RASHIN GATA 51-55

🌼🌼 *RASHIN GATA*🌼🌼

        *TANBARIN*
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

```NAH```
*FOUR STARS*🌟🌟🌟🌟

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR_FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI```
```(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HUSAYN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR```
```(CUTE ZARAH)```

51-55

   Tayi kuka har idanuwanta suka kumbura, tunanin inda zata ga mijinta takeyi, wani abokinshi mai suna Sufyan ya fad'o mata tashi tayi ta nufi gidan Sufyan ko ta samu wani bayani dangane da mijinta..
   Tafe take duk ta gaji ga ba ko sisi a hannunta ga k'aton ciki tana tafiya tana hutawa har Allah yasa ta iso gidan Sufyan..
  A k'ofar gida ta had'u da Sufyan, hangota yayi ya taso da sauri ya iso wajenta, "Amina lafiya kika fito baki ga halin da kike ciki ba?" murmushi k'arfin hali tayi tace "Sufyan fitar ta dole ce" hakane mu shiga daga ciki, ba musu tabi bayanshi suka shiga cikin gida...

   Da sallama suka shiga gidan amsa masu tayi kallonshi tayi tace "yallab'ai mantuwa kayi?" Ah ah ba mantuwa nayi ba ya bata amsa, tare nake da Amina, da sauri ta tashi ta kamo Amina tace "Amina kece ke tafe haka ga ciki kuma na tabbata watan haihuwarki ya tsaya" hmmm wlh nima na fad'i haka toh tace "dole ne yasa ta fito" tashi tayi ta kawo mata lemu ta aje gabanta..
   Gaisawa sukayi cikin sakin fuska, lemun da ka aje mata ta d'an kurb'a ta aje cup d'in. Kallon Sufyan Amina tayi tace "magana nakeso nayi dakai kuma nasan duk abinda zan tambayeka kasani ka dubi girman Allah ka gayaman gaskiyar abinda na tambayeka" murmushi yayi yace "in shaa Allah"...

   Zama ta gyara tace "dama game da abokinka ne nasan kasan komai kuma duk abinda yakeyi yana shawara dakai shine nakeso naji gaskiyar abinda yafaru dan zuciyata bata aminta da b'atanshi haka kawai ba"...
   Zama ya gyara yace "tabbas ranar wanka ba'a b'oye cibi" hakane suka bashi amsa ita da matarshi..
   Kamar yanda kika sani duk garin nan Aliyu baida aboki sama dani, lokacin da kika bashi dukiyarki yazo ya sameni ya gayaman, nan na zaunar dashi na mashi nasiha akan yaji tsoron Allah daya rik'e maki dukiya da amana, yakuma tabbatar mani da in shaa Allah zai rik'e dukiyarki ba tare daya ci amanarki ba...
   Haka tafiya tayi tafiya yana kula da dukiyarki ni kaina shaida ne, kwatsam ranan yazo mani da labarin zai k'ara aure, ban hanashi ba amma nace sai anyi bincike..
   Na kumayi bincike akan yarinyar, sai dai abinda naji kan yarinyar ya d'agaman hankali saboda ba d'iyar arzik'i bace ba infact ba gidan iyayenta take zama ba, na sameshi na mashi bayani yakuma gamsu kuma ya tabbatar man da yafasa aurenta..

   Bayan wasu yan kwanaki ya kirani yace man shi yana airport zaiyi tafiya kuma yanajin tafiyar bazai dawo ba, nace mashi saboda mi? Yace ban gayama ba nafayi aure bansan sanda natashi zaune ba, yace nasan zakayi mamaki ko? To ba abin mamaki bane ba kai a ganinka zaka iya hanani auren Bilkisu? Hmm wlh mai iya hanani aurenta ban ganshi ba kuma a yanzu haka muna airport zamu bar k'asar..
   Zuface ta karyoman da kyar na samu miyau abakina nace mashi ina fatan ka ajema matarka dukiyarta? Wata shu'umar dariya ya saki yace "ai wannan dukiyar tafita hannunta nida amaryata zamu cita, saidai idan ubanta zai dawo daga lahira ya sake tara mata wata dukiyar amma wannan bata dawowa abinda baka sani ba shine duk abinda kasan ta mallaka yanzu haka duk ya koma nawa tun daga kan gidaje da filaye duk sun zama nawa, yana gama fad'ar haka ya kashe wayarshi...
  Wayar na dinga kira amma najita kashe, bak'aramar damuwa na shiga ba saboda nasan ba yin kanshi baneba shu'umar matar da ya aura ce zata iya komai akan kud'i toh kinji abinda yafaru tabbas mijinki ba b'acewa yayi ba...

   Kuka ne yaci k'arfinta tace "Aliyu ka cuceni ka yaudareni yanzu mizance ma d'iyarka idan tazo duniya? Ashe dama dad'in baki  kakeman da kake cewa Amina Allah yaban kud'i kiji dad'i, Amina idan na samu kud'i sai kinfi kowace mace a duniya burina in kyautata maki Amina in maki halacci yanda kikaman ashe duk dad'in baki ne kaico na ni Amina yanzu na zamo ban da kowa ba miji ba iyaye ba d'an uwa" kuka take sosai kamar ranta zai fita..
   Lallashinta suka dingayi da kyar suka samu tayi shiru, "kiyi hak'uri Amina ki d'auka k'addararki ce haka" matar Sufyan ce ke fad'a mata haka..
   Hawaye ta share tace "tabbas *JARABAWA TACE* haka na  (FEEDOH DEEDOH)  Allah kuma yabani ikon cinyeta"..
   Amin suka amsa mata, mik'ewa tayi zata tafi amma ta kasa d'aga k'afarta, jitayi cikinta ya murd'a ga wasu ruwa na biyo k'afarta, duk'awa tayi tace "wash cikina" da sauri matar Sufyan ta kamata, kallon Sufyan tayi tace "d'auko mota mu kaita asibiti haihuwa zatayi"..
   Dasauri ya fito da mota daga gareji da taimakon Matar Sufyan suka saka Amina mota suka nufi Asibiti da ita..

   Sudai four stars suna mata fatan Allah ya sauketa lafiya..

*four stars*🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245