RASHIN GATA 31-35

🌼🌼RASHIN GATA🌼🌼

*TANBARIN*
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

```NAH```
FOUR STARS🌟⭐🌟⭐
 
*ZAINAB Y HUSSEAIN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```SADIYA ABDALLAH```
```(STYLISH BICH)```

*ZAHRA BUKAR*
*(CUTIE ZARAH)*

```FEEDOH DEEDOH```
```(YAR_FICIKA)```

Page 31-35

  Parking yayi a inda aka tanada dan ajiye motar da sauri ya fito Kallon Dady yayi yace "akirasa a waya" ok yi sauri naga kamar tafara motsi tom Dady!
  Inalillah nayi mantuwa,  Doctor Feedoh ta fad'a wadda take ajiye glop kan teburin gaban Ammar, mantuwar mi? wallahi namanta totally banwa Dr Nana magana ba akan cewa za'a kawo patient ba kuma da alama..... k'arar wayar sa itace tahanashi k'arasa maganar da zaiyi. "Ya salaam sune.
  "Hello Dr gamu munzo muna wajen pharmacy, ok gani nan. Dr feedoh sunzo plz kitaimakan ki yiwa Dr Nana waya tazo kifara bata hak'uri tunda ba lokacin ta bane..
   Su kuma bara naje wajen su, kiramun Sageer yazo da gado plz, haka yai sauri ya fita wajen su domin ya shigo da su. Haka ya fita ganin su da sauri ya k'arasa gabansu tsugunawa yai Alhaji ina yini" lafiya Dr Ammar kaine sannu, eh nine in brief yai musu bayanin cewa yanzu Doctor d'in zatazo daidai nan aka kawo gado aka tafi da ita amenity aka kaita personal wajene a sama yake ta lipter aka shiga da ita da sauri sauran doctors d'in wasu India wasu chines haka suka shiga kafin Dr tazo, tunda sunga file na kelina hospital so sunga cutar tata.
  A can Feedoh sai kiranta take amma no responde tayi  kira har ba adadi amma shiru, hakan yasaka ta zuwa wajen Dr dan gayamasa.
  Chan ita kuma driving d'inta take cike da kwarewa wayarta a silent take bata lura da komai illa titin dake gaban ta da tunanin Maman ta.
   Ko data shiga gate en gidan Parker motar tai jakarta da wayar ta, ta d'akko sai wani files. Tun daga nesa take kiran Maman tata,
Mama gani na dawo, da gudu ta qarasa shiga gidan, turus tai ganin Mama da blanket a jikin ta tasaka hannu ta rik'e kanta duka biyun watsar da komai tai a k'asa ta tafi da sauri, Mama ! me zan gani Mama kanki ke ciwo Mama baki gayan ba why ? sai kuka rungumota jikinta tayi, fuskarta take shafawa fuskarta sharkaf da hawaye...
  Nana mene haka? zazzabi ne fa ba wani abu ba, kinzo zaki tayarmun da hankali sai kace cutar shekara nai tashi ni kiban wuri, dariya tasaki amma ga hawayen nan, Mama ban yadda ba jikin ki zafi fa Allah nidai kidenamun haka tashi naga meke damun ki, naqi nidai Allah saikin tashi maza dan har allura zan miki, a'a kinga banaso maganin dai zakiban amma allura banaso.
  Aikam sai anyi, haka tafara duba Maman ta wadda zazzabi ne kawai sai ciwon kai.
   Mts Dr wace ita wai waye ubanta ana kiranta amma taqi dagawa meta taka?, saboda ance ita d'aya ce impossible, magana yake yana huci, amm kayi haquri Alhaji bara naje dakaina na kirata, ok Ammar bara nazo muje tare naga dame take taqama Mom najin jiki amma ita tana gida tana hutawa batasan wazata duba ba?, batasan commissioner ta kudi zata duba ba, batasan cewa ni ba'a duban Mom a nigeria ba, batasan cewa ko a yanzu saina duba kalar tsaftar taba sannan zata tab'an min uwa ba, God forbids zanga wacece ita.
   Son bakasan uzirin taba, so baza kaje kacimata mutun ci ba, relax my son, Dady wani uzuri ga ma'aikaci a qasan mu fa take ci kana ma'aikaci ai bakada 'yancin kanka, "a ganin kaba, amma kowa yanada yancin kansa bafa a 15 century muke ba, so kowa yanada freedom nayin komai, beside kamanta private hospital muke not government hospital dan haka mune zamu lallab'ata cz zaman kanta takeyi ba k'ark'ashinmu take ba u ar still baby  Momin ka bata nunamaka rayuwa ba, duk ta san gartaka dayawa gaskiya," umma ce ke magana, kai Umma wane sangartawa kuma? Uhmm Dr yi tafiyarka ka kirata Allah yasa Lafiya dai, "ameen" yace sana yawuce.

Cikin minutes daba sufi 15 ba yak'arasa unguwarsu dake maitama, a bakin get din gidan ya tsaya yana hon, sai da aka dan jima kafin Mai gadi yabud'e k'ofa ya lek'o, ince dai lafiya dai ko yaro? Ina bayan gida lokacin dakaketa hon din, ayya babu komai baba, Dr khadija na nan Kuwa? Eh yanzu tashigo bajimawa, kiranta za'ayi? Eh kace Mata Dr Ammar ne, tam jira ina zuwa.

    Har bakin falon yaje yana kwada sallama, daga Can ciki yajeyo tana amsawa, a'a baba lafiya dai koh? Eh Yatah kinyi bak'o ne, wake nan? Tabuk'aci sani, eh wai koh Drrr Amash, Dr Ammar? Eh haka Kowa Yatah, damuwa k'arara a fuskarta, tace "kafada masa ina zuwa," cike da mamakin zuwan Dr Ammar gidan takoma d'aki, cikin ranta tana fad'in daga baro asibiti yanzu aman har anbiyo ni, sai da taja tsaki kafi ta saka hajib d'inta da nikaf. A bakin get din ta tardashi ya jingina, k'arasawa tayi kusa dashi, da murmushi a fuskarsa yace "sai kuma kika gani koh?" Eh Dr Allah yasa dai lafiya, eh to lafiya aman ba lafiyar ba gaskiya, yanzu dai zuwa zaki Mu komai asibiti Mara lafiya, aka kawo rai a hannu Allah kuma ke kad'ece kike dasani akan cutar *MOLD SICKNESS* Ayya Dr bazaka iya bata temako ba  zuwa gobe? Haba Dr Khadija nida ba bangaran nakaranta ba, ke kadai kike dasani akan cutar pls kizo muje, Dr Mama ce bata da Lafiya shine banason natafi nabarta, pls Dr taimako zaki, ae nasan kin duba Mama yanzu kafin kidawo tasamu lafiya insha Allah, Allah ya yarda to, bara nad'auko key d'in motar ok babu damuwa, bata wani jumaba tafito suka dauki hanyar asibitin motar Dr Ammar na gaba, ta Dr Khadija nabinsa.
   Ran Sameer yagama b'aci, ganin halin da Momynsa take ciki gashi har yanzu Dr Ammar bai dawo ba, kuma sai kiransa yake network yahana kiran zuwa.

Four star🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245