RASHIN GATA 16-20

🌼🌼 *RASHIN GATA*🌼🌼

*TANBARIN*
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

```NAH```
*FOUR STARS*⭐⭐⭐⭐

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI```
```(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HUSAYN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRAH BUKAR```
```(CUTIE ZARAH)```

16-20

   Cikin ikon Allah suka isa Abuja, suna kai tasha wayanta tafara ruri tana neman taimako d'agawa tayi da sallama bansan mi aka ce ba tace "tashar Jabi zamu" ok sai kazo ta kashe wayarta...
   Juyowa tayi ta k'alli Mama tace "wanda zai d'aukemu daga tasha ne ya kira" murmushi Mama tayi tace "bakomai".... Allah yakawosa Lafiya.
   Suna isa tasha daidai lokacin da wanda yazo d'aukarsu ya iso, motarshi suka fad'a sukayi maitama, tafiyar minti talatin ta kaisu maitama. Panama strt ministers hill taga an rubuta batasan sanda hawaye suka gangaro mata ba, da sauri ta gogesu dan kar Mama tagani...

   Gaban wani black gate ya tsaya, horn yayi da sauri maigadi ya bud'e get d'in cinna kan motar yayi cikin haraban gidan parking space ya samu yayi parking, fitowa yayi suma suka fito, kayansu ya kwaso masu yayi cikin gida dasu..
   Gaba yayi suna biye dashi a baya gaban wani k'ofa ya tsaya ya bud'e suka shiga, falo suka isa madaidaici, aje kayan hannunshi yayi ya juyo ya kalleta "yace"  "Hajia nan ne gidanki ya mik'a mata key ita kuma motar da nakawo ku itama takice yana mik'a mata key d'in motar" k'arba tayi ta mashi godia bakomai abinda yace kenan yamasu bankwana ya wuce...
   Kan Mama ta fad'a tana kuka d'agota Mama tayi tace "ba kuka zakiyi ba Nana godia zakima Allah" d'aga hannunta tayi sama tana ma Allah godia takai mintin ashirin a haka daga k'arshe ta shafa ta kalli Mama tace "Mama muzagaya muga yanda gidan yake" ba musu Maama ta mik'e...

    Plat ne gidan daidai zaman mace d'aya parlour d'ayane sai 2 bed room sai kitchen sai store kowane d'aki yana da toilet sai dainning area sai corridor , fita sukayi waje parking space suka nufa inda aka mata parking motarta mai k'irar matrix black parking space d'in zaka iya parking mota uku..
   Cikin falo suka dawo suna yaba kyan gidan, kallon Mama tayi tace "Mama ko a mafarki banyi tunanin kai matsayin da nake yanzu ba" dariya Mama tayi tace "ai Allah kenan mai yanda yaso da bawanshi...
                     ★★★★★★★
   Tsaye take gaban dressing mirror tana  d'aura nik'ab d'inta fitowa tayi cikin shiri, a parlour ta samu Mama tana kalaci zama tayi kusa da Mama ta gaidata amsawa Mama tayi cikin sakin fuska tace "Nana harkin shirya?" Eh Mama ta bata amsa, toh kiyi sauri kiyi kalacin karki makara, toh ta amsa mata daidai tana zuba dankali a plate..
    Tana gama cin abinci ta mik'e tace "Mama zan tafi"..
   Kallonta Mama tayi ta mata adua'r neman tsari daga mutum ko Aljan tace "Allah ya kiyaye hanya Nana Allah ya kaiki lafiya ya maidoman ke lafiya." Amsawa tayi da Amin Mamanah ta juya ta tafi...

   Tana kaiwa bakin k'ofa Mama ta kira sunanta, amsawa tayi da "Naam"
   Juyowa tayi ta kalleta Mama tace "kinsan Asibitin?" Ah ah tace, toh yanzu ya zakiyi?..
   Murmushi tayi tace "karki damu Mamana zan duba Map in shaa Allah zan gane kinsan yanzu cigaba yazo" hakane Nanana Allah ya kiyaye, ta amsa da Amin ta nufi hanyar fita...

   Da taimakon Map Nana ta isa *NIZAMIYE HOSPITAL* tana shiga ta samu wuri tayi parking fitowa tayi daga cikin motarta ta nufi cikin asibitin, wata nurse ce ta had'u da ita sannu tace mata amsata nurse d'in tayi ba yabo ba fallasa. D'auke niqab d'in kanta tayi tace mata "My name is Doctor Khadeeja" da sauri nurse d'in ta karb'i kayan hannunta tace "ur welcum doctor" dama kuma mun jima muna jiran isowarki, muje na kaiki office d'in Docto Ammar..
   Tafe take tana biye da ita har suka isa Office d'in doctor Ammar knocking tayi ya basu izinin shiga, tana shiga ta gaidashi tace "dama Doctor Khadeeja ce" da sauri ya mik'e yace "sannu da zuwa Doctor" amsa mashi tayi da yauwa cikin niqab..
   Zaki iya tafiya yacema nurse, aje kayan Dr Khadeeja tayi ta juya ta fita tana mamakin miyasa Dr take saka niqab...
   Dr sannu da zuwa, yauwa ta amsa mashi dashi  yace "muje nakaiki office d'inki" ba musu ta tashi tabi bayanshi, office d'in dake kusa danashi suka shiga wuri ya matsa mata ta wuce yace "Dr nan ne sabon office d'inki, hope zamuyi aiki dake da amana"..
   Dariya tayi tace "in shaa Allah doctor Ammar na gode" bakomai doctor yana fad'an haka yawuce yakoma office d'inshi..
   Kallon office d'in tayi tabbas yamata kyau sosai komai na buk'ata akwaishi, zama tayi tafara duba files d'in dake gaban tabur d'inta...

Four stars⭐⭐⭐⭐

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245