RASHIN GATA 96-100

🌼🌼 *RASHIN GATA* 🌼🌼

         *TAMBARIN*
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

```NAH```
*FOUR STAR*🌟🌟🌟🌟

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HUSAYN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```

This page is for our cutest & adorable Daughter *Miss xoxo*, as you grow
older we want you to fly out like a free
bird. Go forth and pursue all your
dreams. Live life to the fullest and make
sure that your happiness is second to
none. And while you are at it, just
remember that every time you need a
hug or a place to call your own, we are
always here, Never forget that Mom loves you much & more❤❤❤❤
     Stay Bless❤

  96-100

Waye Sameer

   Barrister Sameer Muhammad Saddam cik'ekk'en sunan sa, d'a ne tilo ga Alhaji Muhammad da Hajiya Sadiya (Umma), tsabagen so da k'aunar da Hajiya Zarah (Momy) ke mai tun haihuwar sa yasa Umma ta sallama shi ga Momy tamkar ita ta haife shi, cikin so da kauna gaba daya iyayensa ya taso, duk cikinsu yafi kaunar Momy sa tamkar ransa,  duk wata farin cikinsa bai wace Momyn sa ba shiyasa koda wasa baya son abunda zai tayar mata da hankali ballle yakai ga k'unan rai. Tun yana k'arami yake da burin zama barrister, Allah ya cika mai burin sa, sai dai zama barrister bai wani d'ad'arasaba kasancewar k'iyayya da yake ma talakawa aganinsa tsayawa kare hakkin talaka rashin aikin yine. Sau da dama yafi bawa cases din masu hannu da shuni attention duk da badan kudi yakeba ya kan yine amatsayin amfani da abunda ya b'ata lokaci sa ya karanta, aganinsa kudin da mahaifinsa ke dashi ya ishe su harma da budget din Nigeria gabadaya for 30 years.

****
  Sannu ahankali Dr Nana tagano mafarin problem din, ba tare da bata lokaci ba tafara aiwatar da aikinta cikin k'warewa allurai tama Mummy sannan ta matso maganin dake cikin tube ta shafa mata gaba daya sashen jikinta, ajiyar zuciyar samun relief Mummy ta sauke ahankali, nan take wani mugun bacci data kwana biu bata yiba ya kwashe ta. Murmshi Nana ta saki hade da janyo white blanket dake kan gadon ta rufa mata kafafunta sannan ta fito daga dakin.
   Ganin ta fito yasa suka mike daga inda suke Zaune, Abba ya fara da cewa, "Nana ya ya jikin nata ?" da sauki, akwai important magana dana keso ku sani about her illness..
  Katse ta Sameer yayi cike da taikaici, yace "stop beating around d bush, ki gayamana what is it about"
Bata kallesa ba balle ta tanka, focus dinta gaba daya nakan Abba da Umma dake sauraran abunda zata furta, "muyi maganar a office" ta fada hade da jiyowa ta kama hanyar cikin office dinta, da azama suka rufa mata baya cike da fargaba, zaune suka iske ta karasawa sukayi suka zauna a kujerar baki dake ajiye, dago da kanta tayi da niyya magana taga Sameer hakince kan kujera ya zuba mata manyan idanuwan sa, "shi kuma wannan waya ba shi izinin shigomin office" ta fadi aranta, shuru tayi batace uffan ba illa file din gabanta data hau dubawa, Umma dake hankalce dasu yasa ta gano bakin zaran, duban Sameer tayi tace "kai tashi ka fita, ka jiramu awaje"..
   Rai bace ya dubi Umma, kaman yayi kuka wai na fita sai kace wanda na shigo fadar shugaban kasa zaa koreni...
   Tsawa ta daka mai, ba shiri ya mike ya fice hade da bango kofar tamkar ginin zai tsage, yake kawai Abba yayi yana mamakin d'ansa da Nana tamkar masu ganin hanjin juna.
