RASHIN GATA 56-60

🌼🌼 *RASHIN GATA* 🌼🌼

         *TANBARI*
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

```NAH```
*FOUR STAR*🌟🌟🌟🌟

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HUSAYN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```

  56-60

   Family Support Hospital suka nufa da ita dake garin yobe, suna isa nurses suka amsheta sukayi labour room da ita duk abinda ake buk'ata na haihuwa sai da Sufyan ya sayeshi nan cikin asibitin..
   Awarta d'aya da shiga Allah ya sauketa lafiya, likita yafito ya gaya masu Allah ya sauketa lafiya tasamu Baby girl zo kaga murna wajen matar Sufyan...
   D'akin hutawa aka mai data shiga sukayi da sallama, zaune suka isketa ta rungume d'iyarta tana ta kuka mai tsuma jiki, k'arasawa sukayi gabon gadon Matar Sufyan ta karb'i Babyn daga hannunta, tsayuwa Sufyan ya gyara yace "Amina yanzu ba lokacin kuka baneba adua zakiyi" girgiza kanta takeyi tana kuka tace "Sufyan dole inyi kuka kaico na da wannan rayuwar da nashiga nida d'iyata yanzu mi zance mata? Idan ta girma ta tambayi waye babanta?" Hak'uri zakiyi komai yayi farko yana da k'arshe, mik'ama Sufyan babyn tayi ta cigaba da lallashin Amina da kyar suka samu tayi shiru...
   "Wane suna zaki saka mata?" Sufyan ya tambaya, "Nana Khadeeja sunan mahaifiyata" ta bashi amsa, hud'uba ya mata da Nana Khadeeja. Ranan aka sallamesu saboda daga jaririyar hai mai jegon suna cikin k'oshin lafiya...

   Sati na zaga yowa akayi suna bawani taro tayi ba dan tace babu wanda zata gayyata duk abinda ake na haihuwa tun daga kan rago zuwa kayan sawa babu wanda Sufyan baima Nana da Amina ba, kuka kam Amina tayishi kamar zata cire ranta tagaji ta dan gana..
   Bayan suna da sati guda Sufyan sukazo da matarshi dan yima Amina sallama an mashi transfer an maidashi kaduna ba k'aramin damuwa Amina tayi ba amma ta hak'ura da zasu tafi ya kawo kud'i masu yawa cikin jikka ya bata yace "Amina wannan kud'in na baki sune saboda Nana ki nemi sana'a  kiyi inasan kiba Nana Ilimi ingantacce inaji a jikina duniya zatayi Alfahari da ita" amsar kud'in tayi tana kuka ita kanta batasan iya yawan kud'in ba, haka suka mata sallama suka tafi..
   Tun daga sannan tafara tunanin wace sana'a zatayi daga nan ta yanke hukuncin sayar da Lacess atamfofi da materials jikka da takalmi da taimakon wani makwabcinsu ta fara wannan sana'ar Allah kuma yasa mata hannu cikin sana'arta..

   Haka rayuwa ta dinga tafiyama Amina da dad'i ba dad'i saidai abun farin cikin yanda Allah yasa mata hannu cikin sana'arta, tana sana'arta tana renon Nana data fara wayau...
   Lokacin da Nana ta isa shiga skul ta sakata a Leader Private school, ta kuma sakata Islamiyya dake nan kusa dasu Allah yayima Nana kwakwalwa saboda yarinyar duk abinda aka gaya mata ba'a maimaitawa zamu iya cewa irinsu Nana sune ake cema gifted Nana bata san wata matsala ta rayuwa ba daidai gwargwado Amina tana k'ok'ari kanta saidai matsala  d'aya da idan ta fita waje yara basa barinta sun dinga zaginta da dukanta wai ba asan babanta ba kullum idan tafita da kuka take dawowa tun abun na damun Amina har yakai da ta hak'ura daga k'arshe ma ta hana Nana fita in ba makaranta zata ba ko aikenta batayi..

   Lokacin data gama primary school kyanta yafara fitowa alamomin yanmatanci suka fara fito mata, kullum Amina cikin Nasiha take mata akan ta dinga kula da kanta da tarbiyarta..
