JARABAWA TACE 206~210

JARABAWA TACE



yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                          (NWA)
              

2⃣0⃣6⃣➖2⃣1⃣0⃣

   B'angaren Lady ma haka take duk wanda ya ganta yasan tana cikin farin ciki, su Yaya har tsokanarta suke "ku kyaleni na tsaneshi bazan tab'a sanshi ba dan baku akama abinda aka mani ba shiyasa" da sun fara sai tara kumbure fuska tace "Uncle kana jinsu ko?" Dariya yakeyi yace "kyalesu zasu gaji su bari kinji My Lady" ...
   Ita kanta abin mamaki yake bata tabbas duk wanda bai yi hak'uri da jarabawarshi ba toh bazai ga da kyau ba, gashi hak'urin da tayi Allah ya saka mata da miji mai santa, wani lokacin Fu'ad har tausai yake bata saboda irin san da yake mata..
     Tabbas data biyema zuciyarta ta bijirema zab'in da Allah ya mata da ta tabka babban kuskuren da batasan ranan da zata gyara shi ba...
   Kullum adu'arta Allah ubangiji ya bata ikon yima mijinta biyayya....

    Yau aka kawo lefen Lady akwati goma sha biyu iya fad'in kayan lefen b'ata baki ne na barma masu karatu su k'iyasta da kansu duk inda aka kawo wannan lefe tabbas kasan babu kayan banza...
   Da daddare suna fira yace "My lady akwai abinda bai maki ba na lefen a canja?" Dariya tayi tace "komi fa yayi" indai akwai abinda bai maki ba ki fad'a karka damu my love komai yayi. Daganan suka fara firan soyayya...

   Zaune take falo ga IV da Fu'ad ya kawo mata ta tusashi gaba tana ta kallo, da sallama suka shigo gidan, amsa masu tayi k'arasowa sukayi cikin falon, kallonta Zainab tayi tace "Besty yadai?" Murmushi tayi tace "IV nan nake kallo na events Fu'ad ya aiko dashi na rabama k'awayena ni bai mayi shawara dani ba, infact bai san banda k'awaye bama ni.."
   Dariya Inteesar tayi sosai tace "Anty Lady kinga ranan k'awaye yau ko?" Harararta tayi tace "bansani ba" toh yanzu besty miye abunyi? Ina nasani Besty, murmushi Intee tayi tace "karki damu indai k'awayene zasu baki mamaki..."
    "Taya?" A tare suka tambayeta..
   Ido ta zaro tace "kuji yanda kuke had'a baki, Anyway k'awayena zamu kai mawa kuma nasan zasuzo" kallonta sukayi Zainab tace "kin tabbata?"..
   Karki damu Ya Zainab za suzo i knw dem so idan da bazasu zo ba bazance akai masu ba. Da wannan shawaran suka amince suka fara rabon IV..

   Kwanansu biyu suna rabon IV duk wata k'awar Inteesar sai da suka kai mata kuma sun tabbatar masu za suzo, ba k'aramin dad'i sukaji ba bare ma da suka gansu yan gayu dasu....
   Anty Maijidda ce ta kawo mata mai gyaran jiki daga maiduguri, sati d'aya za'ayi ana gyarama amarya jiki kuma ko k'ofar gida bata zuwa...
   Yau aka farama Amarya dilka amma zaka rantse da Allah an dad'e ana mata saboda wani shek'i da takeyi...