   Ajiyar zuciya Nana ta sauke sannan tace "jikin Momy da sauki, sadai kwanan biyu nan da bata samun medication on time da mis using dinsa yasa jikin nata yake nai man fin karfin ta, shawara daya ce Abba, ku samo nurse da zata zauna da ita tana kula da maganin ta da cinta da shanta, musanman magani da idan kayi wasa da tym dinsa wanda ka fara da farko rugujewa zaiyi azo kuma ana faman treatment daga farko, hakan bazai kawo sauki ba sai dai ma yakara symptoms na illness dinta."
    Hankali tashe Abba ke sauraranta bayan ta ida ya maido dubansa ga Umma, ikon Allah sam bama wasa da maganin ta, ya hakan ya faru ?

   Nikai na Alhaji mamaki nake, sam bama wasa da lokacin shan magungunan ta, kasan aikin marar lapia sai likita duban Nana Umma tayi tace "inaga daukan Nurse zamuyi gudun faruwar hakan nan gaba"
   Girgaza kai Abba yayi alamun shawarar bai kwanta masa ba, ya dubi Nana yace "yata mazai hana ki zama nurse dinta na gida, dan Allah karki gaji da bukatun mu ke d'ayace zaki iya mana wannan alfarma"
   Ware ido Nana tayi a tsorace tace, "Abba kuyi hakuri nikam bazan iya ba, zan daiyi kokarin samo maku nurse"

   Umma ce ta chafe da cewa "Nana ki taimaka bawai zamu hanaki aikin asibiti bane ko zamu rabaki da maihaifiyar kiba zuwa kula da Mummy na lokaci kadan zakiyi kafin ta samu karfin jikin nata"
   Shuru Nana tayi tana tunanin taya ma zata kai kanta gidan su Sameer yaji dadi wulakanta ta, gaskia bazai yuyuba  ta fada aranta.
  "Ki kwantar da hankalinki, albashi na musamman zamu cire maki" cewar Abba...
   K'wafa Nana tayi tana jin   takaici dalilin dayasa Masu kudi suke ganin money can buy everything, su aganin su kudin da zasu batane zai sa ta yadda, "Nana ba haka take ba" ta fadi aranta...
  Kallon juna Abba da Umma sukayi ganin bata da shirin tanka su, mikewa Abba yayi da niyyan tsugunawa rokonta tayi azaman mikewa tsaye  karasa wa gabansa tayi tana fadin "Abba dan Allah karka yi haka, idan ban taimaki Momy ba Allah zai hukunta ni abisa baiwar daya bani, ban amfane ta da ita ba, kayi hakuri zanyi amma da izinin mahaifiya ta".
  Sai sannan Abba yaji dadin kalamanta, shida Umma suka hau mata godiya, daga bisani suka fice bayan sun gama magana akan gobe zata fara zuwa gidan idan Mama ta amince...

  Dakin da Momy ke ciki suka daukota da taimako Sameer suka sanya ta ciki mota suka wuce gida batare dayasan abunda iyayensa da Nana suka zantaba.
  Kusan Magrib Nana ta dawo gida agajiye likis, ta iske Mama a kitchen tana kokarin tuka tuwo, da azama ta karasa ciki hade da gaida ta bayan ta amshe muciyar hannunta "Mama na hanaki aikin wahala bakyaji, dakin bari nazo nayi tuwon".
   Da badan bak'in da nayi ba aida tuni na dade da kwashe wa..
"Bak'i kuma? Mama suwaye bakin" Nana ta tambaye cike da mamaki.
Baban Sameer da matar sa suka zo..
  "what?" badai harda Sameer aka shigo mana gida ba ?

  Dariya Mama tayi tace "abokin naki waje ya tsaya, iyayen suka shigo sun min bayanin komai kuma ni na amince masu ki fara zuwa aikinki gidan".
  Haushi ne ya cika Nana, wato sun rigata zuwa gurin Mama, murmushin dole ta kirkiro tace "Mama nifa ba abokina bane saboda shi yasama bansan zuwa gidan"
  "Ina ruwanki dashi, kedai badai kiyi aikin ladan ki ki dawo ba" acewar Mama.

   "Hakane Mama ba ruwana dashi" ta fadi, amma aranta fadi take da ruwana dashi dan bazan lamunci cin fuska ko wulakanci garesa ba.

