RASHIN GATA 126-130

🌼🌼 *RASHIN GATA* 🌼🌼

         *TANBARI*
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

```NAH```
*FOUR STAR*🌟🌟🌟🌟

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HUSAYN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```

THIS PAGE IS FOR YOU YAN DANDALIN FEEDOH DEEDOH, MUNGODE KWARAI YANDA KUKE BIN LITTAFIN NAN. FOUR STARS NA MIK'A GODIYA #1LOVE♥

  126-130

   Tashi yayi yabar masu parlour'n saboda maganganunsu takaici kawai suke bashi, d'akinshi ya nufa bisa gado ya fad'a yafara juyi yana zubar da  wasu hawaye masu zafi..
   Wacece yarinyar da za'a  bashi? Shin irin macen da yake mafarkin ya aura ce? tana da ilimi? Ko kuma jahilace? Gaba d'aya ya jero ma kanshi wannan tambayoyin wanda shi kanshi bai da amsoshin su sai iyayenshi, amma ko wacece sai ta raina kanta dan sai na maida ita mak'ask'anciya sai na wulak'antata...
  Kyakkyawar Surar Nana ce ta fara yimashi gezo, rintse ido yayi yace "mike shirin faruwa dani?" Wata zuciya tace mashi kafara santa ne..
   "No" ya fad'a da k'arfi bazan tab'a santa ba i hate you Nana na tsaneki na tsani komi naki shegia Aljana....

*****
   Yamma lik'is ta iso gida, horn tayi Baba maigadi ya bud'e mata yana washe baki, saida tayi parking ta fito ta gaidashi bata jira ya amsa ba tayi cikin gida, dan duk tagaji wanka kawai takesan tayi ta huta.....
   Da sallama ta shiga parlour'n bata iske kowa ba dan haka d'akinta ta fad'a tana ajiye jikka ta fad'a toilet saida tayo wanka kana tafito, tana fitowa Mama na daidai shigowa da sallama amsa mata tayi tana fara'a, take tausayin tilon d'iyarta ya bayyana a zuciyarta, dan tasan tabbas Sameer sai ya wahalar mata da ita, ji takeyi kamar ta fasa dan in akwai abinda ta tsana shine ganin Nana cikin damuwa...
    Sai da ta tattaro kalaman da zata gaya mata, murmushi ta sakar mata tace "Nanar masai yau mi Mama tayi ba'a nemeta ba?"..
   Turo baki tayi tace "ni gaskia Mama kina b'ataman suna wane irin Nanar masai" dariya Mama tayi daidai tana zama tace "to kiyi hak'uri na daina" rungumeta tayi tace "yauwa Mamana" kanta ta shafa gaba d'aya tausayin Nana ya gama cika mata zuciya...
  D'agota Mama tayi tace "idan kingama shiryawa kin ci abinci inada magana dake" amsawa tayi da "to my Mamma my everything" murmushi Mama tayi ta mik'e tabar d'akin cike da damuwa....

  Bin Mama tayi da murmushi, gaban wardrobe ta tsaya riga da wando ta saka na company Zarah feshe jikinta tayi da turare, raba kanta hud'u tayi ta saka ribom sak baby doll haka ta fito, kallon kanta tayi a madubi batasan sanda ta saki wata dariya ba dan ita kanta ta san tayi kyau....
   Parlour ta nufa, dainning area ta wuce ta zuba abinci wanda zai isheta, bismillah tayi ta faraci. duk hankalin Mama ya koma kanta...
   Sai da taci ta k'oshi ta sha ruwa kana tayi hamdala, tasowa tayi ta k'araso inda Mama take tace "Mama nagama" shiru Mama tayi kamar bata jita ba, girgiza ta tayi tace "Mama dake fa nake" ajiyar zuciya Mama tayi ta sakar mata murmushin da iya karshi bisa labb'anta....

  Kallonta Mama tayi tace "kiban hankalinki Khadeejah magana nakeso nayi dake" tabbas tasan maganar mai muhimmanci ce tunda Mama ta kirata da sunanta...
" Toh Mama ina jinki" abinda tace kenan shiru Mama tayi ta rasa ta ina zatama fara...
   Kallon Mama tayi tace "Mama tun da nadawo na lura da kina cikin damuwa dan Allah ki gayaman damuwarki in shaa Allah ba zan baki kunya ba...
   Ajiyar zuciya tayi da taji kalaman Nana ko bakomi ta samu kwarin guiwa..
  Hannunta ta kamo tace "Nana kiyi hak'uri da abinda zan gaya maki hakan ba yana nufin ban sanki bane ba sai dai ina hararo maki alkairi da zai sameki Nan gaba...."
   Ita kam bata gane ina kalaman Mama suka dosa ba, kallonta tayi tace "Mama dan Allah kiman bayani yanda zan gane.."
