RASHIN GATA 86-90

🌼🌼 *RASHIN GATA* 🌼🌼

         *TANBARI*
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

```NAH```
*FOUR STAR*🌟🌟🌟🌟

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HUSAYN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```

  86-90

   Kuka yake sosai wanda shi kanshi baisan miya sashi kukan ba, d'agowa tayi ta kalleshi tace "My Son yadai? Bafa cema nayi ciwon ya tashi ba inajin alamu kuma koma ya tashi ai ga wannan Dr d'in yar albarka" dasauri ya kalleta. D'aga mashi kanta tayi tana murmushi, kasan bansan kukan ka oya share hawayenka, ba musu ya share hawayenshi, daidai su Daddy na shigowa...
   Ganin Sameer na kuka ya k'araso da sauri yace "my Son mike damunka ne naga kana kuka?" Daddy sai kuma ya sake fashewa da kuka, hankali Daddy ya tashi ita dai Umma yar kallo ta zama....
   Son miye matsalarka dan Allah gayaman, cikin shashekar kuka yace "Daddy jikin mummy ne ke neman tashi nidai mubar k'asar nan" kallon matarshi yayi cikin tausayawa yace "Mummyn Sameer miyasa baki gayamana ba da ba'ayi visa kuka tafi ba dan inaga visa d'inki ta k'are...."
   Dakyar ta d'ago tace "haba Alh ina ga da nan da can duk d'ayane nifa naji dad'in magungunan da Dr d'in nan ta rubuta mani kuma ai banace ciwon zai tashi bane ba, in ma naji zai tashi zan tafi na ganta.."
   Gabanshi ne yayi mugun fad'uwa nidai Daddy pls kai mata visa mubar k'asar nan. "Wai mike damunka ne Sameer? Duk fa inda mutum yake Allah ne ke bashi lafiya kawai ka cigaba da yima Mummmyn ka adua kaji" Umma ce tayi magana..
   Dakyar suka samu suka lallasheshi, nan suka yini saida lokacin bacci yayi kana kowa ya nufi d'akinshi, shidai Sameer ya kasa bacci maganar Dr kawai ke mashi yawo, tsoki yayi yace "koma aljanace wlh zan iya mata..."

                   *Washe gari*

    Nana! Nana!! Nana!!! A hankali take tashinta, mik'a tayi tare da salati bud'e idanta tayi da suka kumbur saboda kuka, murmushi ta sakar mata tace "Mamana yadai?" Rankwashin ta tayi tace "bansani ba" k'ara ta saki tace "Allah Mama akwai fa zafi" tana turo baki kamar zatayi kuka...
   Tausayin d'iyarta ya kamata sauri tayi ta goge hawayen da suka zubo mata, "tashi ki shirya kin san yau zamu wuce yobe fa" abinda tace mata kenan..
   Mamanah ai wanka kawai zanyi naci abinci jiya na mana parking kina bacci wanda zai kaimu k'arfe goma mukayi dashi zaizo..
   Toh tashi ki shiga wanka kinga yanzu kusan tara, mik'ewa tayi ta nufi hanyar toilet, juyowa tayi tace "Mama idan muntafi yaushe zamu dawo?" Nana nima ban sani ba ni dama zaki yarda muyi zamanmu can ki nemi aiki nan kisa yan haya...
   Dawowa tayi ta zauna kusa da ita tace "Mama kiyi hak'uri mudawo nan d'in na cigaba da kasuwanci aiki ya fita raina kuma ma da wuya na samu aiki idan har sun b'ataman record d'ina" k'arashe maganan takeyi tana hawaye...
   Hawayenta ta share mata tace "kidaina kuka Allah zai maki sakayya in shaa Allah nayarda idan mukaje ko wata ne idan mukayi sai mudawo"....

   Dasauri ya shiga d'akin sakamakon mafarkin da yayi da ita, yana shiga ya tarda ita bisa gado tana nishi kad'an kad'an ga kumburi da tayi, ihu yasaka sai kace ba d'an musulmi ba. Musulmi da aka sani idan abu ya sameshi yace "Innalillahi wa inna ilaihir raj'un" amma shi ihu ya saki Allah sa mudace Amin...
   Dasauri Umma da Daddy suka k'araso cikin d'akin dan ganin mike yafaruwa, "lafiya Sameer?" Tambayar da suke mashi kenan, kasa amsa masu yayi sai nuna masu Mummy da yayi, dasauri suka isa wajenta, ina ko da suka isa Mummy babu rai...
   Kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Umma da Daddy "Daddy  minene? Kuman bayani" Sameer Mummynka fa bata numfashi, "what" abinda yace kenan sungumarta yayi ya nufi waje da ita bin bayanshi su Daddy sukayi, mota ya sata suka shiga fad'awa yayi yaja mota da k'arfi horn ya dinga dannawa a gigice maigadi ya wangale mashi gate, cinna kan motarshi yayi ya fizgeta sai a sibiti....
