KUNYA ADON MACE 21~25

*KUNYA* *ADON* *MACE*

*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻

*_page_* 2⃣1⃣ *_to_*2⃣5⃣

Tana shiga d'aki ta aje kayan, wayanta tajawo ta shiga gallery pic d'in wani handsome guy naga tana kallo, "wanda nidai yar ficika narasa gane shin waye wannan da sanshi ya hana aysaah komai, surutan da takeyi ne yamaidoni hayyacina, "da kasan irin sanda nake maka dakazo da sauri wajena, naso ace yanda nakesanka kaima haka kakesona, inama zan iya gayama abinda ke cikin raina watak'ila da kasoni saidai *kunya* *adon* *mace*, bazan tab'a fad'ama ba harsai sanda da kanka kace kanasona, fad'awa tayi kan gado tana kuka sosai, kamar zata fidda ranta, da haka har bacci yayi gaba da ita.....
                 *********
Kodata farka idonta ya kumbura saboda kuka, wanka tashiga tayo, kana ta d'aura alwalla, humra ta shafa sai body spray jallabiya ta saka, kana ta kabbara sallah, bata tashi daga inda takeba saidatayi isha tagama kaima Allah kukanta kana ta tashi ta sauka k'asa wajen iyayenta...

"Ganin mahaifinta parlor ya bata mamaki, da gudu ta isa wajenshi tafad'a kanshi, tana dariya aysaah tace papa yaushe kadawo shine bansani ba, kumatunta ya shafa yace my dota tun d'azu nadawo kuma na lek'a d'akinki naga kina bacci shiyasa na kyaleki, duk abinnan da akeyi hankalin ammi nakan aysaah, ammi tace my babe zo Nan tashi tayi taje kusa da ammi, dubanta tayi cikin kulawa tace kuka kikayi? D'agowa tayi a razane tace ah ah murmushi ammi tayi tace gashi k'arya bata dace dakeba in fact bakima iya ba, saboda duk kinkama kanki, oya tell Mie d truth miyasaki kuka har idonki ya kumbura karkiman k'arya, aysaah tace ammi cikina yayi ciwo shinefa, ammi tace miyasa baki kirani a waya ba? Aysaah tace ammi forgive me pls bazan k'araba, ammi tace shikenan mutafi nabaki magani da sauri aysaah tace nasha ay, ammi tace shikenan....
                 *******
Zaune suke saman dainning table suna cin abinci, papa yace my boy kafa k'ara fari da kyau, murmushi Salman yayi yace papa yanayin k'asar danaje ne haka, ammi tace shiyasa zankai d'iyata can tayi masters dariya akayi gaba d'aya, Salman yace papa inasan naje kaduna gobe, papa yace yana da kyau haka, amma yaushe zaka dawo salman yace banwuce 1week papa yace Allah yakaimu, aysaah tace ammi nah zanbi ya salman ammi tace my babe kibar karatun naki ina? Kumbure fuska tayi tana kuka, ita adole saita bishi, jawota yayi yace haba my baby doll kiyi hak'uri kizauna nimafa duka sati guda zanyi kinji, nida nakesan kizama babbar lauya yanda dana jawo fad'a olrdy lil sis d'ina zata Kareni, dariya ta dingayi, haka dai suka dinga fira har lokacin bacci yayi kowa yatafi ya kwanta.....



            "Tunda tayi sallan asuba takasa komawa ta rasa abinda ke mata dad'i kodan yayanta zaiyi tafiya ne oho? 9:00am ta sauko k'asa cikin shigar k'ananan kaya, wanda sukayi matuk'ar karb'anta kitchen ta wuce dan had'ama ya salman breakfast tana gamawa  d'akin ammi tawuce bata sameta ba, saboda tana sashen papa, "k'arfe 11:00am ya Salman yagama komai wajen motarshi ya nufa da gudu tazo tafad'a jikinshi tana kuka, aysaah tace dan Allah bruh karka tafi kabarni, d'agota yayi ya share mata hawaye yace  kiyi hak'uri lilsis nima bada san raina zantafi ba, dandai tafiyan yazama Dole kinji my babe, d'aga kanta tayi yace toh stop cry share hawayenta tayi yace yawwa gud gal, peack ya mata a goshi, kana ya saketa ya shiga motarshi, d'aga masu hannu yakeyi harya bar haraban gidan, fad'awa tayi kan ammi tana kuka, janta ammi tayi sukayi cikin gida tana aikin lallashi....


"Tunda suka shiga gida ammi ke aikin lallashi da nasiha amma aysaah kuka takeyi hartakai ga ammi tamata fad'a, shinefa aka samu tayi shiru, rannan aysaah sukuku tayini har dare abun yana damun ammi sosai, saboda batasan taga d'iyarta cikin damuwa, yau ko abincin dare k'inci tayi tana gama sallah ishaa ta rufe d'akinta, ammi tazo tayi bugun k'ofan amma tak'i bud'ewa, hoton dream guy tajawo tana kallo tana surutu ga kuma hawaye daketa bin kuncinta.......


*Yakamata* *masu* *karatu* *Susan* *wacece* *aysaah,* *shin* *aysaah* *waye* *takeso* *Kodai* *aljanine* *take* *so* *dan* *da* *Alama* *wanda* *take* *so* *baimasan* *tanayi* *ba* *kudai* *cigaba* *da* *bin* *yar* *ficika*...


Phirdauceejeebo.blogspot.com

*IG*: *yar_ficika*


® *Feedoh* *Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245