***
  Sanye yake cikin black & white suit daya kara fiddo da zahirin  kyansa, ya kwashi wayoyinsa da key car ya fito da azama ya wuce dakin Momy. Kwace  ya iske ta bisa gado, karasawa yayi gareta hade da zama gefenta yana fadin "Momy na" murmushi tayi dakyar, Hade da kare mai kallo gaida ta yayi ta amsa cike da kaunar sa cikin sanyi murya tace "Sameer yau ka tuna da office ne?"
Sosa keya yayi yace "inada da important case dazanyi attending ne" Mom ya jikin naki ? "Da sauki my son" ta amsa..
   Mikewa yayi tsaye yana fadin Mom saina dawo, kina bukatar wani abu ?
No, dear Allah ya dawomin dakai lafiya ta rakashi da adduar tsira sannan ya fice, baiyi niyya shiga gurin Umma ba ganinta da yayi a kitchen yasa ya karasa can,
"Ina kwana" yace da ita daga bakin kofar...
  Fuska tamke ta amsa mai da lafiya batare data juyo ta kalle saba, ba karamin haushi sa take jiba, tarasa hanyar da zatabi ta kutubar dashi daga mugun halayyan daya daukar wa kansa. Ganin bata basa fuska ba yasa ya fice daga gidan cike da kunan rai, ya tabbar fushin Ummansa bai da na tsaba da shegiyar Doctor nan daya tsana tamkar mutuwar sa, motar sa kirar Lykan Hypersport ya shiga yaja ta  afuzge. 

   Ciken red gown material tayi shirinta tsaf ta dauko white hijab tasaka hade da Nikab dinta, sallama tama Mama ta fito da hanzari kasancewar yau ta makara tashi bacci kuma awa kalilan ya rage lokacin medication na Momy ya cika, bata dau motar taba tafice ta tari taxi ta shiga bayan ta fadi mai Address da Abba ya bata. Mintuwa 30 suka iso gidan ta sallami taxi ta karasa bakin gate ta kwankwasa, ba tare da bata lokaci ba mai gadi ya bata izinin shiga dan Umma ta sanar mai da zuwanta....
  Daskarewa Nana tayi tsaye ganin tamfatsetsan gida mai kyan gaske, da sauri taja baya gabanta na dukan uku uku, "anya gidan ne" ta fadi aranta, tasan dai Sameer masu kudi ne amma batayi tunanin they are bastardly rich haka ba, Address dake jikin paper ta duba ta kara tabbatar da gidan ne, "no, i cnt be here" ta fadi tana ja da baya, sai kuma ta tsaya tunanin mi zatace da Mama idan ta koma gida, jiki sanyaye ta yanke shawaran karasawa ciki.
   Kofar palon bude ta karasa ciki hade da sallaman ta, Umma dake fito wa daga kitchen rike da flask na ruwan zafi ta amsa da farara'ansa, gaidata Nana tayi aladabce sannan ta karasa takawa ciki.
  Sannu ki Nana, Allah yayi miki albarka ya Mamaki ?
"tana nan kalau" ta amsa adan kunya, ta rasa dalilin dayasa take jin nauyin matan.....
  Muje na kaiki dakin Momy
Toh tace sannan ta mara mata baya tana mai karewa kayatancen palon kallo,
Momy na zaune kasan center carpet tana karin kumallo suka shigo, Nana ta gaida ta hade da tambayan ta karfin jiki "da sauki" Momy ta amsa mata tare da murmusawa, Pack din maganin Umma ta dauko cikin drawer ta mikawa Nana, amsa tayi hade da zama kusa da Momy tana kokarin balla magungunan....
    Umma sai kallonta take ganin bata da shirin cire hijab da nikab din jikinta, "Nana aida kin cire hijabin, muka dai ke cikin gidan"
Bata ce uffan ba ta yane nikab da hijab din atare, cigaba tayi da ballo maganin batare data dubesu ba, Umma dake kallon ta sai aiyyana tsantan kyan Nana take azuciyar ta,batayi tsammani tada kyau haka ba, "Allah ya baki, ga kyau da illimi da sanin darajan bill adam" Umma ta fadi aranta, mikewa tayi ta bar dakin ta koma kitchen kammala abunda take.
