RASHIN GATA 106-110

🌼🌼 *RASHIN GATA* 🌼🌼

         *TANBARI*
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)```

```NAH```
*FOUR STAR*🌟🌟🌟🌟

*FEEDOH DEEDOH*
*(YAR FICIKA)*

```SADIYA ABDULLAHI
(STYLISH BCH)```

*ZAINAB Y HUSAYN*
*(AUTAR HAJIYA)*

```ZAHRA BUKAR
(CUTE ZARAH)```

"If you're alone, I'll be your shadow. If you want to cry, I'll be your shoulder. If you want a hug, I'll be your pillow. If you need to be happy, I'll be your smile... But anytime you need a friend, I'll just be me." THIS PAGE IS FOR YOU ZEEZEE YABOUR (Habeebty)..

106-110

   B'ata fuska yayi yace "ya ina maku magana amma kun tsaya kuna kallo na? Kodan ba ni baneba cikin wannan halin?" Su abin ma dariya ya basu kallonshi Umma tayi ta d'aure fuska tace "ashe kasan darajan mutum kake wulak'anta Nana" b'ata fuska yayi yace "yanzu mi yakawo maganan  Nana dan Allah?.."
   "Tabbas bai san ko wacece ba" Umma ke fad'in haka cikin zuciyarta..
   Mummy, Umma magana fa nake maku? "Ba inda zamu" Umma ta bashi amsa, fita yayi yabar d'akin fuuuu kamar wani kububuwa...
   Number family Dr d'in tayi try cikin sa'a ta shiga nan ta mashi bayani, "gani nan Hajiya" abinda yace kenan..
  Kallon Mummy tayi tace "gayanan zuwa" Alhamdulillah Mummy tace.....

  Baifi minti goma ba ya iso gidan, waya yama Umma yace "gashinan yazo" sawa tayi aka shigo dashi har d'akinta...
  Gaisawa sukayi daga nan ya fara duba Nana sai da ya gama dubata tsaf kana ya d'aura mata ruwa ya mata Allura, juyowa yayi ya kallesu cikin murmushi yace "Hajia dama period ne zatayi shine take fama da ciwon ciki wannan is normal things ga mace dan most of them d'in mata suna yinshi amma ga ruwa nan na samata na mata allura in shaa Allah data tashi zataji sauk'i.." godiya su ka mashi, bankwana yayi masu ya wuce..
  Kallon Umma, Mummy tayi tace "ikon Allah kenan kiga mutum shida aikinshi ya kasa ba kanshi taimako, amma fa yarinyar nan ta ban tausai lallai tana wahala" ajiyan zuciya Umma tayi tace "Wlh Mummy karki ga yanda hankalina ya tashi nidai har ga Allah ina k'aunar yarinyar nan har cikin raina.."
   Nikaina Umma inasan yarinyar nan inama Babynah ya sameta, b'ata fuska Umma tayi tace "daina ma wannan maganar yaron da ya tsaneta taya kike zatan zan bari ya aureta" murmushi tayi tace "ai Sameer yaro ne" hmm dama haka zakice..
   Dariya Mummy tayi tace "kalli yanda ya rud'e" ai baisan kowacece ba saboda nik'af d'in da take sakawa amma daya sani bazai kalli inda take ba...
  K'arfe biyar daidai ta farka, idata ta bud'e a hankali d'akin tabi da kallo daga k'arshe ta d'ora idonta kan Umma da tayi ta gumi, murmushi Umma ta sakar mata tace "kin tashi? Sannu da jiki kinji" murmushi tayi ta sunkuyar da kanta k'asa tana wasa da hannunta...
   Tashi ki shiga toilet ki wanka ko kinji k'arfin jikinki, ba musu ta mik'e ta nufi hanyar da Umma ta nuna mata, tana shiga toilet d'in ta bishi da kallo dan tun da take bata tab'a cin karo da toilet mai kyanshi ba....