   Wayanta ne yafara ringing ganin wanda ke kiranta ne yasa gabanta ya fad'i dan tun randa aka fara mata gyaran jiki yakesan ganinta amma ba hali...
   Sai da ta kusa tsinkewa kana ta d'auka, jiki sanye tace "Hello" baiko amsa ba yafara masifa...
   Wifey miye haka? Yau kusan kwana uku ina binki kink'i yarda muhad'u dana maki magana kice gyaran jiki ake maki wani abu nace zan maki ne? Wlh kun d'auki hakki na da yawa haba, ina d'akin Aflan idan kina iya zuwa ina jiranki. Baiko jira amsarta ba ya kashe wayarshi...
   Kallon wayar tayi hawayen da suka zubo mata ta share..
   Tash tayi ta nufi d'akin Aflan a falo sukaci karo da Anty Maijidda "ina zaki?" Tambayar da ta mata kenan..
   Am am dama, dama mi? Fu'ad ne kesan ganina yana d'akin Aflan..
   Kallon da Anty Maijidda ta bita dashi ne yasa jikinta ya fara rawa juyawa tayi ta nufi d'akinta da gudu..
   Kan gado ta fad'a tana kuka, jitayi an d'agota. Besty lafiya kike kuka?..
   Besty Fu'ad ne, da sauri ta kalleta tace "mi Fu'ad d'in ya maki?" Besty Fu'ad fushi yake dani nan ta kwashe komai ta gaya mata, kuma Anty Maijidda ta hanani ganinshi Besty kinsan halin Fu'ad Allah tausai yake bani nikaina ina san ganinshi amma ba yanda zanyi nidai dama ba'a fara wannan gyaran jikinba duk shi ya nisantani da masoyina..
  Murmushi Zainab tayi tace "kuyi hak'uri ku duka kinji duka ma saura kwana nawa ku zama abu d'aya" da kyar ta lallasheta...

*****
   Yau aka fara event inda sukayi kamu  Beejay ce tama amarya makeup, house of kaya suka mata dress color d'in cream amarya tasha kyau har ta gaji duk wanda ya kalleta baisan ya daina kallonta, haka ango yasha kaftan na getzner shi kuma BZ ne suka mashi d'inki masha Allah sunyi kyau har sungaji..
  Bride maid ma sunyi kyau dan ankon red atamfa sukayi inda sukayi d'inkin bubu da zani gaskia daga amarya har k'awayen amarya sunyi kyau sosai abokan ango ma ko ince dangin ango sunyi kyau kowa kagani da getzner d'inshi tana shek'i...
   a katsina motel a kayi kamu inda yasha decoration sai dai ango fushi yake da amarya da sun had'a ido zai wurga mata harara ita abun ma dariya yake bata..

  Ado gwanja ne ya masu wasa, amarya da k'awayenta sun cashe anguna kuwa sunyi b'arin kud'i...
   Takwas daidai aka tashi kowa ya nufi gidanshi tare da paper bag mai d'auke da hoton ango da amarya..
   Tunda suka shiga mota bai ce mata k'ala ba bai kuma kalli inda take ba har suka iso gidansu...
  Wuri ya samu yayi parking bai kalli inda take ba yace "sai da safe" hannunshi ta jawo tace "fushi kake dani?" Bai ce mata k'ala ba sai ma hannunshi da yake k'ok'arin kwacewa...
   Kanta ta d'ora bisa kafad'arshi tana hawaye, jin hawayenta yasa ya d'agota da sauri yace "No princess kidaina kuka pls" taya bazanyi kuka ba kana fushi dani ka kasa yarda dani wlh nima inasan ganinka babu yanda na iya ne pls kayi hak'uri...
  Hawayen ya share mata yace "ya isa hakanan na hak'ura" dagaske? Murmushi yayi yace "eh mana" to prove me ingani, peack ya mata ga kumatu, lumshe idanta tayi tanajin wani abu na ratsata..
  Fira suka d'anyi daga k'arshe sukayi bankwana yawuce gida...

   Yau ta kama friday kuma yau suke dinner tunda suka tashi suke shirye shiryen dinner wacce za'ayi a katsina sahara suites..
   K'arfe takwas ta fito ciki  shirinta na red nd gold dress d'in  tayi matuk'ar karb'an jikinta falke ta mata d'inki nan ma Beejay ce ta mata makeup...
  K'awayen amarya ma sunyi kyau dan ankon lace sukayi pink color, kuma d'ikinsu duka iri d'aya wannan aikin Inteesar ne..
   Shima ango yasha kyau cikin farar getzner d'inshi..

