JARABAWA TACE 186~190

JARABAWA TACE



yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                          (NWA)



               1⃣8⃣6⃣➖1⃣9⃣0⃣

   Mik'ewa Uncle yayi yace "bari naje gida nasa Deeyerh ta had'o maku kayan buk'ata ko?" D'aga kai  Yaya tayi alamar "Eh" waya Fu'ad ya d'auko ya kira Ammi ringing uku ta d'auka bai koyi sallama ba bare ya gaidata yace "Ammi muna asibiti da Lady a nan Alheri clinic kizo yanzu, bai jira mi zata fad'a ba ya kashe wayarshi...
   Mamaki Yaya keyi irin wautar Fu'ad, kallonshi tayi tace "akanmi zaka d'aga mata hankali ka kuma kashe wayarka?" Dariya yayi yace "bafa d'aga mata hankali nayi ba kawai na gaya mata ne" mika mata in ba d'aga mata hankali ba ka kirata bako sallama kuma ka fad'a mata tashin hankali baka jira mitace ba ka kashe wayarka. Dariya yayi yace "yi hak'uri Mummy bazan k'ara ba"..
   Dariya Aflan da Intee sukeyi Aflan yace "Mummy wlh halin Fu'ad kenan yana san tadama Ammi hankali" harararshi Fu'ad yayi shiyasa ya kasa ida magananshi, "Mummy kiyi hak'uri bazan k'ara ba zan koma yanda kikeso" gaba d'aya suka sa mashi dariya harda Lady...

   Kanshi ya d'ora bisa hannun Lady yana hawaye, dasauri ta d'agashi tace "yadai?" Turo baki yayi yace "ba kece kika biye masu ba kinaman dariya" aikam nan Aflan yak'ara fashewa da dariya harda rik'e ciki, ita kanta Lady dariyar takeso tayi amma ba hali, hannunta ta d'ora bisa kanshi tace "kayi hak'uri bazan k'ara ba" wani sanyi yaji ya ratsashi har cikin zuciyarshi d'agowa yayi yace "dagaske?" D'aga mashi kai tayi tace "trust me" murmushi yayi yace "I trust you my darlyn baby"..
   Mamaki abun keba Yaya dan ita a tarihinta bata tab'a cin karo da soyayya irinta Fu'ad ba, kallonshi tayi tace "Fu'ad yakamata ka jajirce ka zama na miji fa yanzu idan Lady ta maka laifi ashe kuka zakayi ba hukuntata ba?" Dasauri ya kalleta yace "Mummy wlh ban iya hukunta Lady duk laifin da zataman bazan juri ganinta tana cikin b'acin rai ba nidai kutayani da adu'a Mummy amma san da nakema Lady ba kad'an baneba"..
   Gaba d'aya ya gama basu tausayi har ita Ladyn dan sai datayi hawaye, hannunshi ta kamo tace "kayafeman akan abinda na maka tabbas Allah ya kawoman kai ne kazama sakayya ga sauran mazan da suka yaudareni naso nayi butulci ga Allah tabbas dana saki kabarni da na tafka babban kuskure a rayuwata"..
   Karki damu Lady duk abinda kikayi kina da hujja yinshi, yanzu burina bai wuce ki amince da soyayyata ba, dariya tayi tace "soyayyarka tuni na gama amincewa da ita sai dai fatan Allah yasa Alheri cikinta" gaba d'aya suka amsa da
              "AMIN"
    Daidai Ammi na shigowa d'akin da sallama, amsa mata sukayi shigowa tayi ciki tana fara'a "sannu da zuwa ina wuni?" Yaya ce ta fad'i haka, ansawa tayi da lafiya lau ya mai jiki daidai tana aje basket d'in hannunta, da sauk'i ta bata amsa, gaidata su Aflan da Inteesar sukayi ta amsa cikin sakin fuska, shiko gogan baiko kalleta ba..
    K'arasawa wajen gadon Lady tayi tace "d'iyata ya jikinki?" Sunne kanta tayi ta amsa dasauki ga Fu'ad yak'i sakin hannunta, "Fu'ad ya cikaki da surutu ko?" Dariya tayi ta k'ara sunne kanta..
    "Fu'ad bakaga Ammi bane ba?" Yaya ce ta tambayeshi, turo baki yayi yace "Mummy tun fa d'azu na kirata sai yanzu ta zo shiyasa nayi fushi da ita" salati Yaya tayi tace "Fu'ad Allah ya shiryaka" murmushi Ammi tayi tace "ayi hak'uri Auta na tsaya yi mata abinci ne" dariya yayi kana ya kalli inda ta aje basket d'in...

   Tashi yayi yazo gaban Ammi yace "Ammi kitayani godia yau Lady ta amince tana sona" dariya Aflan yayi yace "wai bazaka kyale Ammi ba?" Harararshi yayi yace "basan sa ido"..
   Murmushi Ammi tayi ta kamo hannu Lady tace nagode sosai da irin karramawar da kikama Fu'ad in shaa Allah zakiyi Alfahari dashi sai kinyi dariya in Allah ya yarda". Sunne kai tayi tana jin kunyar abinda Fu'ad ya mata. Kallonshi Ammi tayi tace "kuka ya k'are ko?" Turo baki yayi yace "Ammi karfa ta rainani" dariya Ammi tayi tace "nayi shiru to" Aflan yace "Ammi yanzu ma yagama wani kukan" waikai ina ruwanka danine? Allah bari Daddy ya dawo shi zai rabani dakai, Ammi tace "to ai gaskia ya fad'a" Yaya ce tace "shima Aflan d'in ya cika neman rigima" tashi Aflan yayi yazo kusa dashi yace " natuba bazan k'araba" hararashi yayi yace "anjima ma k'arawa zakayi"....
   Yaya tace "wai Ammi ya akayi kika gane d'akin dan naga bai maki bayani ba yana gama d'aga maki hankali ya kashe wayarshi".
   Murmushi tayi tace "ai kad'an daga aikin Fu'ad kenan, koda nazo asibitin naita kiran wayarshi bai d'auka ba sai ga wata nurse tazo na tambayeta akayi sa'a kuwa ita ta masheta ta shiga da ita emergency shine ta gwadaman d'akin" wlh Ammi wayana silent take..

   Dr ne ya shigo d'akin ganin suna surutu ya d'aure fuska yace "akanmi zaku dameta da surutu?" Dariya Fu'ad yayi yace "sallamarta zakayi taji sauki"..
   Zaro ido  Dr yayi yace "dayake bata mutu ba ko? Dole kayi dariya toh sai tayi wata" d'aure fuska yayi yace  "katambayeta ta warke Allah" dariya Dr yayi daidai yamata allura ya sake d'aura mata drip saida ya gama ya juyo ya kalleshi yace "kayi hak'uri zan sallameta amma ba yau ba yanzu ma allurar bacci na mata dan kun sata surutu dayawa tana buk'atar hutawa"..

   Ammi tace Dr waya gayama ana biyema rigimar yaron nan? Ka cigaba da aikinka kaji, dariya Dr yayi yace "hajiya ai matarshi ce har kuka yakeyi dole na lallab'ashi karya saman kuka"...
   Aikam nan akafara dariya, itako Lady bacci yayi gaba da ita, harara ya watsama Aflan yace "bakada aiki sai dariya zanyi maganinka"..

   Sai dare kowa ya tafi gida da kyar aka samu Fu'ad yatafi dan cewa yayi nan zai kwana, sai da Uncle ya lallab'ashi kanan yatafi akabar Inteesar nan wajenta...

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245