KUNYA ADON MACE 76~80

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
® *(NWA)*

*_page_*7⃣6⃣ *_to_*8⃣0⃣

*BAYAN SHEKARA BIYU*
Abubuwa sun faru cikin shekara biyu ciki harda zuwan asad nigeria wajen aysaah tare suka zo shida ablah satinsu biyu kana suka koma nan ma ansha kuka dan da kyar aka raba ablah da aysaah, yanzu haka aysaah tana final year d'inta second semester itakuma zarah anzama yanmata saboda itama tana base university tana karanta mass communication, babu abunda ya canja tsakaninta da salman, kullum aduan ta d'aya Allah ya sa salman ya sota shiko hankalinshi bai kanta, saboda ya riga da ya mallakama sahr zuciyanshi, kuma duk abinnan aysaah batasan da zaman sahr ba "zaune take d'akin ammi tana karatu ammi ce ta shigo d'akin da sallama amsa mata aysaah tayi tana murmushi dafata ammi tayi tace my babe kizo papa yana san ganinmu, haka kawai taji gabanta na fad'uwa d'agowa tayi a sanyaye tace ammi nah lafiya daiko? Murmushi ammi tayi tace lafiya lau my dota kedai tashi muje mik'ewa tayi tabi bayan ammi, parlor suka sami mummyn zarah da papa, zama ammi tayi itama aysaah wuri ta samu kusa da ammi ta zauna, "gyaran murya papa yayi aysaah ya kira ta d'agowa tayi tace naam papa, kinsan dalilin da yasa na kiraki girgiza kai tayi alamar ah ah, yace Alhamdulillah yanzu ajinki nawa? A sanyaye tace papa final ya nake "gud kinsan abinda yasa na kiraki  girgiza kai tayi, yace sonake ki turoman wanda kikeso saboda da kin gama makaranta zan aurar dake kinga baiyuwa kina gida gasu zarah suna tasowa, idan kuma baki da wanda kikeso to dama abokina yaman maganarki yanasan na aura ma d'anshi ke, nace yabari sainaji daga bakinki ba aysaah data kusa sakin fitsari ba koni *yarficika* saida gabana ya fad'i, kyarma ta kamayi saikuma ta fashe da kuka ta fad'a jikin ammi....
              **********
tsawa mummyn zarah ta daka mata uwarmi aka maki daga cewa ki fiddo miji shine sai kuka ko so kike mu zauna muda ke arasa gane matan gidan, ammi ta d'ago rai b'ace tace dan Allah hajia ki saurarama yarinyar nan hakanan shin dawane zataji haba mana, d'agowa tayi tace papa banda saurayi kuma wanda kakesan kabani wlhi bansanshi  duk da bantab'a ganinshi, papa yace na gama magana nidai nabaki nan da 3month daidai kingama exams d'inki da 2weeks kenan idan baki fito da wanda kikeso ni zanbaki yaron abokina, tashi tayi ta nufa d'aki da gudu tana kuka tana shiga ta maida k'ofa ta rufe ta fad'a kan gado tana kuka sosai hoton salman ta jawo tafara surutai ya zakaman haka kasan duk dunia nafi kowa sanka amma ka kasa gano hakan, yanzu gashinan za'a aura man wani ba kaiba Allah ka kawoman mafita fashewa tayi da sabon kuka mai cin rai...

      "Itama ammi tashi tayi ta nufa d'aki rai b'ace dan gani take ba'ama tilon d'iyarta adalci ba...

"Duk abinnan da akeyi salman yana kd amma gobe zaidawo....

*WASHE GARI*
Koda aysaah ta tashi fuskanta yayi kumburi dagani kasan taci kuka, wanka ta shiga tana fitowa turare ta saka ta d'auki doguwan riga ta saka, "d'akin ammi ta shiga da sallama ammi na ganinta ta taso ta tareta zaunar da ita tayi ta had'o mata tea mai kauri ta bata ta sha saida ta tabbatar data k'oshi kana ta ajiye cup d'in, kiran sunanta ammi tayi jiki sake ta d'ago ta kalleta a sanyaye ta amsa da naam, "shiru ya d'an biyo bayansu kana ammi tace sonake kiban hankalinki nan, kinsan dai bazan so abinda zai cutar dake ba ko? D'aga kai tayi  ammi tace good, nasan bazaki rasa wanda kike so ba toh ki gaya mashi yazo yaga babanki, hawaye suka fara sunturi a kuncinta kamar famfo tace Allah ammi banda saurayi banyi niyar fara soyayya yanzu ba nama zuciyana alk'awari ne, ammi tace alk'awari? Wane irin alk'awari kikayi kuka kawai takeyi ammi tace toh nidai aysaah bani da abinda zan gayama babanki ya fasa abinda yayi niya, kifito da wanda ke sanki if not nasan ba abunda zai hana yabaki yaron abokinshi, fashewa tayi da kuka tace pls ammi karki bari yaban wani wlhi zaku iya rasani saikuma ta tashi tayi d'aki da gudu tana kuka itadai ammi binta tayi da ido....

      "Wayanta ce yayi ringing kamar bazata d'auka ba saita duba sunan ammi ne tagani a screen d'in wayan, d'agawa tayi banji mi aka ceba saitace gani nan, tashi tayi ta d'auki gyalenta ta d'aura tayi k'asa, "ammi tagani da mummynzarah gaidasu tayi ammi ta bita da kallo  kwana d'aya da yini d'aya duk ta fad'a, "aysaah tace ammi yana ina? Yana d'aki tunda ya shigo yake nemanki yace kikai mashi abincin shi, amsawa tayi da toh ta wuce kitchen abinci ta had'a mashi bisa tray da lemu ta d'auka ta nufa d'akinshi "tana isa bakin k'ofa zata murd'a kenan taji maganashi, haba sahr kiyi hak'uri ba wani dad'ewa zanyi ba zandawo kuma kinsan yanzu ne zan tunkari iyayena da maganar auren ki tunda kin kusa gama makaranta kinga da kin ida sai ayi bikinmu, banji mi taceba salman yace aykinsan bazan tab'a son wata bayanke ba so ki kwantar da hankalinki, "numfashinta ya nemi d'aukewa, nikaina *Feedoh Deedoh* saida biro na yafad'i tray d'in hannunta ne ya kufce ya fad'i komai ya tarwatse k'asa, k'arar fad'uwan abu salman yaji yasa ya nufo k'ofan da sauri............



Phirdauceejeebo.blogspot.com


*IG: yar_ficika*

© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245