   K'arfe tara aka fara dinner inda aka fara da opeining prayer daga nan Zainab tazo tayi biography amarya, tana gamawa Aflan yayi na ango dan angon ma ba wasu abokai gareshi sosai ba..
   Daga nan karode bello ya fara wasa yana gamawa davido ma yayi nashi yana gamawa Adam A Zango shima yayi nashi..
  Daga nan kuma aka yanka cake ango ya ba amarya itama taba mijinta...
  Kowa yaci yasha anyi pictures dan masu pix sun kai biyar wanda su kazo cikinsu dai mai gaskiya kawai nafi ganewa lolzz
   Duk wanda kagani fuskarshi d'auke da murmushi, sai k'arfe sha biyu aka tashi daga dinner...

   Hausawa sunce rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya. Kuma duk abinda aka sama lokaci to tabbas lokacin zaizo wannan haka yake..
  Yau asabar aka d'aura auren Fu'ad da Nafeesa akan sadaki dubu d'ari uku lakadan ba ajalan ba inda dubban mutane suka shaida d'aurin auren cikinsu harda governor katsina Alh Aminu bello masari, da sarkin katsina Alh Abdulmuminu Kabeer Usman....
   Ana gamawa aka wuce katsina motel danyin reception...

   K'arfe biyar yan d'aukar amarya sukazo, kwance take d'aki tayi rubda ciki tana kuka, Anty Maijidda ce ta shigo d'akin tace ta tashi ta shirya, Anty ta taimaka mata ta shirya amma k'in yarda tayi su had'a ido..
  Tana gama shiryawa ta nufi falon Uncle da ita, k'asa ta zaunar da ita tace "Uncle ga amanarka nan zata tafi gidan miji kasa mata albarka" hawayenshi ya share yace "Nafeesa yauce ranar da zamu rabu kibi mijinki ki mashi biyayya fiye da yanda kike mana nasanki nasan halinki ina alfahari da irin tarbiyan da kike da ita inasan kiyi amfani da ita ki rik'e mahaifiyarshi kamar ita ta haifeki, ga wannan ki rik'esu zasu taimakeki a rayuwa" litattafan adu'o ine ya bata amsa tayi tana kuka kije Allah ya baki sa'ar rayuwa Allah ya albarkaci aurenki yana kaiwa nan ya shige d'aki yana hawaye..
   Duk'ewa tayi tana kuka ita kanta Anty Maijidda sai da tayi kuka..
   Hannunta ta kama ta nufi d'akin Yaya da ita suna sallama ta fizge ta ruga da gudu ta fad'a kan Yaya tana kuka, ita kanta Yaya kukan takeyi babu wanda bai masu kuka ba..
  Anty Maijidda tayi k'arfin hali tace "gatanan ki mata fad'a" babu fad'an da zan mata saboda nasan kun mata kuma Uncle d'inta yamata, Nafeesa kije Allah ya baki sa'ar rayuwa yasa gidanki kenan, ki cigaba da yima iyayenmu adua...

  Aflan ne ya shigo d'akin daidai ta mik'e rungume juna sukayi suna kuka kamar zasu cire ransu babu wanda bai masu kuka ba cikin kuka yace "Anty Lady dagaske tafiya zakiyi kibarmu? Dan Allah karki tafi wlh bazan juri rashinki ba a gidannan dan Allah ki zauna damu.."
  Tsananta kukanta tayi tana nafasa kubarni gidanmu..
  Uncle ne yashigo da kanshi ya kamata ya fita da ita tana cijewa tana kiran Aflan haka ya kaita cikin mota ya sakata kana su Anty Maijidda suka shiga..
  D'aki Aflan ya koma da gudu yana kuka..