    Kauda kai Mama tayi gefe tace "neman aurenki akazo na kuma amince na basu dama ko yaushe suka shirya su aiko sai a tafi can yobe" tunda Mama ta fara magana ta kafa mata ido kamar tv, "Allah yasa dai mafarki nake tabbas idan mafarki nake bazan so na koma baccin nan ba" abinda ta dinga cewa kenan...
   Ba mafarki kike ba dagaske ne abinda kikaji, d'agowa tayi tana hawaye tace "Mama mina maki haka? kin gaji da zama dani? Wane laifi na aikata maki haka da har kika yanke hukunci yiman aure, shin waye ma mijin? Mama waye wannan da kika bashi aure na ba tare da amincewa taba" Gaba d'aya ta jero ma Mama wannan tambayoyin...
   Ita kanta Mama hawaye takeyi, kiyi hak'uri ba laifin da kikaman inaso kisamu ingatacciyar rayuwa ne koda ba raina kuma mutanen da sukazo neman aurenki nasan ko banda rai su masu rik'e kine, kuma maganar miji kibarshi for now Nana bazaki san waye zaki aura ba idan anyi auren zaki san waye saboda bai gari yanzu, yanda kikaji maganar auren haka shima yaji, kuma yayi hak'uri yayi biyayya kema inasan kiman biyayya indai dagaske kike da kike cewa zaki sani farin ciki kisani dariya to inaso ki cikaman burina yau ki auri zab'ina...

   Tashi tayi tabar parlour'n da gudu tana kuka, tana isa d'aki ta fad'a kan gado kuka mai tsuma rai ta saki "wannan wace irin rayuwa ce ita kuma tata k'addaran kenan? Ba data ma akayi ba shi yaganta yace yana so ba? Tabbas Mama ta daina sona tun da har zata iya ba dani ga wani wanda shi kanshi da alamu takurashi akayi ya aure ni" haka ta dinga magana ita kad'ai tana kuka...
  Waya ta jawo tayi dailing number Umma, ringing biyu Umma ta d'auka cikin kuka tace "Umma na shiga uku" murmushi Umma tayi dan tasan za'ayi haka dama...
   Daurewa tayi tace "miyafaru ne Nana?" Kuka ta ciga dayi, Nana dan Allah kiman bayani kada kisa hankalina ya tashi ko Mamanki ce ba lafiya? Cikin kuka tace "ah ah" to miye? gayaman mana...
   Umma ashe dama mahaifiya na daina san d'anta? Umma Mama ta daina sona, mikika mata ta daina sanki Umma aure zata man....... Nan ta kwashe komi ta gaya mata...
  Saida Umma ta nisa tace "shine babban so da mahaifiyarki ta nuna maki kuwa, Nana ki saurareni da kyau, inasan kima mahaifiyarki biyayya kamar yanda kikace shi wanda zaki aura yaima mahaifansa biyayya namiji ma kenan bare ke mace, duk abinda Mamanki ta maki wallahi sanki takeyi dan haka ki amshi auren da zata maki da hannu biyu ki kuma zauna da mijinki tsakani da Allah da zuciya d'aya in shaa Allah zaki ci riba, mahaifiyarki na sanki fiye da yanda wata uwar ke san d'anta, Mamanki itace gatanki itace komi naki dan haka ki amshi zab'inta watarana sai kinyi alfahari da zab'in Mahaifiyarki, haka ta dinga yi mata nasiha mai ratsa jiki bata barta ba sai da taga jikinta yayi sanyi kana ta kyaleta...
   Cilla wayar tayi bisa gado, tayi gumi dan yanzu ma hawayen sun k'afe, tabbas abida Umma ta gaya mata gaskia ne..
   Tashi tayi ta nufi parlour inda tabar Mama nan ta iske ta,wuri ta samu kusa da ita ta zauna cire mata tagumi tayi tace "Mama tabbas kin cancanci na amshi zab'inki kodan baihuwar da kikaman, bayan haka ga gatan da kikaman kikabani ilimi ingantacce kece uwata kece ubana,  banda abinda zan saka maki Mama, amma kisani na amince da zab'inki zan aure shi kuma zan zauna dashi da zuciya d'aya...."
   Rungumeta Mamaa tayi tana tasa mata albarka, ga hawaye da suke ta sunturi a kuncinta. D'agowa Nana tayi ta girgiza mata kai kidaina kuka Mama wallahi na amince, murmushi ta sakar mata tace "Allah ya maki albarka ya rabaki da dunia lafiya, Nana kisani duk abinda kikaman  wanda na sani da wanda bansani ba da wanda ma zaki man nan gaba na yafe maki" rungume Mama tayi ta saka sabon kuka, gaba d'aya kukan suke saida sukayi mai isarsu kana sukayi shiru.....

FOUR STARS🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245