RASHIN GATA 46-50

🌼🌼 *RASHIN GATA* 🌼🌼

         *TANBARI*
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

```NAH```
*FOUR STAR*🌟🌟🌟🌟

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HUSAYN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```

  46-50

*ASALIN LABARIN*

      Alhaji muktar shahararran mai k'udi ne yana da mata ta aure guda d'aya wato Hajara, zaman soyayya suke tsakanin su, "ya"yan su biyu tal a duniya Mubarak shine babba sannan Amina Mubarak yana da mata da yara biyu duk Mata.
     duk arzikin alhaji Muktar hakan bai hana Amina auren talaka ba, Aliyu shine mijin Amina bashi da ko sana'a sai dai kullum ya fita yayi aikin k'arfi sannan yasamo na abinci.
    Haka kuma bai san taje gida da nufin a taimaka mata  Yayan ta baya k'aunar yanayin da take ciki, kasan cewar yana matu'kar sonta, bai had'a sonta da kowa koda kuwa d'an shi na cikinshi ne tsananin son dayake mata shi yasa tsana mai tsananin tsakanin matar shi da ita Amina..

********
   Sallama yayi ya shiga cikin gidan da leda a hannun shi zama yayi akan turmi yana kallon ta yace "Amina karb'i wannan garin kwakin ki had'a mana" cikin sanyin jiki ta karb'a dama tana da ragowar k'uli na shekaran jiya data rage.

    Shekarar su biyu da aure amma har yanzu jiya ei yau tana gama had'awa ta kawo musu zasu fara ci kenan yaro yayi sallama gidan atare suka amsa tace "yaya dai?" kallonta yaron yayi yace "wai kije gida ana neman ki" cikin mamaki tace "injiwa fa?" Hajiya Murja tace azo ace miki yanzu aka kawo su Alhajin ku da Hajiya sunyi accident.
     saurin tashi tayi tare da sakin kwakin data damka a hanun ta cikin tashin hankali tayi hanyar shiga d'aki hijjab ta d'auko ta fito zatayi hanyar waje Aliyu yayi saurin rik'ota tare da cewa, kibi a hankali karki tafi cikin gaggawa kanta kawai ta iya girgizawa alamar to tayi waje da sauri tana addu'a cikin zuciyar ta.

*********
    Tana k'arasawa tun a k'ofar gida taga mutane sunyi jigum babu mai walwala a cikin su tun tana fargaba kar dai wani abu yasamu Abban ta da Mamanta har takai ga shiga gidan taji wasu suna cewa Allah ya jik'an alhaji da Hajiya ya kawo haske, wallahi mutanan kirki ne, da gudu tayi cikin gida tana kuka, cikin hanzari mutanen dake gurin suka taimaka aka k'arasa da ita d'aki kasan cewar fad'uwa tayi kafin ta iso falo.
       Hak'ik'a ahalin gidan sun yi kuka sun gode Allah haka Amina ta kuma lalacewa komai yayi mata zafi sai dai Yaya Mubarak yayi musu abubuwa na yau da kullum a haka aka shafe shekara d'ayq da rabi Yaya Mubarak yace "za'a raba musu gado" bai d'auki komai ba a cikin nata ya damk'a matasu hand 2 hand' bayan kwana biyu dayin haka Amina ta d'auki gadon ta ba tare da kowa yasani ba ta bawa mai gidan ta da nufin yayi jari har a fitar mata da dukiyar ta.

********
   Bayan wata biyu Allah ya azurta Amina da ciki lokacin Aliyu ya fara safarar kaya daga England zuwa Nigeria rayuwa ta fara musu dad'i haka ma Yaya Mubarak yana jin dad'in yadda k'anwar ta shi ta koma, uwa uba abinda ke cikin ta sallama sukayi da Aliyu da nufin zai tafi London saro kaya sosai tayi missing d'inshi haka suka rabu cikin kewa.
     Sai dai tunda Aliyu yabar Nigeria, bai sake neman family d'inshi ba har gashi yanzu 4month babu shi ba waya bare sak'on gaisuwa anyi cigiyar anyi shirun anyi addu'a amma shiru, Yaya Mubarak shiya nemi ta bashi kud'inta a neman mata wata sana'ar nan take ta gaya mai abinda tayi sosai yaga laifinta yamata fad'a tare da nuna mata illar hakan ga rayuwar sosai tayi kuka har ta godewa Allah, haka Yayan ta ya cigaba da kula da ita ganin haka yasa itama matar shi tace bata yadda ba har fad'a sukayi data ga haka sai ta fad'a bokaye. kwatsam ta wayi gari Yayanta sun bar k'asar batare da saninta ba haka tasha kuka kamar zata mutu shike nan yanzu batada kowa ga tsohon ciki ga wahalar rayuwa........





*four stars*🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245