"Sorry Momy" cewar Nana.
"Yauwa Nanata, nagode kinji Allah ya baki miji na gari mai kyau kamarki"
Murmushi Nana tayi ta mika hannun dan daukan ruwan dake jug, sanyi ruwan yasa ta ajiye tace "Momy da ruwan sanyi kike shan magani?" Eh nafison shi da ruwan sanyi ba'a shan magani da abu mai sanyi shi kesa magani yaki nuna effect da wuri, hakan kuma ba karamin matsala yake janyo wa ba, bara na dibo ruwan dumi, ta karasa maganar bayan ta mike tsaye.

  Momy tace "ki duba store na kitchen akwai bottle water marar sanyi"
"toh" ta amsa mata hade da ficewa daga dakin, sam ta mance da sanya hijab, ta fito da kayan jikinta.

****
  Zaune yake cikin office chambers dinsa yana duba wasu file dake gabansa, can kuma yahau dube desk drawer, bai samu files din da yake naima ba, guntun tsaki yaja hade da mikewa afusace " shit** nabar su kan gado garin sauri" ya fada hade da surar makulin motar sa, fice wa zaiyi sukayi kicibis da secretary dinsa dake kokarin shigowa, yayi sauri bangajeta hade da wuce wa, bata damu ba, inda sabo ta saba da wulakanci boss dinta, harma gaba daya maaikata bai daukesu abaki komai ba karasawa ciki tayi ta ajiye mai wasu takardu dake hannuta.
  Cikin sauri yake tuki harya iso gidan, bangaransa ya nufa ya kwashe files din sannan ya fito, harzai fice yayi tunananin karasawa ciki duba Momy.
  Palon Nana ta tsaya waige waigen neman hanyar kitchen din bata gani ba, can ta hango eva water kan dining table, karasawa tayi tadau ruwan hade da dauka glass cup data gani gurin, zuciya daya tafara takunta tana tsiyaya ruwan cikin copin, bata ankara ba taji ta gware da mutum adan tsoro su biyun suka ja baya kansancewar bai lura da ita ba wayar hanunsa yake dannawa, dago wa tayi ta dubesa hade da sauri sakin glass cup din akasa tayi sauri ja da baya, cikin barin jiki tahau warware dankwallin kanta dan rufe jikinta, kekam yayi tsaye yana zuba mata daradaran idanuwan sa cike da mamakin kyan da dirin da Allah ya axurta ta dashi, wace ce ita, miya kawo ta gidansu, ya fadi aransa, babu tatanma cikin matan da Momy ta saba kawo masa ya aura ne, amma wannan karon tayi zaben data dace dashi, duk aransa yake zancen nan...
  Dankwali tane ya fadi kasa, Tayi azaman dukawa ta dauka ya rigata dukawa atare suka sanya hannayansu kan dakwali, da sauri Nana ta cire hannunta saboda wani irin shock daya ziyarci zukatansu..
"Sameer miya dawo dakai" muryar Umma ta katse masu hanzari, akidime Nana ta rugu hanyar da taga Umma ta fito, ta shiga tana kuka sakin baki Smeer yayi yana bin yalwan gashin kanta da kallo, "ba dakai nake ba" Umma ta kara fadi cikin kausar murya.
"Ba komai" ya fadi, rai bace ya juya waje bata  tare daya karasa ciki ba...
  Murmushi Umma tayi tadau dankwalin ta bita dashi kitchen din da taga ta shiga, bayan fridge Nana ta makale tana kuka cike da tashin hankalin Sameer yaga jikinta, raina ta zaiyi yasamu daman kara cin zarafinta, saidai kuma yadda ta lura da kallon dayake mata tamkar bai gane taba...
  "Nana kukan mi kike ?" Umma ta tambayeta
Sauri goge hawayan tayi tace "ba komai Umma, dama ruwan zan dauka"
Gashi, Umma ta mika mata ruwan da dankwalin, nagode ta fada tayi sauri ficewa daga kitchen din ayayinda Umma tabita da kallo.

