KUNYA ADON MACE 41~45

*KUNYA* *ADON* *MACE*

*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻

*_page_*4⃣1⃣ *_to_*4⃣5⃣

Kwance take d'aki tana kallon pic d'in Salman ga hawaye na bin kuncinta k'arar bugun k'ofanta ne yasa tayi saurin b'oye pic d'in ta nufa bakin k'ofa tana murza ido kamar mai bacci bud'ewa tayi ammi tagani tsaye tana murmushi, rab'ata ammi tayi ta shige d'akin biyo bayanta tayi tasamu wuri tazauna kallonta ammi tayi tace my babe bacci kikeyi d'aga mata kai tayi alamar eh tace toh tashi ki shirya kina da bak'o a parlor "d'ago kanta tayi tace bak'o kuma ammi d'aga mata kai tayi zumb'ure baki tayi Allah ammi nibazanje ba, had'e rai tayi tace toh karkije d'in wlh kinji na rantse bakije ba bani bake munb'ata  arazane tad'ago, yes I mean it, gyalenta taja fuuuuuu tayi gaba murmushi ammi tayi tace saidai kinje, tana isa parlor wazata gani asad ne d'aure fuska tayi tace malam lafiya miyakawo ka gidanmu ina ma kasan gidanmu murmushi yayi yace relax pretty cikin muryanshi mai sanyi yakamata kizauna ba musu ta zauna, "kallonta yayi yace haba pretty fad'a banaki baneba dan baki kama da masu fad'aba ba, gaskia tun randa naganki naji kinman kuma sanki nake da aure gidanku kuma yanda akayi nasanshi binku na dingayi a baya baku saniba harnaga gidanku, tasowa yayi yazo kusa da ita ya d'uka pretty Allah nakamu da sanki fiye da yanda kike tunani dan Allah kisoni kozanji sauk'i "hawaye ne suka dinga wanke mata fuska dan tabbas tasan zafin so saboda itama tana ciki san wani da zata iya cire salman da tabbas taso asad saboda shima namijine ajin farko, "hawayenta ya share mata kiyi hak'uri pretty bana fad'a maki dankiji haushi bane kawai dan kisan yanda nakesanki, kuka yaci k'arfinta tashi tayi ta nufa d'akinta da gudu tana kuka mai zafi hakadai asad ya k'araci zamanshi yatashi murmushi yayi yace aysaah na hango sona a idonki in shaa Allah ke rabo na ce.....

*BAYAN* *KWANA* *BIYU*
Zaune yake parlon bak'i sahr ce kusa dashi tana hawaye hankalin salman duk yagama tashi tasowa yayi yazo kusa da ita ya zauna hannunta yakama ya rik'e gam kamar za'a kwace mai ita, haba wifey kidaina kuka wlhi kukanki yana d'agaman hankali tafiya fa ba mutuwa ba kuma kinsan ina tare dake in shaa Allah bazan dad'e ba zandawo gareki kidaina kuka kinji, "hawayenta ta share toh yanzu miyasa bazaka zauna gidanku ba kasan bansan kayi nesa dani pls kayi hak'uri da komawa abujar nan, Salman yace haba sahr kinsan dai komawata Abuja dole ne koba dankomai ba, kodan aikin da ake neman man, in fact ya zama dole nakoma naga baby doll d'ina I miss her so much kiyi hak'uri bazan dad'e ba, hakadai yadinga lallashinta da kalamai masu dad'i har ta hak'ura hannunta yakamo har wajen motanshi kallonta yayi yace zan wuce wifey ki rik'eman amanar kanki kinji d'aga kanta tayi I'll in shaa Allah Peck ya mata kana yashiga mota tsaye take tana d'aga mashi hannu saidata ga yabar gate d'in gidansu kana tayi cikin gida da gudu tana kuka.....
              *************
"Yana zuwa gida ya shirya tsaf ya d'auki jikanshi yasaka a mota dawowa yayi cikin gida d'akin mufeedah ya nufa kwance take tana latsa waya d'agowa tayi tana murmushi bruh badai harka shirya ba na shirya abunda yace mata kenan, zama yayi kusa da ita yace lil sis kinsan minakeso dake girgiza kai tayi yace pls ga amanar sahr nan ki kularman da ita nasan zaki taya brudah d'inki san abinda yakeso, hawaye tafarayi saboda gaskia tafisan salman da aysaah dan tasan irin san da aysaah takema Salman, goge mata hawaye yayi yace nasan nabaki aiki mai wuya amma kituna yanda k'arfin san sahr yake gurina wlhi zaku iya rasani akanta, d'agowa tayi a razane tace in shaa Allah bazaka mutuba kuma zanyi komai saboda farin cikinka karkadamu bruh, Peck yamata yace datz my sis datz y I lurv u, lurv u mre bruh rungumota yayi kana suka tashi, sallama yayima iyayenshi ya d'auki hanyar abuja da zumud'in ganin fav sis d'inshi murmushi yayi dan yasan yau akwai rigima.....

*NOTE*

*I* *Dedicated* *dis* *page* *to* *all* *my* *fans,* *tnx* *so* *much* *for* *d* *bday* *wishes* *nagode* *sosai* *Allah* *yabar* *zumunci,* *lurv* *u* *dayawa* *dayawa* *my* *people*❤



Phirdauceejeebo.blogspot.com



*IG*: *yar_ficika*



© *Feedoh* *Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245