KUNYA ADON MACE 106~110

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
  ® *(NWA)*

*_page_*1⃣0⃣6⃣ *_to_*1⃣1⃣0⃣

```BAYAN KWANA BIYU```
Zaune suke d'akin da aka kwantar da aysaah in banda k'aran fan ba abinda kakeji ammi ce tayi ajiyan zuciya ta kalli papa tace nidai rashin farkawan yarinyar nan yana damuna ace kwananmu biyu yau amma ko motsi batayi kuma danama likita magana saiyace zata iya farfad'owa kowane time. "salman yace wlhi ammi nikaina abun na damuna "papa yace haba ammin aysaah kinsan fa likitocin nan na bakin k'ok'arinsu tunda sukace zaya farka zata farka kidaina saka damuwa aranki, mummynzarah tace kidaina damuwa ammi d'iyarki takusa farkawa in shaa Allah kaima my boy ya kamata kadaina saka damuwa kaifa namiji ne kaida aka san namiji da zama strong amma shine kake damuwa haba my boy be a man mana. "Girgiza kai salman yayi yace Allah mummynah ciwon baby doll yana d'agaman hankali, nasani amma adua ita yakamata mudingayi "yanzu katashi kaje zaka kai su mummyn ablah unguwa....
        ★★★★★★★★★★
"Ammi Karki tafi kibarni dan Allah ammi karki tafi wlhi shinakeso shine zab'ina ammi kice karsu ban wani suban zab'ina' "ba ammi ba harta papa saida maganan aysaah ta bashi mamaki dama akwai wanda aysaah ke so shine takasa fad'a toh wannan waye? Tambayar da babu mai amsarta sai ita, ammi ce tace aysaah lafiya? Bud'e idonta tayi kallo tabi ammi dashi saikuma ta rufe idonta papa ne da sauri yaje ya kira doctor, yana zuwa yayi dube dube ya mata allura "kallon ammi yayi yace congrats hajia d'iyarki ta farfad'o kuma ba wata matsala yanzu saidai d'an abunda ba'a rasa ba "murmushi ammi tayi tace nagode doctor...

"D'akin cike yake da mutane yan dubiya harda haneefa tana farkawa tafara kiran sunan ammi da sauri ammi ta k'araso gabanta hannu ta mik'a mata kamata ammi tayi ta tadata zaune kallon ammi tayi ta mata murmushi tace ammi zanyi sallah "da taimakon ammi aysaah tayi wanka tayi alwalla zuwa tayi ta kabbara sallah saida tabiya bashin sallan da ake binta kana ta ma ammi alamun ta gama kamata ammi tayi ta maidata bisa gado, "kowa sannu yake mata itadai ta bisu da kallo kawai haneefa ce da ablah suka k'araso wajen gadon suna tambayanta jiki aysaah ta ce dasauk'i "kallonta haneefa tayi ta bud'e baki zatayi magana kenan ammi ta k'araso wajen da abinci a plate....
            ◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆
Abinci take bata tanaci salman ne ya shigo da sallama ganin aysaah zaune tana cin abinci da sauri ya k'araso gaban gadon, kallonta yayi yace my baby doll sannu kauda kanta tayi gefe guda, ammi kawo na dinga bata da sauri aysaah tace ah ah ammi nah nike nakeso nanfa suka fara rigima dariya kawai ake masu, mummynzarah tace my boy taso kyalesu, mummyn ablah tace yanzu salman daga fara samun sauk'in yarinya shine harzaka fara matsa mata kumbure fuska yayi ya fita yabar d'akin yana gunguni dariya suka bishi da ita....

"Doctor ne ya shigo ganin aysaah zaune yace eyyeh my patient kin samu sauk'i fa, d'aga kai tayi tace eh mana ko yanzu kayi discharging nawa ma dariya yayi yace da sauranki yanmata ba yanzu zan sallame ki ba, dubata yayi kana ya mata alluran bacci "kallon ammi yayi yace yau yarinyarki tasha surutu da yawa dan haka na mata alluran bacci dan tasamu sauk'i sosai....

"Salman ne ya shigo d'akin yana had'e rai shi ala dole anmashi laifi kallonshi ablah da haneefa sukayi suka kwashe da dariya harara ya wurga masu yace bestiee harda ke ko? Murmushi tayi tace ya salman kaine da abin dariya Allah fushi baimaka kyau dama ka daina. Ablah tace tayani gaya mashi sis, kallon ammi yayi yace ammin baby doll kinajinsu fa ammi tace ay gaskia suka fad'ama daga samun sauk'in yarinya na zaka fara rigima da ita doka zan sakamaku kan yarinya na bari dai mukoma gida dariya mummynzarah tayi tace my boy zo nan rabu da ammi kaji....

"Binsu mummyn ablah tayi da kallon sha'awa gaskia rayuwan gidansu aysaah na burge kowa komi nasu tare sukeyi kansu had'e yake saidai fatan Allah ya k'ara had'a kansu.........





Phirdauceejeebo.blogspot.com



*IG: yar_ficika*




© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245