KUNYA ADON MACE 126~130

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
  ® *(NWA)*

*_page_*1⃣2⃣6⃣ *_to_*1⃣3⃣0⃣


Tana shiga d'aki ta fad'a kan haneefa tana dariya d'agota haneefa tayi tace lafiya naganki haka? Murmushi tayi saikuma hawaye da suka fara gangaro mata "share mata hawaye haneefa tayi tace haba bestie miye na kuka? kallon haneefa tayi tace mafarki na ya zama gaskia bestie yau nice gaban ya salman yana rok'on nasoshi bansan yanda zan gaya maki irin farin cikin da na shiga ba yau "kallonta haneefa tayi tace toh ayba hawaye zakiyi ba godia zakima Allah d'aga hannu tayi tana kwararo aduan godia ga Allah "saida ta gama haneefa tace toh yau kinga ranan adu'an da kikeyi ko? kinga ranan hak'urinki kuma ko? D'aga kai aysaah tayi tace gaskia ne bestie nakuma gode sosai yanda kika dinga encouraging d'ina "burina d'aya ya cika saura kuma d'ayan, da sauri haneefa ta kalleta tace wanene d'ayan kuma? Hawayen da suka mak'ale suka gangaro tace na ganin ya asad mana inasan naga ya asad kafin nayi aure inasan ya asad ya halarci biki na "haneefa tace hakane ki cigaba da adua in shaa Allah shima kunkusa had'uwa "suna cikin fira wayanta ya fara ringing tana dubawa taga salman ne murmushi tayi ta d'auka wayan.......

"Tana d'auka a shagab'e take magana salman yace haba baby doll shine kika taho ko? Yaufa ne yakamata mu fahimci juna...

Allah ya salman kunyarka nakeji murmushi yayi kamar tana ganinshi yace aiko zanmaki maganin kunyar nan...

Haka dai suka dinga firan soyayya tsoki haneefa tayi dan sun matsa mata pillow tasaka a fuskanta da haka har bacci ya d'auketa....

Fira sukeyi kowane yana gayama d'an uwanshi yanda yakeji "dare sosai suka raba suna fira daga k'arshe sukayi bankwana badan sungaji da junansu ba.....
          ★★★★★★★★★★★
"Text aysaah tama salman " kamar haka   ```com b with me wen d sun is sleepy.. you making me hold tyt my pillow like u d one. You write in oral... Ya salman u're d sweet nd socially skilled gud nyt nd dream of me... lurv u so much``` , tana gamawa tayi sending ta maida wayanta ta kashe tana dariya, "adua tayi ta kwanta tana murmushin jin dad'i.....

Kwance yake yana tuna aysaah komi nata burgeshi yakeyi sms yaji ya shigo wayanshi yana dubawa yaga aysaah ce da murmushi ya bud'e text d'in....

Karantawa yakeyi yana sake karantawa murmushi yayi yace ashe haka baby doll ta iya luv😂 dialing number dinta yayi yaji switch off....

"Murmushi yayi yamata reply  " ```sometimes ur nearnes takes my breath away & all dat i wanna say cant b expressed dan bn in silence... Lurv u so much d Apple of my eyes...```

Haka dai ya dinga juyi yana murmushi shi kad'ai har bacci b'arawo yayi gaba dashi.....

9:00am ta tashi tana kunna wayanta taga sms d'inshi karantawa tayi tana dariya aje wayan tayi ta nufa d'akin ammi.....

Tana shiga d'akin ta fad'a kan ammi dake lazumi saida ammi ta gama kana ta kalleta b'ata fuska tayi tace wai yaushe zaki hankali? Ina lazumi kin fad'oman marairaicewa tayi tace kiyi hak'uri ammi bazan k'ara ba..

Ammi tace Allah yasa "yanaganki haka kamar akwai magana bakinki? Murmushi tayi tace ammi kinsan waye bak'ona na jiya? Ammi tace ya xa'ayi nasani "dariya tayi ta rufe fuskanta da tafin hannunta tace ammi nah ya salman ne fa "jawota ammi tayi ta rungume tace shine kikejin kunyar gayaman harda rufe fuska dariya ta dingayi "ammi tace Alhamdulillah Allah na godema  da farin ciki  d'iyata ya dawo kamar da......

Rungume ammi aysaah tayi tace ammi nagode sosai tabbas kin ceci rayuwata Allah yabani ikon yimaki biyayya "ammi ta amsa da amin....

"Kallonta ammi tayi tace ina haneefa aysaah tace tanacan tana baccin banza dariya ammi tayi tace aygara ta huta "agogo aysaah ta kalla tace kai ammi bari naje na had'ama ya salman abinci kar ya makara tana fad'an haka ta tashi ta ruga tana dariya  "murmush ammi tayi tace Allah ya shiryaki salman ya b'ataman yarinya....


*NOTE:*

*Assalamu Alaikum, my beautiful people ina mai baku hak'uri saboda zan tsaida littafin d'in kunya adon mace, saboda exams d'in da zanfara monday amma idan nasamu interval in shaa Allah zanmaku posting, nd ina neman adu'an ku, lurv u hameesha hameesha my sweeriees*❤


Phirdauceejeebo.blogspot.com




*IG: yar_ficika*


© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245