JARABAWA TACE 201~205

JARABAWA TACE



yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                          (NWA)



        2⃣0⃣1⃣➖2⃣0⃣5⃣

   Da sallama ya shiga cikin gidan babu kowa, d'akin Ammi ya nufa da sallama amsa mashi tayi tare da bashin izinin shiga, kusa da ita ya samu ya zauna. Kallonshi Ammi tayi tana murmushi tace "Auta tunda ka samu Lady ka manta dani ka daina firar dare dani" dariya yayi ya d'ora kanshi bisa cinyarta yace "Ammi kefa kikace na nemo maki surika" dan nace anemo man surika sai kuma a daina fira dani? dariya yayi yace "Ammi gara mufahimci juna da ita" murmushi tayi ta shafi sumar kanshi data keta shek'i tace "dole kaman dad'in baki" dariya yayi sosai yace "ba maganan dad'in baki"...
   Fu'ad ta kira sunanshi amsawa yayi da "NAAM" dan yasan duk san da Ammi zata kirashi da sunanshi to muhimmiyar magana zatayi dashi...
   Tashi magana nakeso nayi dakai, ba musu ya tashi. Fu'ad inasan ka rik'e yarinyar nan fisabilillah da zuciya d'aya kaga kai ne babba to dan haka sai kazama namiji idan ta maka laifi ka zaunar da ita ka mata magana cikin ruwan sanyi yanda zaku fahimci juna, dan Allah kaba marar d'a kunya ka rik'e amanar ta ka share mata hawayenta kaga irin halin da tashiga na maza dan Allah ka tausaya mata ka kusance ta ka bata duk wani taimako ka jawota jikinka kasan matsalarta kaga marainiya ce nan gaba kai zaka zama iyayenta dan Allah ka rik'e ta da amana, duk da nasan d'ana na kuma san halinshi amma ina k'ara tunatar dakai ne amatsayina na maifiyarka...
   In shaa Allah Ammi zanyi amfani da maganarki zan zame ma Nafisa gata sai tayi alfahari da zuri'armu gaba d'aya, kuncinshi ta shafa tace "shiyasa nake Alfahari dakai Allah ya maka Albarka ya baku zuri'a d'ayyaba" Amin Ammi nah...
    Kallonshi tayi tace "watarana zaka barni ni kad'ai gidannan ko?" Tausayin mahaifiyarshi ya kamashi yace "Ammi ai ginin danakeyi akwai part d'inki kinsan ban iya barin ki ke kad'ai" dariya tayi tace "to mizai sameni?" Nidai hakanan Ammi gara ki koma kusa damu, zan koma amma sai matarka ta haihu kana, dariya yayi yace "ba yanzu ba kenan" yana fad'ar haka ya mik'e yana dariya ya nufi d'akinshi...
   Girgiza kanta tayi ta d'aga hannu sama ta nama Allah godia, daya gwada mata Fu'ad zaiyi aure..

   Yana shiga d'aki toilet ya fad'a wanka yayi sai da ya feshe jikinshi da turare kana ya saka kayan bacci, AC ya kunna yaja blanket..
   Waya ya jawo ya danna kira, final choice nagani akan screen d'inshi sai pic d'inta daya bayyana wanda tayi matuk'ar kyau gashi ta bud'e hak'oranta tana dariya yanda kasan mai tallar closeup...
   Ringing biyu ta d'auko, "Hello prince charming" abinda tace kenan, amsawa yayi da Naam wifey ya kike? Lafiya lau ta bashi amsa..
   Fira sukayi sosai kowa na tona asirin zuciyarshi sai k'arfe biyu sukayi bankwana dan ma tace mashi bacci zatayi da kyar ya kyaleta..
    Bankwana sukayi kowa ya kashe wayarshi, adu'a yayi ya ja blanket ya rufe kanshi, murmushi yakeyi yana tuna Ladynshi da haka har sarkin b'arayi yayi gaba dashi....

   Tsaftatacciyar soyayya ke tsakanin Lady da Fu'ad, burin kowa ya kyautatama d'an uwanshi, ko fad'a sukayi basu yarda su kwana basu shirya ba...
   Babu wanda bai san soyayyar Fu'ad da Lady ba, har dai b'an garen Fu'ad kowa yayi mamaki idan aka gaya mashi Fu'ad na neman aure, duk wanda ya bud'a baki sai yace "yarinyar da tasamu Fu'ad tayi dace da namijin kwarai"...

   Komai yayi farko yana da k'arshe tabbas hak'uri babban abu ne duk wanda yayi hak'uri yaga bai ci riba ba to hak'urin kad'an yayi saboda duk wanda yayi hak'uri to zai ci riba gaba. Jarabawa babu ta inda bata zo maka, babu ta inda Allah baya jarabbatan bawanshi wani ta yara, wani ta aure, wani dukiya, kai ta ko ina ma, shiyasa duk idan Allah ya jarabceka da abu ka saka hannu biyu ka karb'a dan gaba sai kayi dariya. ALLAH kasa mudace kabamu ikon cin rabawar daka bamu...

  A yau yan gidansu Fu'ad sukazo neman auren Nafisa kuma an basu inda suka bada kud'in neman aure dubu d'ari, an saka biki wata uku masu zuwa...
   Koda Ammi tajema Fu'ad da labarin ambashi Lady har an saka biki wata ukku, kallon Ammi yayi ya fashe da kuka, hawayenshi ta share mashi tace "miye kuma na kuka? Ina d'auka farin ciki zakayi sai kuma naga sab'anin haka" kanshi ya d'ora bisa cinyarta yace "Ammi farin ciki ne yasani kuka yau nine na kusa mallakar Lady amatsayin matata tabbas mahak'urci mawadaci"..
    Wannan haka yake Fu'ad duk idan mutum yayi hak'uri tabbas zai ga nasara a gaba, a yanzu ba kuka zakayi ba godia zakama Allah dan shine ya dubeka ya cika maka burinka..
    Hannunshi ya d'aga sama ya nama Allah godia yana kuka, yana gamawa ya shafa...
   Juyowa yayi ya kalli Ammi ya sakar mata murmushi, murmushin ta sakar mashi tace "yaro na ya kusa girma an kusa fara kiranshi da Daddy dan haka sai ka aje shagwab'a" dariya yayi yace "ai har nayi jikoki idan kina raye ba zan daina shagwab'a ba" dariya tayi ta jawoshi ta rungume tace "Allah yasa ina raye zan ga jikokinka" kinama raye Ammi nah kedai Allah yaja da kwana, "Amin" ta amsa mashi...

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245