi take idanuwanta cike da kwallah hankalinta atashe aman ta kasa furta koda kalma d'aya sai hawayen dake sharara akan kumatunta.
   Babu abinda yake banda murmushi daman nasan haka zata faru, domin duk Wanda ya shiga sabgar Sameer dole yayi kuka da idonsa sai asannan tayi maganar itama, idan kayi nasara rabani da aikina yanxu kaima akwai lokacin da zakayi kuka da idonka akan wanan aikin watarana, juyawa tayi  batare da tak'ara ce masa komai ba ta tada motar tah, tabarsa da tunani fal a cikin zuciyarsa...

    Kaga yariya saikace aljana, k'ilama aljanarce shiyasa ma kullum tana cikin bak'in abu ashe tasan abun da tak'unsa tsaki yaja mtseew aikin baza koma maye naji dad'i tunda an koreta, Motarsa ya fusga sai gida yana cike dajin dad'i da farin ciki..
   Koda Nana taje gida kasa b'oye damuwarta tayi, Assalamu Alaikum Mama tah kina ina? Sai sallama take gidan shiru, wa'alaiku salam gani nan Nana, da gudu ta k'arasa ta rugumeta tare da fashewa da matsanecin kuka, subbahalah Nana mai yafaru haka? Mai Zan gani? Kuka kuma Nana?

  Janta jikinta tayi zuwa bakin gado, Mama nah na shiga uku ya rabani da farin cikina da burin uncle dakuma naki buri, ban masa komai ba Mama, wlh ban masa komai ba, aman shi ya shiga tawa harkan har yasa narasa aiki nah yau...
   duk magagun datake babu abinda Mama keyi sai kallonta cike da mamaki, "Nana wai maike damunki waye shi wanda ya shiga rayuwar taki? kuma mai yafaru dake a gurin aiki?" A tare ta jero mata tambayoyin nan, Duk babu amsar da Nana ta iya amsawa sai cigaba datayi da kukan, hankali Umma yayi mumunar tashi abinda bata tab'a yiwa Nana ba yau sai da tasa Mama ta dakamata wata uwar tsawa, zaki gayamin komi kuma waye shi Wanda yashiga rayuwarki har haka?.

    Mama Sameer ne wlh ban masa komai ba, nasani d'iyata nasan babu abinda zaki yima wani mara kyau yanzu gayamin waye Sameer kuma mai yayi miki?  Sai asanan ta kwashe labarin kaf tabawa Mama babu abinda tab'oye mata har k'aryar datayi mata cewa wani ya takurawa k'awarta ne a asibiti yau sai da ta k'aryata tace ita ya takurawa, tunda Nana tafara magana Mama ke hawaye yanzu yaza suyi kenan? Nana kin tabba shine kuma yayi miki haka? Eh Umma shine wlh.
   To share hawayen haka ae ubangiji Allah natare damu karki damu zuwa gobe sai mufara shirin komawa garin mu koh? a'a Mama gida da motar dasuka bani halak malak d'inane, aman duk da haka zamu koma can zuwa wani d'an lokaci sai mudawo, saboda inason nafara wata sana'ar da zan rik'e ki dashi, rungume ta Mama tayi suka  fashe da kuka.

  Dakyar Mama ta samu ta tsaida kukan ta, sanan ta samu tasa Nana ma tayi shiru wanka ta shiga tafito tazo ta kwanta hannuta rik'eda carbi tana ja, yayinda Nana ma tafad'a toilet tayo Nata wanka tare da d'auro alwalah.
  Yau Sameer cike da murna ya shiga gida a dainning yatar da Daddy da Umman sa, hatta Daddy dinsa yagane yau Dan nasa yana cikin farin ciki, my Son murna mai keyi ne yau? Daddy ae yau Rana tace, murmushi shima Daddy din yake, saboda Dan'sa yana cikin farin ciki, uhmm Daddy ina Momyna? Tana d'aki inajin barci ma take, ok Daddy bara na dubuta..    
  Umma bin bayyasa tayi da kallo har ya shige part d'in Mummy, tabe baki tayi saboda kwata-kwata batason banzar dabi'ar Sameer taranshin gaida manya da bayayi...
   Juyowa tayi ta kalli Daddy tace "yanzu kuna ganin tarbiyar da kuka ba Sameer daidai ce? Ka kalli yanda ya shigo baisan ya gaida mutane ba wlh ina jiye maku randa za kuyi kuka."
   Wai ke mi Sameer ya maki haka kika tsaneshi? Duka ma Sameer d'in nawa yake watarana zai daina. "Allah ya kyauta" Umma tace ta cigaba da abinda take...

   Akan gado ya sameta, tanata barcin ta, bakin gadon yahau, yafara kiran sunna tah Mummyna ya hau tashinta, uhm my Son inajin dad'in barcin nan fa ka tasheni, sorry Mum, koma barcinki, a'a na tashi kuma ae, noo Mum ki koma kawai, a'a son na tashi nace, kinci abinci? a'a yau banji dad'i ne shiyasa, bana jin sha'awar komai yanzu ido waje yake kallonta Mumy ba dai ciwonki ne zai tashiba? Haka dai na kejin alama my son....
   Kanshi ya dafe yace "na shiga uku Mummy mike shirin faruwa ne? pls nidai mubar nigeria d'innan"..
   Kanta ta d'ago kallonshi tayi da idanuwanta da suka juye suka zama jawur tace "Sameer da nan da can d'in ai duk d'aya ne kadai cigaba daman da adu'a"..
    Kuka ya fashe dashi maganar Dr tadawo mashi da tace " idan kayi sanadiyar rabani da aikina kaima zakayi kuka akan aikin nan" to gashi kuwa tun ba'aje ko ina ba ya fara kukan...

Four star's🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245