RASHIN GATA 121-125

🌼🌼 *RASHIN GATA* 🌼🌼

         *TANBARI*
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

```NAH```
*FOUR STAR*🌟🌟🌟🌟

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HUSAYN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```

121-125

   Suna isa sukayi horn maigadi ne ya fito dan ganin su waye, da sauri ya wangale masu gate cinna kan motarshi Daddy yayi sai da yayi parking kana suka fito, wajen mai gadi Daddy yaje suka gaisa hannu yasa a Aljihu kud'i ya d'ebo masu yawa wanda bansan iya karsu ba yaba Baba maigadi, godia ya shiga yi mashi har suka shige yana godia...
   Da sallama suka shiga, amsawa tayi tare da tashi tarosu tayi tana dariya, rungume juna sukayi ita da Umma suna yaushe gamo. Cikin parlourn suka k'arasa zama sukayi, da sauri ta tashi ta kawo masu abinsha, saida suka gaisa sukayi fira....
   Zama Daddy ya gyara yace "Maman Nana wajenki mukazo" dasauri tace "ni Daddy?" Murmushi Umma tayi tace "eh mana.."
   "Neman iri mukazo" abinda Daddy yace kenan neman iri kamar ya? Dariya Umma tayi tace "Daddyn Sameer kamata yanda zata gane mana.."
  Gyaran murya yayi yace "inasan na had'a auren Nana da Sameer" dasauri ta juyo tace "What?" Dafa ta Umma tayi tace "please karkice bazaki yarda ba wlh Nana ita kad'ai zata iya gyara Sameer dan Allah ki taimakemu..."
   Ajiyar zuciya Mama tayi tace "taya za'a had'asu aure? Bayan kunfi kowa sanin basu san junansu su tsani junansu dan Allah kubar wannan maganar.."
   "Karki damu ni nasan suna san junansu, su tasu salon Soyayyar kenan" Umma ce tace haka. Maman Nana kiyarda damu wlh bazamu cuci Nana ba baza tayi danasani ba, shikenan Daddy naji amma wani hanzari ba gudu ba taya kuke ganin zasu amince da junansu a zaman ma'aurata?...
   "Inasan a d'aura masu aure batare da sun san junansu zasu aura ba kawai inasan kima Nana magana kice kin mata miji muma munsan yanda zamuyi da Sameer" cewar Daddy kenan..
  Shikenan Daddy amma wani hanzari ba gudu ba ya kamata kusan asalin Nana zaku iya zuwa Yobe ku bincika asalinta...
   Ay Maman Nana ke yakamata ki gayamana wacece ita bawai mu bincika ba, ajiyan zuciya tayi tace "shikenan yanzu kuwa zan baku labarin wacece Nana....." Kwashe komai tayi ta gaya masu bata rage masu komai ba, babu wanda baiyi kuka ba cikinsu, gyaran murya Dadddy yayi yace "tabbas Nana abin tausayi ce dake naji ina k'arasan na taimaka mata kuma ta hanyar aura mata d'ana zai sa na taimaketa..." Godia taima Daddy daga nan sukayi bankwana suka tafi....

   Su Daddy na isa gida daidai Nana na fitowa da sauri ta k'arasa wajen Umma ta rungumeta tana dariya, d'agota Umma tayi ta b'ata fuska tace "ina zaki kuma?" Turo baki tayi irin na shagwab'abbun yarannan tace "ina da patient asibiti ne kuma najira baku dawo ba shine na fito zan tafi.."
   Rungumeta Umma tayi tace "yi hak'uri Nanana naje unguwa ne" murmushi ta sakar mata "kinci abinci?" Umma ta tambayeta eh naci Umma nah...
   Gyaran murya Daddy yayi dariya tayi tace "Daddy ina wuni?" Nak'i na amsa tunda baki ganni ba, dariya tayi ta sunne kanta jikin Umma, murmushi Umma tayi tace "ina zata ganka ina kusa?" Dariya yayi yace "nasani Umma Nana bata ganin kowa indai kina kusa da ita". Gaba d'aya sukayi dariya....
