RASHIN GATA 71-75

🌼🌼 *RASHIN GATA* 🌼🌼

         *TANBARI*
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

```NAH```
*FOUR STAR*🌟🌟🌟🌟

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HUSAYN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```

  71-75

    Yana fita ta d'ora kanta bisa tebur d'in dake gabanta, d'agowa tayi da hawaye "minama yaron nan? Miyasa yake shiga harkana? Miyasa ya tsaneni haka dayawa?" Kanta ta jeroma tambayoyin nan wanda ita kanta batasan amsarsu ba. Knocking d'in da ake shiya dakatar da ita daga tunin da take "yes come in" tace, masinja ne ya shigo yace "Hajiya kinada patients d'in da zaki duba naga time na tafiya" hakane Baba gani nan fitowa, sai kin fito ya bata amsa ya juya ya fita...
   Kayan buk'atarta ta kwasa ta fita, tana fita suka had'u da Dr Ammar murmushi ya sakar mata wanda ta rasa dalilin yi mata irinshi dan duk in suka had'u irin shi ya ke mata "Dr ashe kinzo shine baki nemeni ba?" Maganarshi taji yana tambayarta...
   Murmushi tayi tace "wlh ina zuwa office na wuce yanzu nake niyar shiga mu gaisa" ai gashi mun had'u dariya tayi sosai wanda idan da zaga fuskarta to tabbas zaka san maganan ta bata dariya "aikam" ta bashi amsa..
   Nan dai suka gaisa ta juya zata wuce "Dr" ya kirata tsayawa tayi cak amma bata amsa ba bakuma ta juyo ba...
    Takawa yayi ya isa wajenta "mike tsakaninki da yaron nan yake zuwa nemanki ya kai sati kullum sai yazo" ya tambayeta, juyowa tayi tace "wake nan?" Sameer mana..
   Mizai shiga tsakanina dashi nima bansan neman dayake man ba, toh yakamata dai kibi a hankali dan yaron bai da kunya, murmushi tayi tace "karka damu Dr" tana fad'ar haka tajuya tayi tafiyarta..

    Haka ta dinga duba marassa lafiya d'aya bayan d'aya, bakin gadon wata ta tsaya dubata tayi sosai, daga k'arshe ta rubuta mata magunguna juyawa tayi tama  mai jinyarta magana amma bata ga kowaba girgiza kai tayi  Nurse takira tace "kinga takardan maganin nan idan masu jinyar yarinyar nan sunzo su siyo mata maganin nan dan ana buk'atarshi da sauri" toh Dr zan gaya masu aje takardan tayi ta cigaba da aikinta...
    Tsaye yake bakin gadon yarinyar murmushi yayi ya d'auki takardan maganin ya aje wata, fita yayi yana dariya. Wanda mukanmu Four stars bamusan miye yake shirin yi ba...
   Yana fita ya fad'a motarshi cike da fara'a dan ganin burinshi ya kusa cika, fizgar motar yayi yabar asibitin cike da murna...
   Cike da fara'a ya isa gida, baiko ida rufe motar ba yayi cikin gida, haka ya fad'a batare da yayi sallama ba hanyar d'akishi ya nufa ji yayi tace "wai kai wane irin yaro ne zaka shigo gida ba sallama?" Juyowa yayi yace "Ummana yanzu kuma minayi dan Allah daga banyi sallama ba sai ki taman fada?" harara ta wurga mashi, Mummy ce tafito ta rungumeshi tace "dan Allah ka dinga kiyaye abinda ba'aso kasan idan aka tab'aka ba so nake ba amma kuma laifin ka ne" bubbuga k'afarshi yakeyi yace "na shigo cikin farin ciki amma an b'ataman rai" tsoki Umma tayi tabar parlourn dan takaici...
   Rungumeshi Mummy tayi tace "kayi hak'uri my baby kaji? Muje kaci abinci" haka tajashi suka tafi...

   K'arfe biyar daidai ta tashi, jikkarta da sauran tarkacenta ta d'auka, bayan mota ta zuba su kana ta shiga mota key ta ma motar kana ta fita daga asibitin. Tuk'i take a tsanake ga k'ira'ar sudais na tashi da kaganta kasan bata cikin damuwa hankali kwance take tuk'inta...
    Horn tayi maigaidi ya wangale mata gate yana murmushi, saida tayi parking ta fito har k'asa ta gaidashi amsawa yayi yana shi mata albarka..
   Cikin gida ta nufa tana kwalama Mama kira, parlour ta tarda ita zaune tana kallon MBC bollywood, fad'awa tayi kanta tace Mamana kina jina kika kyaleni?.
    D'agota Mama tayi tace "Haba Nanana ban jiki ba hankalina yatafi ga kallo" dariya tayi tace "nagani kam"..
   Ya aiki? Hope ba wata matsala? Murmushi tayi tace "lafiya lau babu wata matsala Mama" Allah ya k'ara tsareman ke Nanana. AMIN Mamana..
   Sai tayi niyar gayama Mama abinda Sameer ke mata sai ta fasa saboda batasan hankalinta ya tashi..
   Bubbuta tayi tace "tunanin mi kike?" Murmushi tayi tace "bakomai" toh tashi kije kiyi wanka kizo kici abinci..
    Peck ta mata tace "angama Mamana" murmushi Mama tayi tana k'arajin san tilon d'iyarta data zame mata abun alfahari..

FOUR STARS🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245