JARABAWA TACE 191~195

JARABAWA TACE



yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                          (NWA)


  
            1⃣9⃣1⃣➖1⃣9⃣5⃣

          *BAYAN SATI D'AYA*

   Zaune take ta jingina da pillow ga abinci gabanta amma ta kasa ci, kallonta Intee tayi tace "yakamata dai kici abincin nan" ya mutse fuska tayi tace "nifa banjin yunwa" aikam cin abinci ya zamar maki dole daga bayansu sukaji anyi magana, gaba d'aya suka juya suka kalli inda ake maganar, tsaye yake jikin k'ofa ya hard'e hannunshi bisa k'irji yana murmushi..
   Murmushi ta sakar mashi ta rasa miyasa komi nashi burgeta yakeyi, k'arasowa yayi wajensu kallon Intee yayi yace "ya kuka kwana hope ba matsala ko?" Eh babu munama sa ran yau a sallamemu, inasu Mummy bangansu ba? Basu kaiga zuwa ba....
   Kujera yaja ya zauna ya k'ura mata ido, dariya tayi ta juyar da fuskarta gefe guda, murmushi yayi ya rik'o hannuta yace "ya k'arfin jiki?" Dasauki ta bashi amsa..

   Abincin ya d'auko ya kai bakinta kauda kanta tayi alamar bataci, nan suka fara rigima, dayaga tak'i karb'a aje abincin yayi ya mik'e tsaye..
   Dasauri ta rik'e hannushi juyowa yayi ya kalleta k'asa tayi da ido tace "ina zaka?" Gida zantafi mana, miyasa? Saboda zamana baida amfani tunda baza kici abinci ba, mararaicewa tayi tace "kayi hak'uri banjin yunwa ne" naji bakiji amma in dagaske kina sona to ki bari nabaki kinji?" D'aga kanta tayi tace  "na amince"..
   Zama yayi yana dariya yafara bata abincin babu yanda ta iya haka ta dinga karb'a tana taunawa kamar mai tauna magani, saida yaga takusa amai kana ya kyaleta ruwa ya bata tasha kana ya aje plate d'in...

   Hannunta ya rik'o yace "bae pls ki kalli ido na kice I love you" dariya tayi sosai tace "Fu'ad i can't gaskia"..
   Turo baki yafari yana buga k'afa, murmushi tayi cikin ranta tace "lallai kam ya cika auta"..
   Kinyi shiru pls kiyi abinda nace mana, nacema fa bazan iya ba shikenan na gode ya juya mata baya..
   Dariya tayi ta juyo dashi tace "Fu'ad i love you so much.."
   Lumshe idonshi yayi yace "I love you more"..

   Haka Dr ya shigo ya samesu yana ganinshi ya fara mashi tsiya suna wasa, kallon Dr yayi yace "yau ne zaka sallameta ko?" Waya ce maka zan sallameta yau ai sai tayi wata, ido ya zaro yace "aikam zan sace ta" dariya Dr yayi sosai yace "bama sai ka sace ta ba yau zan sallameta"..
   Dubata Dr yayi, rubuce rubuce yayi cikin file d'inta takarda ya mik'ama Fu'ad yace "kaje kayi clearing yau na sallameku" dariya Fu'ad yayi ya karb'i takardan" bankwana sukayi da Dr, kallonshi tayi tace "akira su Uncle ko sai su biya" harara ya wurga mata ya juya ya fita sai da yakai bakin k'ofa yace "Intee ki had'a kayan dana zo wucewa zamuyi kawai basai sunzo ba" to ta amsa mashi...

   Shigowa yayi yace "kutashi mu wuce" shiya kama Lady ya mik'ar da ita hannunta ya rik'e suka tafi har wajen mota gaba mota ya bud'e mata ta shiga shiga sukayi, key ya ma motar kana ya d'auki hanyar gidansu Lady...
   Horn yayi bakin gate d'in gidan mai gadi ne ya wangale masu gate d'in cinna kan motarshi yayi cikin gidan, parking space yasamu yayi parking, suna fitowa daga mota daidai su Uncle suna fitowa daga cikin gida...
    Dasauri suka k'arasa wajensu Yaya tace "mizan gani haka?" Dariya yayi yace "an sallamemu Mummy" hararar Aflan Uncle yayi yace "duk kai ka b'ata mana lokaci" dariya yayi yace "dama bansan zuwa"...

   Jawo Lady Yaya tayi tace "sannu kinji" dariya tayi ta sunne kanta..
   "Kunyi clearing da asibiti ne?" Uncle ne ya tambaya eh munyi Daddy, nawa kuka kashe yana zura hannu aljihu...
   Dariya Fu'ad yayi yace "Daddy dan mutum yama matarshi abu sai iyayenta sun biya?" Dariya Uncle yayi yace "wai karmu d'aura ma nauyi" murmushi yayi yace "daga yanzu nauyin Lady yadawo wurina Daddy"..
   Dariya sukayi gaba d'aya, Yaya tace "yakamata mushiga daga ciki" Ah ni zanje wajen aike ne Mummy, Fu'ad ne ya fad'i haka...
   Hannunta ya kamo yace "ki kularman da kanki kinji zanje indawo u make sure kinci abinci kinsha magani kinji baby nah?"  D'aga mashi kanta tayi tace "ur wish is my command"..
    Dariya yayi ya mata peck a hannu, salati Yaya tayi tace "Fu'ad bakajin kunyarmu" dariya Uncle yayi yace "kinfa sa masu ido" yauwa Daddy fad'a mata, tab'e baki tayi tace " kunji dashi duk kai ke b'ata yarannan" ta juya ta tafi..
   Dariya sukayi su duka, bankwana Fu'ad ya masu ya juya ya shiga motarshi...

©FEEDOH DEEDOH

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245