  Ta dad'e tana wanka daga k'arshe ta fito, ganin an aje mata pad da pant kan gado yasa tayi murmushi, d'auka tayi ta koma toilet dan shiryawa..
  Tana fitowa daidai Umma na shigowa d'akin, k'arasowa tayi ta rungumeta "Sannu Nanana" abinda Umma tace kenan, murmushi tayi ta sunne kanta, mike maki ciwo yanzu? Babu ta bata amsa a hankali...
  Alhamdulillah to yanzu ki shirya ga kaya nan ki saka sai driver ya kaiki ko? D'aga kanta tayi alamar to..
   Shiryawa tayi cikin red abaya da Umma ta aje mata tana cikin d'aura nik'ab Umma ta shigo "masha Allah" abinda Umma tace kenan...
  Dariya tayi tace "Umma minene?" Babu komai tace tana dariya. Tana gama shiryawa ta fito d'akin Mummy ta shiga ta mata bankwana, rakiya sukayi mata har wajen mota, shiga tayi tana d'aga masu hannu suma hannun suka d'aga mata har tabar gidan...

suna shiga gate d'in gidan bata bari ya ida parking ba ta fito, tana gudu tace "mashi nagode" dariya yayi ya juya kan motarshi ya fita....
  Mama Mama Mama haka ta dinga kwala mata kira, da sauri ta fito daga kitchen tana l"afiya?"..
  Fad'awa tayi jikinta tana kuka, tuni Mama ta rikice ta yada wuk'ar hannunta, hannunta taja suka zauna "minene? Wani abu ya had'aku?" D'agowa tayi tace "ciwon mara nayi Mama sai da suka kira Dr dinsu.."
  Murmushi Mama tayi tace "to shine na kuka yanzu ai kinji sauki ko?" D'aga kanta tayi tace "Eh" yauwa Nanar masai. Dariya tayi tana bubbuga k'afa k'asa...
  Amm na manta d'azu Sameer yazo yama dad'e "What?" Sameer Mama miya kawoshi? D'aure fuska tayi tace "bansani ba wai Nana mi Sameer ya maki ne haka?" Hawaye suka gangaro mata tace "Mama Sameer ya tsaneni fa" jawota tayi jikinta tace "i know Sameer ya tsaneki ko kuma ince kun tsani juna, amma baki ganin irin biyayyar da yakeman? Yaufa Sameer nan yaci abinci." Tab'e baki tayi ta tashi tana gunguni, girgiza kai Mama tayi ta koma kitchen....

******
  Nana Nana, juyowa tayi tace "Maman Nana mizan maki?" Uwaki zakiman kitashi ki shirya ki tafi gidansu Umma..
  Baki ta zumb'uro tace "Mama banfa lafiya kuma sun sani" zama tayi gefen gadon tace "haba Nanana yaufa kwananki uku bakije ba ai kin samu sauk'i pls ki shirya kitafi kinji ko?.."
   Tashi tayi zaune, murmushi ta sakar ma Mama tace "tunda kince naje zanje Maman Nana" yauwa koke fa Nanar Sameer, da sauri ta kalleta, dariya Mama tayi. Kuka ta sa mata tace "Allah na fasa zuwa" da kyar ta lallasheta ta tashi dan ta shirya...

  Tsaye yake gaban dressing mirror yana gyara gashin kanshi da yasha mai sai kyalli yakeyi, k'ana nan kayane jikinshi na company Tomy hilfiger, kallo na k'are mashi Sameer dogo ne sosai amma ba fari bane ba kuma zaka kirashi bak'i ba, zaka iya ce mashi chocolate color Sameer handsome guy ne ajin farko yana da cute pink lipstick, yana da bud'adden k'irji ga 6packs d'inshi gashi in yayi dariya duka kumatunshi ke lotsawa muryanshi irin lion voice d'in nanne mai tafiya da imanin mutum, infact Sameer ya had'u namiji ne to d core...
