RASHIN GATA 36-40

🌼🌼 *RASHIN GATA* 🌼🌼

         *TANBARI*
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

```NAH```
*FOUR STAR*🌟🌟🌟🌟

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HUSAYN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTIE ZARAH)```

Page 36-40

   Saboda irin gudun da Dr Ammar da Nana sukayi shi yasa suka iso asibitin cikin sauri,  Kowa cikinsu gurin parking d'in motar sa yayi, Dr Khadija tariga Dr Ammar fitowa saboda daga get zuwa gurin parking d'inta babu nisa yayinda shi kuma wajen nasa yake chan ciki.
    Koda tafito bata tsaya gurinsu Sameer ba, domin batayi tsammani suke da buk'atar taba, hakan yasa directly office d'inta tanufa, sanin cewa Dr Ammar yayi Mata bayyani cutar, koda tashiga office d'in hijab d'inta ta cire ta d'aura lapcut akan kayanta ta kuma zare nikaf d'inta, tasa babban handkichef d'inta ta rufe tun daga hancinta har wuyata, yayinda ta kuma d'aukar babbar hula ta d'aura akanta ta kuma ja d'an kwalinta yarufe goshinta, koda tafito ta tarar Dr Ammar yana shirin knocking d'in k'ofar ta, "yawwa Dr muje ko?", abinda yace kenan eh muje room d'in da aka kwantar da ita, hankalin ta gaba d'aya yayi kan Mara lafiyar hakan yasa bata kulla da Sameer ba da yake binta da harara, domin shi Sameer ma ba haka yaso ba, yaso yayi Mata rashin mutunci ne, aman Dr Ammar yahana saboda sanin halin Dr Khadija da yayi a yan kwanaki, hakan yasa Sameer yaketa banka Mata harara dabatasan ma yanayi ba, direct room 3 sukayi gaba dayan su.

    Koda suka k'arasa room din, sun tarar jikin Mummy yak'ara tsananta, domin duk k'uraje sun bayyana a jikinta yayinda da kuma babusu, hakan yasa hakalin Khadija yakuma tashi  Dr,  Hajiya, Alhaji a kud'an bani gurin, domin naga duk inda k'urajen suka fito Mata saboda sani dad'ewar ciwon a jikinta, OK Dr sukace su duka sukayi hanyar fita aman banda Sameer da yaye k'ik'am guri daya, kayan Mummy tad'an Fara yayewa domin sanin yanayi ciwon sosai, juyowa tayi domin dauk'ar glass d'inta kawai taga mutum a tsaye, yana cikin Riga da wando yayinda yad'aura hula akansa kayan sunyi masa kyau sosai, "Kai kuma fah?" tace dashi..
    Kallon rashin sani ta mashi tace "Malam yadai waye kai kuma?"..
   Harara ya wurga mata yace "bansani ba" ido ta zaro tace "kamar ya baka sani ba? Anyway kafita inasan na dubata ne idan na gama sai ka dawo"..

   Bazan fita ba miye kike tak'ama dashi waye ubanki wai a garinnan? Kinsan waye ni kuwa ko kuma ita kinsan wacece ita da sai da kika gadama zakizo? An gaya maki talaka k'azama irinki na duba Mahaifiyata ne? Dubarki k'azama dake saboda tsanin muninki har rufe fuskarki kikeyi wlh baccin ance zamu iya rasa ta da banga abinda zatayi wajenki ba..
   Sakin baki tayi tana kallonshi saboda tunda take ba'a tab'a ci mata fuska irin haka ba sai yau..
   Kallonshi tayi tace "kagama? to kasani kai baka isa kace zaka takani ba kowaye kai kuwa kuma komi kake tak'ama dashi ni nafi k'arfin wulakanci saboda Allah bai wulak'antani ba kai baka isa ka wulak'anta ni ba, kuma kasani bazan dubata ba duk abinda kake tak'ama dashi kayi" tana kaiwa nan ta cire handglops d'in hannunta tabar rum d'in rai b'ace...

   Tana fitowa tayi office d'inta kayanta ta kwasa tayi hanyar fita tana fita sukaci karo da Dr Ammar ganin yanayinta yasan ba lafiya, Dr! Dr! Dr! Yake kiranta amma ko juyowa batayi ba, dasauri ya sha gabanta daidai zata bud'e mota, ajiyar zuciya yayi yace "haba Dr miye wai?"..
