RASHIN GATA 61-65

🌼🌼 *RASHIN GATA*🌼🌼

        *TANBARIN*
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

```NAH```
  *FOUR STARS*⭐⭐🌟🌟

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAH```
  ```STYLISH BCH```

*ZAINAB Y HUSAYN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR```
(```CUTE ZARAH)```

Duniya juyi, rayuwa sauyi, yanayi mai tafiya da zamani, zamani ikon Allah, D`an Adam kayan Allah.

61-65

    Hmm wallahi Dr Nana kike ko whatever, u will pay what u did to me kamar ni kisaka Umma ta mareni never har ya shiga mota sai kawai ya fita da sauri office na Dr Ammar yaje knocking yayi baijira ambashi permission ba yasa kai kawai...
   A'a Oga Sameer ne? sannu shigo mana, hannu ya mika masa musabaha sukai anan ya zauna kan kujeran da ke kallon ta Dr d'in, Dr ina wadda ta duba Momy na? oh Dr Nana tad'auki hutu amma tana k'okarin shigowa watak'il kaganta yanzu ma, hope jikin Momy yai sauk'i? "Yeah da sauk'i" yabashi amsa a tak'aice daga haka bai k'ara cewa komai ba saima karkad'a k'afa da yake yana jin wak'ar Shiriya goshal.
   Welcome Dr ya kike ya jikin Mama? lafiya lau Dorcas jiki yayi sauk'i sosai, murmushi Dorcas tayi tace "Thanks God" gata nan ma naji suna magana da Dorcas, u can go n see her.

    Kafad'a ya d'aga irin bai damu ba sannan ya sakai ya fice, office nata yai direct batare daya jira anmasa izini ba.
   Boom ya tura k'ofar da sauri Nana ta d'auki nik'ab nata wanda ta cire ta maida juyowa tai afusace zatayi magana sai kawai idon ta ya sark'e dana Sameer wand ya zuba mata idanu yana mata kallon raini da k'ask'anci.
    Cikin tak'ama ya fara tako k'afar sa har yakawo gaban ta, Ita kam babu abinda take illa kallon sa har yakawo gaban ta, hannun sa ya mik'a saman fuskarta yana k'ok'arin cire niqab dake fuskar ta, saidai kash kafin yakai harta saka abin ma'aunin su na likitoci ta jefamasa a hannun kana ta d'aga d'an yatasan ta fuskar sa tai nuni da shi tace "Sameer kake ko wa? meye haka? rashin hankali ko yarinta? zaka shigo mun office without asking my permission, who dere u are?
Kul kashiga hankalin ka, me namaka idan wani abu kake so jeka can wajen wani ni I'm safe yau bana aiki bare kanemi cimun fuska"..

   "Keeee! ni zaki gayama magana haka daga shigowa wajenki nizaki zaga?, talaka k'azama kamarki kicemun banda hankali abinda ba'a tab'a gayaman ba tun childhood d'ina bare da girma na.." magana yake yana huci tsabar b'acin rai fuskar sa harwani ja tayi, baitab'a cin karo da mutum mara kirki ba like Dr Nana tabbas sai ya guntule mata aikin datake tak'ama da shi.
   Kallon ta yayi yama kasa magana tsabar haushi, itama kallon sa take tana hararan sa, kwafa yai ya buga mata harara ya juya sai da yakai bakin k'ofa ya juyo ya kalleta yace "l'll teach you a lesson" yana fad'ar haka ya fita k'ofar ma sai data sami rabon ta dan bugata yai giif.
    Hmm wannan mutumin mena masa? Meya keso dani ne, haka ake rayuwa shikenan talaka bashida 'yancin kansa? Talaka bazaiyi abinda yake so ba, yacimun mutunci yaci na uwata to mai yayi saura? Kuka tasaka tana tuna rayuwar da tabaro can ma,
ashe nan ma akwai wanda zai tsaneta?.
     Shikam kodaya fita cikin mota ya nufa kifa kansa yayi bisa sitiyari d'agowa yayi yace " lallai wannan yarinyar sai na dasa mata bak'in ciki wanda sai ya kaita lahira" haka ya shafe wajen 30 Minutes yana tunani sai daga can yayi wani irin ihu yes haka zanyi murmushin mugunta yayi yace "Nana hmmm zakisan kin tab'a Sameer"...
 
   Buga sitiyarin motar yake yana wani shu'umin smile yasamo hanyar dazai ruguzawa Nana farin ciki, cikin sauri ya yiwa motar key yafice, can Nana kukan ta tasha sannan ta d'ebi kayanta ta fice bazata iya aikin ba ai ba'a ce dole tazo yau ba ita tasaka kanta amma daga yau bazan k'ara zuwa ba harsai hutu na ya k'are..
    Da sauri ta fito ba tabi takan kowa ba tabi lipter tai k'asa, motar ta tahau sai gida kodata k'arasa bata shiga ba sai data tabbatar ta goge fuskar ta sosai saboda Mama.
*****
    A can kuma Sameer abokin sa yaima waya, yana d'aula yace "kai maza yane?" Lafiya lau MB wani taimako zakamun dan Allah nasan Abban ku shine chief na health duka so ba wani abu mai zafi zaka mun ba ina sone dan Allah inaso a kori wata Doctor..
   Ido ya zaro kamar yana ganinshi yace "Sameer like how? kasan Abba kam bazaiyi ba, amma zan gwada naga wani hospital ne?" NIZAMIYE HOSPITAL nefa bawani asibiti bane ba..

  Girgiza kanshi yakeyi yace "Impossible friend ai wannan asibitin duk wanda kaga an d'auka yasan mi yakeyi kaga kuwa da wuya a koresa, coz federal ta shiga ciki badan haka bama masu visiting na asibitin sai sun kashe kud'i sosai ai kaf Abuja wannan hospital d'in is the best, private ne amma da hannun federal ciki kaga kuwa masu asibitin baza suzo ba ace ana kore masu Doctors inajin hausawan cikin sa basufi 5 ba, wani Ammar dai shine oga hakan bamai yuwa bane amma kasamo wata idea daban abokina."..
   Huup ! ba mafita, yadda na d'auki asibitin ashe ba haka yake ba amma da sannu sai ta raina kant dariya yayi yace "wai wace haka ne? kaida baka shiga shirgin mata ko tasamu ne?" mts Allah ya kiyaye aini still now I'm baby kaga ba ruwa na da shaanin mata dariya yayi yace "to Babyn Mummy" dariya yayi shima yace "bye call u later idan da wani taimakon..." Yana fad'ar haka ya datse kiran..
     Sitiyarin ya buga da hannunshi yace "planA bai yiba zan gwada PlanB Nana saikin raina kanki sai kinsan waye Sameer garin Abuja.." Fizgar motarshi yayi da gudu...

 
Four stars🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245