KUNYA ADON MACE 176~180

*KUNYA ADON MACE*


*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*THIS PAGE IS DEDICATED TO*
         👄 *MIEMIEBEE*👄

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
® *(NAW)*


*_page_*1⃣7⃣6⃣ *_to_*1⃣8⃣0⃣

    A hankali ta fara furta "Ya Asad dama zan k'ara ganinka?" Saikuma ta fashe da kuka, zama tayi tana kuka sosai a yayinda Salman yazo kusa da ita yana lallashinta, shiko Asad mutuwar tsaye yayi danko a mafarki beyi tunanin sake ganin Aysaah ba.
     Takowa yayi yazo kusa da ita ya duk'a yana kallonta tare da yin murmushi yace, "haba Preety miye na kuka? Kiga fa halin da kike ciki amma kina kuka kidaina pls." Kallon Salman yayi yana murmushi yace, "d'an uwa ashe da rabon zamu sake had'uwa?" Dariya Salman yayi yace, "ikon Allah kenan!" Rungume juna sukayi suna murnan ganin junansu.

   Aysaah tace, "Ya Asad wai me yafaru dakai ne? Kuma yaushe kayi aure? Dagaske Little d'iyarka ce?" Gaba d'aya parlorn aka fara dariya, Asad yace, "Preety duk ni zan amsa questions d'innan?" D'aga kai tayi alamar 'eh.' Dariya yayi yace, "zan amsa amma sai gabansu Ammi dan haka kushirya mutafi can."

     Kallon Hanan yayi yace, "dear yau burina ya cika naga second family nah." Murmushi Hanan tayi tace, "congrats Hubby" Asad ya kalli Little ya kirata da, "zo nan Little" da gudu Little taje wajen Asad ta fad'a jikinshi tana dariya, kumatunta ya shafa yace, "Little kinga wannan?" ya nuna Aysaah, d'aga kai tayi tace, "ai itace Antynah danake baka labari Daddy" murmushi yayi yace, "toh Antynki ce dagaske 'cause she's my sis, shikuma uncle Salman shima d'an uwa na ne" tsalle Little ta fara tana murna da gudu taje kan Aysaaah tana dariya. Rungumeta Aysaah tayi tana hawaye, Asad yace, "kutashi mu wuce gidansu Ammi" duk suka mik'e.

    Suna isa gidan basu ida parking ba Aysaah ta fita da gudu tana k'wala ma Ammi kira, kallon Salman Asad yayi yace, "dama haryanzu Aysaah bata daina wannan guje gujen ba?" Girgiza kai Salman yayi yace, "wallahi bata daina bafa" Hanan tace, "ashe Little nan ta gado guje guje da ihu" dariya sukayi suka wuce cikin gidan.
     Shiga ciki Aysaah tayi tana k'walama ammi kira a yayinda ta tardasu su duka a parlour. Da gudu ta fad'a jikin Ammi inda Ammi tayi saurin d'agota tana tambayarta ko lafiya cike da tashin hankali. Dariya Aysaah tayi tace, "lafiya lau dama-"
    katseta Ammi tayi da fad'a tace, "dama me? Waike yaushe za kiyi hankali? Bakisan abinda ke cikin ki ba amma har yanzu kina wawanci toh wallahi ba ruwana idan wani abu ya sami abinda ke cikin ki keda kakar yaron, aikinsan ko wacece ita." Marairaicewa Aysaah tayi tace, "Ammi Allah abin farin cikine-" Bata ida magana ba sukaji sallama.
   Amsawa sukayi Ammi tace, "ashe tare kuke?" Salman yace, "eh Ammi" kafin ta k'ara magana sai ga Asad ya shigo da su Hanan. Zumbur! Ammi ta mik'e tana nuna Asad, kallon inda take nunawa Mummyn Zarah tayi itama ta mik'e lokaci d'aya, atare sukace "Asad kaine?!" Murmushi yayi ya k'araso kusa dasu ya zauna yace, "nine" waya Ammi ta d'auka takira Papa ta gaya mashi ga Asad nan da murna Papa yace gashi nan zuwa.

    Nan fa aka fara gaisuwa yaushe rabo kowa na murnan ganin Asad.
    Asad ya kalli Mummyn Zarah yace, "Mummy haka Zarah ta zama budurwa ashe na kusa yin suruki" Dariya akayi itako sunne kai k'asa tayi tana wasa da yatsunta a yayinda tun shigowarsu Little ke jikin Ammi tana ta wasa.
    Bayan 'yan mintuna Papa ya shigo da sallamanshi a yayinda Asad ya mik'e yaje wajen Papa ya rungumeshi cike da jin dad'i, sosaj Papa yayi murnan ganinshi. Bayan nan Papa ya zauna suka gaisa dasu Asad, gaidashi Hanan tayi amsawa yayi cikin sakin fuska.
      Aysaah tace, "Papa surukar ka cefah" Papa yace, "to Alhamdulillah." Little ce ta taso tazo wajen Papa ya d'auketa yana mata wasa. Mummyn Zarah ake kallonsu tace, "gabanmu zaka d'auki kishiyarmu?" Dariya akayi Salman yace, "ai dayake Aysaah ce"
    Papa yace, "sunanta kenan?" Asad yace, "eh Papa yar k'anwata nama takwara." Saida akaci aka k'oshi kana suka dawo parlour dukan su, lokacin Little tayi bacci karb'anta Aysaah tayi daga hannun Papa tayi d'akin su Rahma da ita. Dawowa parlon tayi ta zauna. Binsu da kallo Papa yayi yace, "Salman ina kuka gano d'an uwanku?" Gyara zama Salman yayi yace, "Papa munje silver birth ne..." Nan ya kwashe komai ya gaya masu harda zuwa gidans hi da sukayi duk ya gaya masu. Cike da mamaki Papa yace, "ikon Allah sai kallo!" Ya cigaba, "Asad miya faru ne muka daina jinku? Kuma munyi bincike amma shiru." Gyara zama Asad yayi yace, "abinda yafaru shi ne..."

*MUJE ZUWA DANJIN MIYAFARU DA ASAD...*







phirdauceejeebo.blogspot.com




*IG: yar_ficika*




© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245