RASHIN GATA 111-115

🌼🌼RASHIN GATA🌼🌼

```NAGARTA WRIYER'S ASSOCIATION (NWA)```

*NAH*
```FOUR STAR'S```✨✨✨✨

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI SHEHU
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HASSAN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```

This page is dedicated to our caring and Luvly mummys
  *SDY JEEGAL, FEENAT JA'AFAR, MAMAN HANEEF, MARUBUTAN INA DA BURI*
    &
*SWEETHEART (MY CHERRY MIEMIE BEE) marubuciyar YGC*  may almighty Allah bless and reward them abundantly (Ameen)...
```FOUR STAR'S✨ NA ALFAHAREE DAKU```

111-112

   Tea ne da Dankali da Kwai sai k'amshi ketashi, "Allah sarki Umma sannu da aiki" Abinda Nana tace kenan murmushi tayi tace "yauwa Nana, Allah yasa abinci yayi miki dadi?" Haba Umma Yayi dadi sosai wallahi..
    Sai da ta cika cikinta sosai, kana ta mik'e Umma bara naduba jikin Mummy to muje ko nima inason ta tashi taci abinci dan tun jiya rabonta da abinci, ido waje Nana tayi tana kallon Umma, Umma dole Ana bata abinci akai akai fah, eh tun safe naje naga bata  tashiba kuma kince tana samun barci sosai to shiyasa ban tashe taba..
  "Hakane fa Umma" abinda Nana tace kenan, Umma ina abincin Nata yanzu? Jeki dubata, bara ni kuma naje na had'a mata koh? "Eh Umma bara naje" Nana tace Sana ta wuce part din Mummy.
  Yau bata wani jimaba saboda wayar data samu daga Dr Ammar saboda wani operation dazatayi, hakan yasata yiwa su Mummy sallama, tabar gidan cikin sauri.
  Yau ma kamar jiya Sameer sai gab da la'asar yabar gidan, cike da farin ciki sai Yau ma ya k'ara sanin irin kirkin da Maman Nana take dashi bakamar banzar yarta ba. D'iyarta ba ya ambata a cikin ransa...

  Sai 6:30 tadawo gida tagaji likis, hakan yasa tana zuwa gida direct bedroom tayi sai data farayin wanka sanan ta d'auro alwala ta gabatar da sallah magariba "Nana Yau ko neman Mama ba'ayi ne?" Mamace tace mata haka Allah Mamana nagaji ne kuma lokacin dana shigo naga kina kitchen kawai direct d'aki nayo..
  Ayya sannu kinji ya aikin yasu Mummy? Lafiya kalau Mama, Yau ma ba'a can na wuni ba ina asibiti nayima wata mata operation ne, ayya anyi nasara koh? Eh Mama anyi nasara aman fah baki gani ba wallahi tasha wuya, "Allah sarki Allah yaba lafiya" Mama tafada tana shafan kan Nana...
   Yau fah Sameer ya kuma zuwa gasheni, gaskiya yaron yanada kirki ga hankali, kece dai Nana baki fahimci sameer ba har gashi bakwa shiri nikam yaro yayimin....

   Sakin baki Nana tayi ta zaro ido tana kallon Mamanta, Mama kikace mai? Sameer yazo gidan nan?
   Eh yazo ya gaishe nine, "tab wih dasake" Nana ta ambata, baki sake Mama ke kallon Nana kinci gidanku da sake kamar ya?
   Turo baki tayi tace "wallahi Mama bazai dinga zuwar mana gida ba, don nasan ba don Allah yake zuwa ba shi kad'ai yasan mai ke kawo sa gidan, kuma wallahi warnning d'insa zanyi kada yakoma zuwar mana gida..."
   Mama zubawa yarta ido tayi dan ita a iyya sanita Nana batada fada, yariyace mai hak'uri da kawaici..

  Haba Nana kirinka hak'uri mana kizama mai juriya, abinda yasa nace haka shine kowace mace da kika gani hak'uri take, kuma dole Allah ya jaraba bawansa saboda ganin k'arfin imaninsa domin samun aljannarka, dan haka kema kizama mai hak'uri duk abinda Sameer zai miki nad'an lokaci ne, saboda wata rana kina gidan mijinki bai ganki ba bare ya maki ko kuma ince kuyima juna...