   Gidanta dake Fauziyya estate aka kaita, gidane na gani na fad'a na kece raini ya dank'ara mata, ga kuma gidan yaji kayan alatu abun saini da Anty Maijidda da mukagani lolzz..
   D'aki uku aka mata sai parlour hud'u sai balcony wanda shima sai da aka k'aya tashi da alatu kitchen d'inma an shiryashi gidan iya tsaruwa ya tsaru na barma masu karatu suyi immagination d'in gidan..
   D'akinta dake sama aka kaita, nan ma nasiha Anty Maijidda ta mata sosai mai ratsa jiki, daga nan sukayi bankwana suka barta daga ita sai su Zainab da Inteesar..

  K'arfe tara daidai aka rako ango amma babu Aflan ciki  yan rakiyan dama tasan da kyar zaizo..
  Nasiha suka masu sosai daga nan suka sayi bakin amarya dubu d'ari suka masu sallama..
  Mik'ewa su Zainab sukayi dan tafiya ai nan ta rik'esu tace batasan wannan ba dakyar aka kwacesu, d'aki ta nufa tana kuka su kansu kuka sukeyi bama kamar Zainab...
  Rakasu yayi yana dawowa ya kulle ko ina ya kashe wuta sama ya haye d'akinta, da sallama ya shiga d'akin amma ta kasa amsawa saima kuka da takeyi, ledojin hannunshi ya aje ya haye saman gadon...

  Lifayanta ya yaye ganin tana kuka hankalinshi ya tashi kanshi ya d'ora bisa cinyarta Wifey miya saki kuka? Ko dai har yanzu baki sona? Hannunta ya kamo ya d'ora bisa k'irjinshi yace "wlh zuciyana zafi zata iya fashewa idan ina ganinki cikin wannan yanayin" kuka ya samata shima...
  Fad'awa tayi jikinshi tace "wlh Fu'ad inasanka san da bazan iya misalta mashi ba kawai ina tausayin halin dasu Uncle zasu shiga more especially Aflan kuka nabarshi yanayi." lallashinta yafarayi yace "kiyi hak'uri haka aure yake babu abinda zai samesu Aflan kuma sai kingaji da ganinshi kinsan zai mai da gidannan kamar gida.." ta yarda da maganarshi shiyasa ta daina kuka..
   Hannunta ya kama ya sauko da ita yace "jeki alwalla" ba musu ta tafi shima d'akinshi ya nufa danyin alwallar..

  Kusan tare suka fito darduma ya shimfid'a masu sallah sukayi raka'a biyu suna sallamewa yafara masu adua'ar neman tsari tare da zuri'a d'ayyaba..
  Juyowa yayi ya kama kanta ya mata adu'ar da manzanmu yace duk wasu sabon ma'aurata suyi, daga nan yamata tambayoyi tabashi amsa....
  Mik'ewa yayi yaje kitchen ya d'auko plates da cups gasasshin kaji ya juye ga fresh milk gefe, a baki ya dinga bata ba musu ta fara karb'a dan yunwa takeji rabonta da abinci tun jiya da safe..
   Sai data k'oshi kana ya faraci yana gamawa yakwashe kayan ya kaisu kitchen...
  Dawowa yayi ya kalleta murmushi ya sakar mata kanta ta juya gefe, hannunta ya kamo yace "tashi muje na maki wanka" ido ta zaro, yah wanka zan maki..
  Fu'ad kalla can yana juyawa ta fizge hannunta ta fad'a toilet ta maida  ta rufe tana dariya, dariya shima yayi ya nufi d'akinshi...