   Juyowa tayi ta kalleshi ta goge hawayen da suka zubo mata cikin nik'ab tace "Dr kayi hak'uri bazan duba marar lafiyar nan ba" daga baya sukaji ance miyasa?
    Juyawa sukayi gaba d'aya sukaga su Umma ne dafata Umma tayi tace "d'iyata miyasa bazaki dubata ba? Ki taimaketa ki ceci ranta dan Allah"..

    Mama yanzu d'anta ya dace yaman cin fuska? Gaba d'aya sukace "Sameer ko?" Eh inaga shi bandai san sunanshi ba..... Nan ta kwashe komai ta gaya masu tace "yakamata yaman uzuri ga Dr nan Mahaifiyata bata da lafiya nabarta nataho ceton Mahaifiyarshi amma zai gayaman irin wannan maganganun ina tunanin iyaye aibasu fi iyaye ba"..
   Dafe kanta Umma tayi ta kalli Daddy tace "kunga irin tarbiyan da kuka d'ora yaronku akanta ko? Kunsan sarai bai san talaka amma baku tab'a gwada mashi da talaka da mai kud'i duk Allah ne yayishi nikam ina takaicin irin tarbiyan yaron nan yake bisa ita ba"
    Gumin daya karyoma Daddy ya goge yace "yanzu ba lokacin wannan maganganun baneba ke kuma Dr don Allah kiyi hak'uri kar kibiye halin Sameer ki dubata in shaa Allah zan d'auki mataki..

   Hawayen dake sharara kan kuncinta tashare, shikenan Alh babu damuwa, shiko Sameer koda tafito jiyayi hankalisa yayi mugun tashi gani Dr tatafi ga Mummy d'insa rai a hannu Allah, bin bayyanta yayi Amman sai ya tarar dasu Daddy d'insa suna bata hakuri,  ransa ne yayi mugun baci ganin duk matsayinsa yatsaya yana bawa yarinyar cikinsa hak'uri, wai ke wace? da ubanmi kike tak'ama da har za'a tsaya ana baki hak'uri, saukar Marin daya jine yasa yayi tsit, tunda yake a duniya daga Mummy, Daddy har Umma babu Wanda ya tab'a daga hannu ya bugeshi sai yau saboda wata banzar yariya, bai iya cewa komai ba sai k'arasawar dayayi gurin motarsa da gudu yabar asibitin, ko takansa Umma bata biba tace "Dr Khadija ta taimaka takoma", cikin room d'in takoma ta duba Mummy sosai sanan takirasu zuwa office dinta, shi ko Daddy baiji dad'in marin da Umma tayiwa Sameer ba, saboda duk duniya babu wanda Daddy keso kamar Sameer, hakan yasa ransa yasosu matuka saidai sanin halin Umma da yayi bata d'aukar shirme da wulak'anta talaka yayi hak'uri.

   Cikin nutsuwa tafara yiwa Dr, Daddy, dakuma Umma bayyan ciwon Mummy.
*Funfuna shine mold sickness* Ana samun ciwon ne ta hanyar cin bread,lemo ko wani Abu haka a gida Mai funfuna, ciwone Mai zafin gaske, so sai shima mutum yafara fun-funa, funngal infection ne, so sometimes ba dole mutum yayi fun-funan ba, amma in ya shaka fun-funan ko ya taba da jikin shi sai mutum yayi reaction. Yayi ta tari soshe soshe yoyon majina dadai sauransu. So ana so mutum yadai na zuwa kusa da fun-funan, idan ba'ayi maganinsa cikin gagawa mutum yakan iya rasa ransa, To ita tata ta skin ce.
   Yanzu zan rubuta muku magani aje a Fara yimata amfani dasu, Dr Ammar ne ya katseta dacewa "Dr kamar wane magani  Mai ciwon yake bukata kenan?" nima inaso nasani, murmushi tayi tace  "ok Dr yanzu zaka jisu"  kamar-  nasal spray, loratidine tablet, caps, levofloxacine, tab diclofenac, any anticeptic sune magungunan da mai ciwon yake buk'ata, Hajiya amata amfani da wad'annan magungunan mugani zuwa nan da wani lokaci, godiya da sa albarka tai tasha gurin Umma da Daddy, murmushi tayi tace "nagode sosai da aduarku" Umma tace "muna iya zuwa muganta?" Mizai hana Mama zaku iya zuwa amma dan Allah afara mata amfani da magungunan yau "in shaa Allah za'a fara" cewar Daddy kenan, sannan sukayi Mata sallama suka tafi, itama key din motar ta ta d'auka tabi bayansu.

Four star🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245