RASHIN GATA 11-15

🌼🌼 *RASHIN GATA*🌼🌼

*TANBARIN*
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

```NAH```
*FOUR STARS*⭐⭐⭐⭐

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI```
```(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HUSAYN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRAH BUKAR```
```(CUTIE ZARAH)```

11-15

Da sauri ta d'ago ta kalleshi tace "Dr abuja fa kace?" Eh abuja ne can akayi posting dinku girgiza kai tayi cikin takaici tace "Dr taya zan iya tafiya Abuja nabar Mahaifiyata? Kafi kowa sanin ni kad'ai gareta wlh bazan iya tafiya na barta ba nikam indai Abuja ne saidai nayi resigning"...
   Murmushi yayi ya kalleta yace "yanzu dan anyi posting d'inki Abuja sai kice zaki aje aiki? Inaga aikin nan shine yake taimaka maki" eh shine amma nafisan na zauna kusa da Mahaifiyata akan na cigaba da aikin nan...
   Tsayuwa ya gyara yace " Dr Khadija inasan yanda kikesan Mahaifiyarki" murmushi tayi tace "Dr kenan dole na sota ita kad'ai gareni dole na nuna mata kulawa da k'auna kamar yanda ta nunaman ina k'arama. Hakane kam Allah yaja maki da ranta tace
      "Amin"
   Khadeejah kiban hankalinki wannan trasfer d'in da aka maki tana tare da d'umbin alheri saboda kin k'ara samu matsayi, zaki koma aiki a *NIZAMIYE HOSPITAL* sun baki gida a maitama sun baki motar hawa kuma sanin kanki ne Asibitin da aka maidaki tana d'aya daga cikin asibitin da ake ji da ita...

  Dariya ta farayi tace "Dr are crious?" Murmushi yayi yace "zan maki k'arya ne?" Ah ah kawai ina mamakin yanda na samu d'aukaka haka..
   Tabbas biyayyar da kikema Mahaifiyarki da kuma rik'o da amana da kikeyi wajen aikinki  zaki kai inda baki tsammani ba Khadeejah kedai abinda nakeso dake ki cigaba da rik'e amana..
   Hawayen da suka taru ta share tace "hakane kaima Dr nagode da irin kulawar ka akaina" bakomai yace ya mik'a mata takardan yayi yana cema ta "congrats" da murmushi tace "Thanks"...
   Zaku wuce nextweek in shaa Allah, Dr ranan friday kenan? Eh dan gara kiyi shirye shirye dan monday zaki fara aiki, nagode abinda tace kenan bankwana sukayi yawuce ta nufi cikin gida da gudu tana kwalama Mama kira...

   Tana shiga cikin gida tsakar gida ta samu Mama zaune fad'awa tayi bisa ita tana dariya, d'agota Maama tayi tace "Nana karyani zakiyi?"..
   Dariya tayi tace "Mama ya za'ayi na karyaki wlh murna ce kawai" murnan mi Nana?..

   Zama ta gyara tace "Mama kinsan me?" Ah ah saikin fad'a, Mama an maidani Abuja..... Takwashe komai ta gaya mata yanda sukayi da Dr tace "kuma ranan Juma'a mai zuwa zamu tafi". Tun bata ida ba Mama ta rungumeta tana kuka, itama sai tasa kuka babu mai lallashin wani saida suka gaji suka bari dan kansu...
   D'agot tayi ta share mata hawaye tace "Allah na gode maka daka nunaman rana kamar irin wanan, tabbas Nana nayi alfahari dake a matsayinki na d'iyata Allah ya kareki ya tsareman ke daga sharrin mutum da Aljan, abinda nakeso dake ki cigaba da rik'e amanar aikinki ina alfahari dake kuma nasan duniya ma tana alfahari dake"...

   Hawaye ta goge tace "Mama kome na zama kece sila samun uwa irinki sai an tona kin zameman uwa kin zameman uba bansan ubana ba ke nasani na gode Mama Allah ya ja kwana". Rungumeta Mama tayi tana k'arajin san tilon d'iyarta a ranta...
      Saura kwana biyu su tafi suka shiga makwabta suna bankwana wasu harda kuka dan Mama da Khadija mutanen kirki ne, idan yaransu basu lafiya Khadeeja ke kula dasu..              
                     ★★★★★★
   Tunda sukayi asuba basu koma bacci ba shirin tafiya sukeyi saida suka shirya tsaf kana suka fito dan tafiya tasha. Fitowa sukayi suka kulle gida suka d'auki hanya, juyowa Mama tayi ta sake kallon gidan hawayen da suka mak'ale mata suka gangaro da sauri ta gogesu ta juya suka cigaba da tafiya...
   Suna isa tasha sukayi sa'a saura mutum uku shiga sukayi basu kai minti biyar ba mutum d'aya yazo nan aka cika mota suka d'auki hanyar Abuja..

   Mudai *FOUR STARS* sai muce Allah ya saukesu lafiya ..

Four stars⭐⭐⭐⭐

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245