   Kuka Nana tasawa Mamanta saboda ita babu abinda ta tsana irin taga ranar da za'ace yau bata tare da Mamanta, hakan yasa hankali Mama ya tashi ai'nun dakyar ta lallasheta..

*2 days*

   Gani Sameer yabar gidan kuma tasan ba lallai bane ya dawo yanzu, hakan ya sata cire nikaf d'inta tare da zare hijab d'in jikinta..
A  hankali take cin jollof d'in da Umma ta had'a mata wadda taji kayan lambu da kifi, saboda yanzu Umma ta ta hanata break gida sai nan take breakfast tanaci kuma Umma na bata labarin yarintar Sameer, tanata dariya harda rik'e ciki, hakan take jinta yau cikin farin ciki ko dan itama ta tsara wani babban game akan Sameer, fatan ta kuma Allah yasa ita ce zatayi nasara...

  Har yakai ga motarshi zai Fara driven, yamanta yabar wani file nawani programs dazaiba barrister hareex, hakan yasa shi zare key d'in motar yafito domin ya d'auki file d'in cikin nutsuwa yake tafiyar har yakai ga palo, cak yatsaya komai nata mai burgewa ne ga smile d'in da yake dad'a rikirkita dan Adam, dariyar da take wani irrin masiffen  kyau take k'ara Mata..
   komai na jinkinsa ya daina amfani tsabar wani shokin daya kamasa, innalillahi wa'innah ilaihir raji'un yake ambata baya fatan abinda yagani ya zama gaskiya, sake murza idonsa yayi tabbas ba mafarki yakeba zahiri itace, ita ce mafarkinsa, burinsa, rayuwarsa gaba d'aya, baya fatan takasanei itace Nana, saboda I hate Nana so much nan danan zuciyarsa tafara bugawa.

   Da sauri yajuya ya koma motarsa newspaper dake ajiye a sit d'in mai zaman banza ya d'auka ya fara karantawa, ko zaiji daman abinda yakeji a cikin ransa..
    ajiye newspaper yayi ya dafe kanshi yana cije pink lips d'insa, kwata-kwata yarasa nutsuwarsa,Nana ta dagulamasa lissafi...
   Tunanin inda yasan face d'in yake, da k'arfi ya bugi sitiyarin motarshi "tabbas ita ce Nana saboda ban manta sanda nasa aka koreta naga fuskanta tana kuka" abinda yace kenan....
   i hate you Nana na tsaneki na tsani komi naki, na tsani duk mai sanki. amma banda Mamanki saboda i so much love your Mummy shez very nice Woman..
   Haka ya dinga surutu kamar mahaukaci yana kuka...

  Tun lokacin da nana taga wucewar sameer ta tabbatar yariga yaganta kuma yagane tah, dan haka aikin gama ya gama kuma babu sauran boye boye. Hakan yasa binsa a baya, Ji yayi an bushe da dariya da sauri ya d'ago, ganinta yayi tsaye ta rik'e k'ugu daga ita sai dankwali..
  D'aure fuska tayi tace "d'an burni yadai? tun ba'aje ko ina ba ka fara sarewa? Kuma gashi game din yanxu yafara, daga ganin halitar mace sai ka rud'e haka to nan dai anfi k'arfinka, naji kana wasu sabbatu wai you hate me hmmm, "k'arya kake Sameer" babu tsanata a idon ka tabbas ka tsani DR Nana wadda take yawo da nik'af amma baka tsani ta tsaye kusa da kai ba dan gashi har kana kuka.. sai dai abinda baka sani bane ni Dr Nana wallahi na tsaneka na tsanka na tsani komai naka, amma inasan iyayenka cz mutanen kirki ne..."
   Cikin zafin k'una ya fito d'aga hannu yayi zai mareta "kada ka saki ka mareta" muryar Umma ya jiyo tana mashi kashedi, itako tuni ta rintse ido tana jiran saukar mari...
   "Zo nan Nana" abinda Umma tace kenan, harararshi tayi ta juya ta bi Umma...
  K'asa ya zauna ya dafe kanshi yana kuka...

FOUR STAR'S ✨✨✨✨

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245