   Gudu yake shararawa bisa titi wanda Allah kad'aine ke tsare dasu, gudu yake yana hayawaye..
   Bakin gate d'in Nizamiye hospital ya tsaya horn yayi akazo aka duba bayan motarshi, ana bud'e mashi gate ya saka kan motarshi baiko samu wurin parking ba ya fito yana kwalama nurse kira...
    Dasauri nurse ta fito da gadon marassa lafiya aza Mummy akayi bisa gadon aka nufi emergency da ita, gabanshi ne yafad'i tunowa da yayi Dr Nana bata asibitin kuma ita kad'ai ce wacce tasan cutar Mummy..
   Kuka yake sosai tare dayin da nasanin abinda yafaru da yasan ciwon Mamanshi zai tashi da baiyi sanadiyar raba Nana da asibitin nan ba, daya biyo ta wata hanyar da zai muzguna mata, dan ya tsani Dr kuma har yanzu yanajin tsanarta a ranshi...

   Maganar nurse ce ta dawo dashi daga dogon tunaninshi tace "Alh munsamu ta farfad'o dama doguwar sumace tayi saidai a yanzu bamu da Dr d'in datasan irin cutarta.." dasauri Daddy ya d'ago yace "ina Dr Nana?"...
   "Dr Nana tabar asibitin nan" daga baya sukaji magana, juyawa sukayi dan suga waye Dr Ammar ne tsaye k'arasowa yayi yace "Alh Dr an koreta daga asibitin nan" dasauri ya kalleshi yace "miyasa?" Kamata akayi..... Ya kwashe komai ya fad'ama Alh..
   Dafe kanshi Daddy yayi yace "ban tunanin salihar yarinyar nan zata iya aikata abinda kuke zarginta dashi" shidai Sameer kanshi k'asa gabanshi sai dukan uku uku yakeyi..
    "Yanzu Dr Amma ya zamuyi?" Umma ce ke tambaya...

   Dr Nana bata da hannu akan abinda yafaru, juyawa sukayi gaba d'aya wata nurse ce tsaye. K'arasowa tayi tace "tabbas Dr Nana bata da hannu akan abinda akace tayi saboda ni shaida ce" dasauri Sameer ya mik'e harara ya wurga mata amma ko inda yake bata kalla ba...

   Gabana Dr Nana ta rubuta ma marar lafiyar nan magani tace idan masu jinyarta sunzo in basu, fitsari ya kamani na nufi toilet ina fitowa naga wannan bawan Allah gaban gadon marar lafiyar har ga Allah ban kawo komai akan ganin dana mashi ba randa abun yafaru ranan naje hutu d next day wata nurse ta kirani take gayaman nan take nasan bawan Allah nan ne dana gani tsaye ya k'ulla mata sharri, ni kuma sanin gaskiyar abinda yafaru yasa nazo yau dan na wanke ta amma Dr bata da laifi..
   Saukar marin da yaji a kuncinshi shiyasa ya firgita marinshi takeyi sai da Daddy ya rik'e mata hannu...
   Kasakeni komi yaron nan yayi kune sila irin tarbiyan da kuka bashi kenan wlh kun cuceshi kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita...

    Kallonshi Daddy yayi yace "abinda ta fad'a gaskia ne?" Eh gaskia ne ya bashi amsa kai tsaye, jikinshi ta k'ara nufowa ta zabga mashi wani marin wanda sai da ya kifa, rik'eta Daddy yayi yace "kiyi hak'uri.."
   Sameer miyasa kayi haka? Dama shiyasa kake san afita da mamarka waje? Saboda abinda ka aikata? Shiru yayi ba amsa tare da k'arajin tsanar Nana a ranshi...

Dr Ammar yace "Alh ba anan ya kamata kuyi maganar nan ba" hakane Dr kaman alfarma ka kiraman Dr a waya, ba musu yayi dailing number d'inta jinta kashe ba k'aramin d'aga mashi hankali yayi ba..
   Kallon Daddy yayi yace "wayarta kashe" murmushin takaici Umma tayi tace "yau gashi zaka kashe maihaifiyarka da kanka duk irin cewar da kake baka had'ata da kowa ba ashe k'arya kake tabbas ka cika butulu Mummy bata cancanci ka mata haka ba gashi ta sanadiyarka zata rasa ranta sanin kanka ne duk garin nan ita kad'ai ce Dr da tasan ciwon Mummynka amma yau gashi ka rabata da aikinta ko tunanin wadda ta rik'e ka da amana bakayi, saboda kana tunk'aho kuna da kud'i? toh yau gashi kud'in ya kasa sai maka lafiyar Mamanka"..
   Daddy ne yace "Dr kasan gidansu?" Eh nasani Alh, muje dan Allah ka kaimu..
   Ba musu yace "to" kallonshi Daddy yayi yace "wuce muje" ran Sameer idan yayi dubu ya b'aci dan yasan ba k'aramin k'ask'anci Umma zata mashi gaban Nana ba dan dai ba yanda zaiyi haka ya bisu suka shiga mota....

FOUR STARS🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245