  Tuki yake yana tunanin kyakyawan fuskar Nana da bai san itace biggest enemy dinsa ba, can yayi tunanin kaman ya taba ganin sexy eyes dinta awani guri, amma a ina ? Ya tambayi kansa, kasa tunawa inda yasan idanuwanta yayi, ya cigaba da murmusawa harya karasa office...
  Jiki sanyaye Nana tayi zaman gida har magrib tayi, kansancewar bata da patient asibiti shiyasa bata leka ba, gabatar da sallah tayi  sannan ta masu sallama tabar gidan, d'an wunin datayi yasa ta gane halin karaminci da kirki na iyayen Sameerduk da d'ardar data keyi bai hanata hira da Momy ba, Momy macece ma'abociyar surutu da barkwanci sam bata kaunar ganin mutum cikin wani halin rashin. Koda ta koma gidan kalau ta iske Mama, taji dadin ganinta cikin koshin lafiya, hirar karamcin yan gidan tayi ta bata labari, koda Mama ta sako mata batun Sameer bata rai Nana tayi ta fice daga dakin, Mama na mata dariya.

  Kusan 8 Sameer ya dawo gida agajiye, bayan yayi dinner ya shiga gurin Umma da niyyan tambayan ta yarinyar daya gani dazu sai kuma ya fasa ya tsaya jira ko zata mai zancen,  basar dashi tayi ganin alamun akwai zancen dake tafe dashi amma ya tsaya mata kame kamen can wata hira daban,
"kai bacci nake ji tashi ka fita" tace dashi.
Umma tun yanzu, bamu gama magana ba, ina  sauraranka, wace magana ke tafe dakai? Sosa keya yayi yama rasa abunda zai ce, ya mike tsaye yana fadin " sai da safe"
"Allah ya tashemu lapia" ta amsa mai ciki ciki.

  Dakin Momy ya shiga ya iske tana bacci, ya rage mata sanyi Ac sannan ya fice zuwa bangaransa cike da tunanin abunda ya faru dazu.

***
   Da wuri Nana tazo gidan, ta taimawa momy tayi wanka ta shirya ta tsaf, duk aikin da Nana take bata cire hijab da nikab dinta ba, dan tayi alwashin Sameer bazai kara ganin fuskar ta ba, ba yadda Momy batayi ba ta cire sam taki cirewa acewarta tafison zama haka.
   Bayan Momy taci abinci, Nana ta ballo magani tana bata, sukaji turowar kofar dakin an shigo ba tare da sallama ba, jin kamshi turaran sa yasa Nana bata dago ba, ta gane makiyin tane ba kowa ba.
Ware ido Sameer yayi cike da mamakin ganinta,
"momy mai matsiyaciyan nan keyi agidan nan?" ya fada hade da karasawa gareta, Dauke kai Nana tayi cike da kunan rai...
  Momy tace "sameer bana son haka, dan Allah ka fita kafin kasa tayi fushi ta tafi"
Ran Sameer ya bacci, yau Momy ke koransa akan matsiyaci yan nan, juyawa yayi ahasale ya fice hade da banko kofar dakin da karfi.
" kiyi hakuri, kinji? Mummy tace mata haka
"ya wuce" Nana ta fadi hade da kirkiro murmushin dole, ba karamin shakan abunda yayi mata tayi ba.

   Bai zarce ko ina ba sai parking lot, ya shiga motar sa yabar gidan tamkar namijn zaki, tunanin inda zai nufa yake dan bazai juri zama gida daya da matsiyaciyar ba can dabaran zuwa gidan Mama ya fado masa, murmushi ya saki hade dayin U turn yabin hayar gidan su Nana, wata zuciya na fadi mai kai da bakasa yarta miye naka da zuwa gurinta?
  Kai ya girgiza, a fili yahau fadin " hating her daughter doesnt mean i dont like her, i so much love her saboda she is a good woman ba kamar matsiyaciyar yarta ba"
  Magana yayi tayi tamkar tababbe harya iso gidan.

FOUR STARS🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245