   Kallonta Umma tayi tace "kije karki makara ko?" eh Umma nah. Peck Umma ta mata tare da fatan Allah ya bata sa'a....
  Duk abunnan daya faru kan idon Sameer ya faru, tsoki yaja yace "shegiyar yarinya mai kama da Aljannun dare ji yanda take shigema parents d'ina sai kace nata..."

   Sallama sukayi, Mummy ta taso ta tare su da fara'a....
   Sai da ta basu ruwa suka sha kana tace masu "anyi nasara?"..
  "Eh anyi" Daddy ya bata amsa, nan ya kwashe duk yanda sukayi ya fad'a mata harda labarin da Mama ta bashi..
   Ita kanta Mummy sai da tayi kuka "tabbas Nana na buk'atar kulawa kuma aura mata Sameer kad'ai ne zai sa ta samu kulawarmu sosai"..
   "Nifa na fara tsoro kar mu aura mashi yarinyar mutane ya cigaba da wulak'anta ta" haba Umma bai kamata ki fad'i haka ba ki bisu da adu'a kawai in shaa Allah Sameer sai ya baki mamaki..
   Tab'e baki tayi tace "ko kuma ya baki kunya ba". Dariya Mummy tayi tace "ba zai ban ba in shaa Allah..."

  Waya Daddy ya jawo dialing number yayi sai data kusa tsinkewa kana aka d'auka. "Kazo ina parlour" abinda yace kenan ya kashe wayarshi...
  Sai da ya kwashi kusan minti talatin kafin yazo dan ran Umma har ya fara b'aci amma hakanan ta daure..
   Sallama yayi ciki ciki wanda na kusa dashima ba lallai bane ya jiyo...
   Zama yayi kusa da Mummy fuskar nan ba annuri yace "Daddy gani.."
   Shiru ya biyo baya na kusan minti talatin dan zullumin yi mashi magana..
  Umma ce tayi k'arfin halin magana, mungama maganar aurenka dan mun gaji da ganinka haka dan haka munyanke shawara zamu had'aka aure da ra'ayinmu kuma wannan umurni ne ba shawaraba...
   Tun kafin ta ida magana ya mik'e "What?" Aure? Umma kinsan mi kike fad'a wallahi ba zai yuba, ba wanda zai man aure yanzu akanmi za'a man aure? Kuma ma wai zab'inku, Sakin baki sukayi suna kallonshi...
  Fad'awa yayi kan Mummy yana kuka, tureshi tayi tace "tashi kaban wuri da hankalinka da tunaninka kake d'aga ma mahaifiyarka murya haka? Wallahi nayi danasanin irin san dana nuna maka, kuma bari kaji magana ta k'arshe auren nan babu fashi idan kuma ka bijire kasa aranka zan bar maka duniyar gaba d'aya dan nasan ciwo na farat d'aya zai man, dan haka sai ka zab'a ko rayuwata ko mutuwata.."
No Mummy ba zaki mutu ba idan kin mutu na zauna dawa, indai hakane naji na amince zan auri wadda kukeso. Kallonshi tayi har yanzu fuskarta d'aure tace "jeka ba mahaifiyarka hak'uri" ba musu ya matsa wajen Umma yace "Umma kiyi hak'uri ki gafarce ni.."
  Shafa kanshi tayi tace "bakomai Sameer, ka amshi zab'inmu  baza kayi danasani ba..
   Shi Daddy ma d'an kallo ya zama ji yake dama ba'a kawo wannan shawaran ba coz ba isan ganin Sameer cikin damuwa..
   Nan dai suka dinga mashi nasiha..
  Jinsu kawai yake dan ya d'auki alwashin ko wacece za'a aura mashi sai tayi danasanin aurenshi, dan sai ya wulak'anta ta ya k'ask'anta ta ya maida ita abun tausayi...

FOUR STARS🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245