   Watarana ta dawo daga makaranta dayake tana ss3 gab suke da zana WAEC wani ya dinga binta yana mata magana shiru tayi ta kyaleshi gabanta ya sha yace "ke shegiya daga kinsamu ana maki magana? In bamani ba waye zai kula shegiya?" Kuka ta dingayi tabar wurin da gudu ta nufi gida, tana shiga bako sallama ta fad'a kan Amina tana kuka d'agota Amina tayi tace "minene?" Kallonta tayi tace "wai Mama dagaske ni shegiyace?" Bayau Mama tafarajin wannan tambayar ba..
    Hawaye ta share mata tace "kina da uba kamar kowa" yana ina? Tambayar da ta mata kenan, hawaye Mama ta goge tace "yanzu zakiji komai....." Nan ta kwashe komai ta gayama Nana..

   Kuka Nana keyi tace "Mama miyasa Baba zai maki haka? Nayi danasanin zuwa danayi matsayin d'iyarshi" kidaina fad'ar haka Nana ki d'auka k'addararmu ce haka..
   Tabbas Mama zakiyi Alfahari dani kamar yanda Uncle Sufyan ya fad'a maki in shaa Allah sai nazama abun kwatance. Hannu ta d'aga sama tace "Ya Allah kajaman da ran mahaifiyata sai tazama abin kwatance a gari Allah kacikaman burina" Amin Nana..
   Hawayen da Mama keyi ta share matasu tace "Mama kin kusayin dariya " murmushi tayi tace "Allah ya nuna mana" Mama mikikeso na karanta idan na gama secondary school? Murmushi Mama tayi tace "so nake ki karanta Medicine saboda Al'umma tayi Alfahari dake" in shaa Allah Mama zan cika maki burinki...

   Sun gama WAEC da wata uku result d'insu ya fito Nana itace best student a school d'insu kyauta ta amshe ta har tagaji Mama dataji Nana ce best student kuka ta dingayi da kyar Nana ta lallasheta...
    A lokacin tayi saukar alqur'ani ga litattafai tasani daidai gwargwado.
  
   Jamb tayi inda taci 250 abun bai ba Mama mamaki ba dan a kwakwalwar Nana sama da hakama zata iya ci..
   Admission ta nema a Yobe state University batasha wahalaba suka bata kuma ta samu course d'in datakeso wato Medicine...
   Sanye take da abaya pink ta saka scarfs shima pink, kayan data saka su suka saka mukaga k'irarta..
   Doguwace, irin matan da ake kira coca cola shape, farace sosai dan zaka rantse da Allah balaraba ce gabanta cike yake da dukiyar fulani kuma tsaye suke dariyar da tayi yasa fararen hak'oranta suka bayyana har saida kumatunta suka lotsa, zamu iya cema masu karatu Nana ta had'u ta ko ina..
   Fitowa tayi ta samu Mama tace "Mama zan tafi makaranta" kallonta Mama tayi tace "ina zuwa" ta mik'e ta shiga d'aki jim kad'an ta fito da niqab tace gashi ki d'aura, kallon Mama tayi tace "miyasa?" Murmushi tayi tace "saboda inasan ki b'oye kanki daga sharrin mazan zamani" ba musu ta karb'a ta d'aura ta nufi makaranta..

   Haka Nana tafara karatunta cikin sa'a dan bata tab'a samun matsala ba kuma bata da k'awa zan iya cemaka duk wanda yake makarantar nan babu wanda bai san sunan Nana ba saidai basu tab'a ganin fuskar ta ba..
   Cikin ikon Allah ta gama karatunta lafiya batare da tasamu matsala ba tana gamawa ta samu Aiki a General hospital dake Yobe..
   Albashinta na farko ta biyama Mama makka kuka Mama tashashi da kyar Nana tasamu tayi shiru..
   Haka ta cigaba da Aikinta cikin amana bata tab'a samun matsala ba

   Haka suka cigaba da rayuwa cikin k'oshin lafiya duk abinda Nana tasamu Mama burinta ya koma kan Mama watarana Mama har shigewa d'aki take tayi kuka saboda yanda Allah ya mata sakayya yabata d'iya kamar namiji..
  Haka suka cigaba da rayuwa damaturu har lokacin da aka mata transfer aka maidata Abuja...

   Cigaban Labari..

Four stars🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245