    Da sallama ta shigo d'akin bai damu daya amsa ba haka kuma bata damu ba, hugging d'inshi tayi ta baya "My Son ina zuwa haka? Naga yau ba ranan aiki bane ba" ta tambayeshi, zanje gidan Maman Nana ne na gaisheta, ya bata amsa a tak'aice. Ido ta zaro tace "gidan Maman Nana?" Juyowa yayi yace "akwai matsala ne Mummy?" Murmushi tayi tace "babu my Son.."
  Peck ya mata a kumatu yace "datz my Mum" yauwa daga nan ka gano mana Nana lafiya? D'aure fuska yayi yace "wlh Mummy i hate Nana" ido ta zaro tace "Sameer are you mad?" Tab'e baki yayi yace "shiyasa na tsaneta saboda yanda kuke mata...."
  Murmushi tayi tace "amma baka da kunya ka tsani Nana kanasan Mamanta."
  Mummy kenan hating her daughter does'nt mean i don't like her, wlh Mummy i so much love Nana's Mum coz matar nada kirki sosai. Sakin baki tayi tana kallonshi dan bata tab'a ganin irin haka ba sai wajen Sameer...
   Iska ya hura mata, ajiyan zuciya tayi "Yadai Mum kike tunani?" Abinda yace kenan bakomi Sameer, dariya yayi ya mata peck a kunci ya nufi shoe rack d'inshi takalmin Aldo ya d'auko ya saka, kallon Mummy yayi yace "na wuce" sai kadawo abinda ta iya fad'a kenan ta kwanta saman gado...

  Da sallama ta shigo parlourn amma ba kowa k'arasawa tayi ciki, daidai yana fitowa jitayi an bangajeta sai da tayi k'ara, d'agowa tayi suka had'a ido tsaki ya saki yace "bak'auya kidinga kallon gabanki bawai kina kallon abinda ke cikin parlourn ba thou dama ba'a saba gani ba an baro karkara da miyar kuka an shigo burni dole ayi k'auyanci" ranta idan yayi dubu ya b'aci ji tayi kamar ta buga ihu saboda b'acin rai...
  Juyawa yayi ya barta nan tsaye, yakai k'ofa yaji ance Sameer sai da gabanshi ya fad'i dan yasan Umma taga komi kuma dizgashi zatayi..
  Juyowa yayi amma bai amsa ba, "bata hak'uri" abinda tace kenan, hak'uri Umma? Mina mata? Ka fini sanin abinda ka mata dan haka zaka bata ko ba zaka bata?...
  "Kiyi hak'uri" abinda ya fad'a kenan, murmushi tayi tace "issokay d'an burni" maganan ta k'uleshi..
  Takowa yayi yazo gabanta duk'ar da kanshi yayi yanda Umma ba zataji ba yace "muddin Umma na dizgani akanki ni kuma zan cigaba da tsanarki.."
   Murmushi tayi sai da fararen hak'oranta suka bayyana cikin nik'ab, "Sameer kenan kana tunanin abubuwan ka na d'agaman hankali? Abinda ka kasa ganewa shine kullum nike nasara akanka ko yanzu ni nayi winning saboda gashi d'an burni mai ji da kanshi naba yar k'auye hak'uri dan haka bansan Game d'in yak'are coz yanzu nakejin dad'inshi dan haka zamu gani tsakanin yar kauye da d'an burni wa zai cigaba da winning" tana gama fad'ar haka ta kashe mashi ido ta juya ta barshi nan tsaye yana huci..
  Dariya Umma tayi dan duk taji badak'alarsu, fita yayi Fuuuu kamar wanda zai tashi sama...
  Rungumeta Umma tayi tace "Nanana i miss you so much" murmushi tayi tace "miss you more Umma na" ya jikinki? Naji sauk'i yana Mummy? Da sauk'i...
   Hannunta Umma taja tace "muje kiyi break sai ki shiga wajen Mummy" ba musu ta bi bayan Umma..

FOUR STARS🌟🌟🌟🌟

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245