  Tana fitowa wanka ta shirya turaren da Anty Maijidda ta bata shi ta shafe jikinta dashi kafin kace mi jikinta ya d'auki k'amshi, kayan bacci ta saka data gani an ajesu bisa gado..
   Daga baya taji an rufe mata ido dariya tayi tace "ai k'amshinka bai b'oyuwa Husby" dariya yayi ya sunkuceta yayi bisa gado da ita...
   Zillewa ta dingayi tana kuka amma ina yafi k'arfinta kuka take tana rok'onshi amma baisan tanayi ba, wasa ya fara yimata daga nan labari yasha banban..
  Nidai k'afafuwana na jawo na rufe masu d'akin da fatan Allah ya basu zuri'a mai Albarka..
   K'arfe biyar na koma d'akin, k'udundune take cikin blanket tausayinta ya kamashi tashi yayi yaje ya had'a mata ruwan wanka, yana dawowa ya d'auketa bai direta ko ina ba sai cikin abun wanka, da kanshi ya mata wanka gasata yayi sosai kana ya barta ta ida fita yayi ya nufi d'akinshi danyin wanka..
   Cikin jallabiya ya shigo d'akin da sallama, amsa mashi tayi amma ta kasa d'ago kanta, zuwa yayi ya tadata murmushi ya sakar mata sunne kanta tayi jikinshi tana dariya, "tashi muyi sallah ko?" Abinda yace mata kenan, ba musu ta mik'e sukayi sallah..
   Tana gama adu'a ta koma kan gado ta kwanta, sai da yagama adua tare da yima Allah godia da yabashi mata kamila yana gamawa ya koma kan gadon, jawota yayi jikinshi ya rungumeta yana k'arajin santa a ranshi da haka har bacci yayi gaba dashi...

   K'arfe sha biyu suka fito cikin shirinsu na k'ananan kaya na company HUGO BOSS rigan fara sai wando bak'i kayan sun karb'esu kamar dansu akayi su..
   Daining suka isa dan Ammi ta kawo masu abinci, zuba mata yayi ya dinga bata a baki sai da ta k'oshi kana ya fara cin nashi yana gamawa ya kwashe kayan ya nufi kitchen dasu...
   Dawowa yayi ya zauna kusa da ita hannunta ya kamo yana murzawa a hankali, kallonta yayi yace "banda bakin da zan maki godia sai dai ince Allah ya maki albarka na gode kwarai da rik'e mutuncinki da kikayi Allah yabani ikon rik'e amanarki". Amin ta amsa mashi tana dariya. Wayanta ne yayi k'ara alaman text ya shigo, ganin sunan Aflan yasa ta saki murmushi. "I miss you so much Anty Lady nayi missing fad'anmu da wasanmu how i wish zamu k'ara zama tare muci abinci tare mu fita yawo tare, amma yanzu duk ba wannan Fu'ad ya mana wayo.." hawaye ta goge ta mashi reply tana gamawa ta mik'a Fu'ad test d'in, murmushi ya mata bayan ya gama karantawa...
   Kallonta yayi ya kashe mata ido, kauda kanta tayi tana murmushi. Dariya yayi ya sungumeta tana ta wutsil wutsil bai dire ta ko ina ba sai kan gado, nidai baro masu d'akin nayi......

Alhamdulillah anan zan aje biro na...

Godia ta tabbata ga Allah madaukakin sarki daya bani ikon gama litaffin nan kura kuran da nayi Allah ka yafeman..

Littafin tukuici ne gareku yan DANDALIN FEEDOH DEEDOH nagode da irin k'aunar da kuke nunama Fu'ad da Lady.....

Na sadaukar da littafin ga Lubabatu Sani Maitafsir Allah ya raya Ama yanuna man aurenta ranan akwai shoki..

Masu neman littafin zaku iya samunshi a blog ko a wattpad
Phirdauceejeebo.blogspot.com
wattpad @yar_ficika..

For comment or correction contact me at phirdauceejeebo@gmail.com

Sai kun jini a cikin sabon littafina BAIMAN HALARCI BA littafin da ya had'a soyayya tausayi cin amana yaudara, hmmm karku sake abaku labari..

Nagode sosai my sweetos.

Kusani wlh yar_ficika na sanku♥

Love y'all my dudes

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245